TSOHON Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), Alhaji Abdullahi Maikano Usman, ya aurar da ‘yar sa ta uku a yau Juma’a.
An ɗaura auren Rabi’atu Abdullahi Maikano da abin ƙaunar ta, Khamis Garba Zarewa, da misalin ƙarfe 2:15 na rana, wato bayan an sauko daga sallar Juma’a, a masallacin Juma’a na Al-Mannar da ke Unguwar Rimi, Kaduna a bisa sadaki N150,000.
Mahaifin amarya ya nuna matuƙar farin ciki, ganin yadda jama’a su ka taru domin ɗaurin auren. Wannan ya sa tun ana shirin ɗaurin auren ya riƙa bi layi-layi a cikin masallacin ya na gaisawa da mutane, ya na kuma yi masu godiya.
Bayan an ɗaura auren, sai aka ɗunguma zuwa sabon gidan Maikano da ke unguwar Babbar Saura, inda aka gudanar da walima.
Sheikh Tukur Adam, babban limamin Masallacin Al-Mannar, shi ne babban baƙo a wurin walimar.
Da farko, Maikano ya buɗe taro da addu’a tare da gabatar da Sheikh Tukur da babban limamin masallacin Jum’a da ke unguwar Babbar Saura, Sheikh Musa Haruna.

Sheikh Tukur ya yi taƙaitaccen jawabi a kan muhimmancin aure da kuma jan hankalin ma’aurata da kira ga matasa da su guji auren sha’awa.
Shehin malamin ya yi addu’o’i ga ma’auratan da iyayen su da kuma sauran masu aure da ma waɗanda ba su kai ga yin auren ba.
Haka shi ma Sheikh Musa Haruna, ya yi jawabi ne a kan aure da muhimmancin haƙuri a lokacin da aka shiga matsatsin rayuwa.
Sannan ya yi bayani a kan yadda wasu matan ke jan hankalin mazajen su wurin neman halak, su guje wa haram yayin da su ke nema wa iyalin su abin da za su kula da su.
Babban limamin masallacin Kano Road, Sheikh Habibu Umar Mahmud, ya halarci wurin walimar, inda shi ma ya sa albarka tare da yin addu’o’i.
Walimar ta ƙayatar matuƙa, domin an ci an sha, sannan an yi zumunci.
Haka kuma dukkan waɗanda su ka halarta sun ƙaru da nasihohin malaman su ka yi.
A zantawar sa da mujallar Fim, Maikano ya nuna murna da farin ciki game da wannan rana, ya ce, “Alhamdu lillahi rabbil alamin, alhamdu lillahi rabbil alamin, wassalatu, wassallamu ala rasulillah, annayul Mustapha, muntaƙa, murtada.
“A gaskiya babu abin da zan ce, alhamdu lillah, na yi wa Allah maɗaukakin sarki godiya da ya ba ni iko, ya ba ni zarafi na aurar da wannan ‘ya tawa. Ina yi masu fatan alkhairi, ina yi masu fatan zuri’a ɗayyiba, ina masu fatan zaman lafiya duniya da lahira, ina masu fatan su kasance tare a duniya, tare a cikin Aljannar Firdausi. Mu ma Allah ya ba mu wannan nasara.
“Na biyu kuma, dukkan waɗanda su ka zo wannan biki, da waɗanda su ka taimaka a wannan biki da dukkan waɗanda su ka yi addu’a a wannan biki, Allah ina roƙon ka da sunayen ka tsarkaka, waɗanda idan aka roƙe ka da su ka ke amsawa, Allah ka yi wa kowa kyayyawar sakayya, alfarmar Annabi Muhammad (s.a.w).”

Haka kuma uban amaryar ya shaida wa wakilin mu cewa shi ya fi ba addini da malamai muhummanci a irin wannan al’amari.
An tashi daga walimar da misalin ƙarfe 3:30 na yamma.
‘Yan fim da su ka halarci ɗaurin auren da walimar sun haɗa da Alhaji Magaji Sulaiman (Sulson), Nura MC, Ibrahim Daddy, Hamisu Bawasa, Harith Maigula, Ɗanladiyo Mai Atamfa, Hussaini Hassan da Dikko Yakubu.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.

