ALLAH ya yi wa tsohon ɗan wasan kwaikwayo ɗin nan mazaunin Jos, Malam Abdullahi Shu’aibu (Ƙarƙuzu ko Abdu Kano), rasuwa ɗazun nan.
Majiya ta ce ya rasu sakamakon rashin lafiya.
Za a yi jana’izar sa gobe da safe a gidan sa da ke Haruna Haɗeja Street, cikin garin Jos, Jihar Filato.
‘Yan fim da dama sun yi alhinin rashin sa, suna addu’ar Allah ya jiƙan sa, ya ba iyalin sa haƙurin jure wannan babban rashin.
Ƙarƙuzu dai ɗan wasan kwaikwayo ne wanda ya yi tashe a wajen masu kallon wasan talabijin na ‘Ƙarƙuzu’ a shekarun 1980.
A wasan yakan yi wa kan sa kirari da, “Ni ne Ƙarƙuzu, ɗan Ƙurmuzuzu, jikan Ƙuzu na Bodara, abar ni sai ta Allah ta yi.”
Shekarun sa 43 a harkar wasan kwaikwayo kafin rashin lafiya ya sa ya daina.
A cikin Agusta 2023 ya taɓa ɓara kan halin ha’ula’i da yake ciki saboda yanayin rayuwa inda har ya yi kira ga jama’a da su kai masa ɗauki.
A lokacin ya ma makance sannan yana fama da matsanancin rashin lafiya.
Bugu da ƙari, ba ya da kayan abinci.
Ƙarƙuzu ya yi bayanin ne a wata hira da kafar yaɗa labarai ta ‘Zinariya TV’ ta yi da shi, wanda bidiyon ta ya yaɗu a soshiyal midiya.
A waccan hirar, wadda mujallar Fim ta kawo maku labarin a ranar 9 ga Agusta, 2023, Ƙarƙuzu ya ce: “Ni dai suna na Abdullahi Ƙarƙuzu, amma al’amura yadda su ke, suna na Abdullahi Shu’aibu, kuma ana kira na da suna na Abdullahi Kano; waɗannan duk suna na ne. Halin da na ke ciki a yanzu, wato a wuri na mai kyau ne, a wurin Allah ma mai kyau ne. Amma ba na jin daɗi.
“Saboda yanzu shekara na 43 ina wannan al’amura. Amma gaskiya, yanzu wani lokaci sai in kwana ba ni da abin da za a ci a gida na. Kuma wani abin tausayi, ni Ƙarƙuzu a yanzu zancen da na ke, wannan gida da nake ciki an sa shi ma a kasuwa, ba gida na ba ne, haya nake yi.
“A yanzu a cikin wannan al’amari da na ke yi, yanzu in an ce na mallaki gida mai ɗimbin yawa, waɗansu da za su ke kallo na sai su ce gaskiya ne. Amma wallahi tallahi, ɗaki ɗaya a ce nawa ne wanda na mallaka, ba ni da shi.
“A cikin wannan aiki da na ke da wannan shekara, na makance. Yanzu zancen da na ke mai kallo na ba na gani, ni sai dai ya gan ni, amma ni ba na ganin sa. Ba na gani, idon ya makance. An yi aiki a wannan idon (dama), bai gani ba, aka zo aka sake yi a wannan idon, bai gani ba. Daga ƙarshe daktoci sai su ka gaya min wai akwai wata cuta, hawan jiki gilakoma, su kuma daktoci sun riga sun yi ƙiyasin cewa wannan idon ba zai gani ba, ‘Ƙarƙuzu sai dai ka haƙura haka’.”
A kan batun ‘yan fim da za su iya taimaka masa, irin su Ibrahim Mandawari, sai ya ce: “Ai duk daga baya kenan. Su kuwa, su Mandawari ai daɗaɗɗu ne a gare mu. Kuma waɗanda mu ke maganar sun mutu. Kamar na jihohi, kamar dai a Kano, akwai Karo-Da-Goma, akwai Malam Mamman, waɗanda mu ka yi aikin da su, duk an rasu tsofaffi.
Ya yi nuni da cewa taimako gare shi zai iya zuwa daga ko’ina.
Ya ce, “Ai yanzu ba wai al’ummar Kano kawai ko al’ummar Jos ko na Kaduna ko na Legas ba, duk al’ummar duniyar nan ina buƙatar a taimaka min. Wannan gida yanzu da aka sa shi a kasuwa za a sayar, ba ni da kuɗi, bayan ba ni da kuɗi ba na gani, ba na zuwa ko’ina. Ina da ‘ya’ya. Maganar abinci kam ma babu. Wannan shi ne zahirin gaskiya.
“To, kuma yau ɗin nan, yau yadda ta ke, sai an daure. Duk abin da za a yi mini, na san abin da za a yi mini abu ne wanda in Allah ya so ya yarda sadaƙatujjariya ne.
“Bayan an yi min, za kuma ka je ka samu abin da ka ke nema a inda za ka tafi lahira ka je ka kwanta.
“In-sha Allahu, ina neman wannan taimako a taimake ni. Ko ba wannan gida ba ma da na ke ciki, ni dai in samu abin da zan ɗan gangara lahira; in na tafi gidan da za a zo a ce wannan gidan wane ne, taimaka masa aka yi ya saya.
“Kuma a tallafa min da kayan abinci. Bayan kayan abinci, a tallafa min da ɗan abin da zan samu ina rufewa. A taƙaice dai ba na gani, ba ni da lafiya, ga shekaru masu yawa.”
Sakamakon neman taimako da ya yi, wani ɓangaren kuma, sai shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Nijeriya ɗin nan, Ahmad Musa, ya ba Ƙarƙuzu taimakon kuɗi N500,000, sannan kuma ya ba da umarnin a nemo gida ya saya masa, wanda bai wuce naira miliyan huɗu zuwa biyar ba.
Kuma haka aka yi, domin kuwa Ahmed Musa ya saya masa gida na N5,500,000 (wato miliyan 5 da rabi).