ALLAH ya yi wa tsohon ɗan jaridar nan kuma dattijon arziki, Alhaji Sanda Adamu Tsafe, rasuwa. Shekarun sa 77.
Ya rasu a daren jiya a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo (UDUTH) da ke Sakkwato bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Marigayi Alhaji Sanda ya yi fice a aikin rediyo a lokacin da yake aiki a gidan Rediyo Talbijin Kaduna.
Daga nan ya yi aiki a Sashen Hausa na gidan rediyon BBC.
Haka kuma ya taɓa zama Janar Manaja na gidan Rediyon Rima da ke Sakkwato, muƙamin da aka tsige shi daga kai sakamakon rikicin sarauta da ya biyo bayan rasuwar Sarkin Musulmi Abubakar na 3 a cikin 1988.
Daga bisani, an naɗa shi Kwamishinan Zaɓe na Tarayya mai kula da Gundumar Birnin Tarayya (FCT).
Alhaji Sanda sananne ne wajen taimakon jama’a da kuma ayyukan addini, musamman a Jihar Zamfara.
‘Yandoton Tsafe Alhaji Habibu Aliyu ya naɗa shi Sarkin Yaƙin Tsafe.
Shi ne ciyaman na kamfanin Adahan Universal Investment Limited.
An haife shi a cikin 1948 a garin Tsafe, inda a nan ya fara yin karatun firamare kafin ya wuce Babbar Makarantar Firamare da ke Kwatarkwashi.
Ya yi karatu a Makarantar Lardi da ke Sakkwato, da Makarantar Share Fage (SBS) ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Daga bisani, ya yi karatu a Makarantar Aikin Jarida ta London, wato London School of Journalism.
Marigayi Alhaji Sanda ya rasu ya bar matan aure biyu, da ‘ya’ya 29, da kuma jikoki 36.
Allah ya rahamshe shi, amin.
