• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Tsohon shugaban MOPPAN, Maikano, ya yi alhinin rasuwar Mubarak, ɗan aminin sa da ya ke riƙo wanda ya mutu a kogi

by DAGA ABBA MUHAMMAD
December 9, 2022
in Labarai
0
Maikano (dama) da marigayi Mubarak

Maikano (dama) da marigayi Mubarak

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

TSOHON Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) na ƙasa, Alhaji Abdullahi Maikano Usman, ya bayyana irin jimamin da ya shiga na rashin Mubarak, ɗan aminin sa Alhaji Magaji Sulaiman da ya ke riƙo wanda ruwan Kogin Kaduna ya tafi da shi.

Idan kun tuna, mun ba ku labarin yadda a ranar Lahadi, 4 ga Disamba, 2022 Allah ya ɗauki ran Mubarak lokacin da ya je kogin a unguwar su, wato Kabala Costain, Kaduna, domin ya wanke ƙafar sa. 

Mubarak, mai kimanin shekara 19 a duniya, shi ne babban ɗan matar Alhaji Magaji Sulaiman wadda mujallar Fim ta ba ku labarin rasuwar ta da ta faru a ranar Litinin, 22 ga Agusta, 2022, mai suna Hajiya Hannatu Yahaya.

Da ya ke zantawa da mujallar Fim kan wannan babban rashi da aka ƙara yi, Maikano ya ce, “Tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (s.a.w.). A gaskiya, na yi jimamin rashin wannan ɗa nawa, Mubarak, domin yaro ne wanda ba shi da hayaniya, yaro mai ladabi da biyayya, wanda a gaskiya duk abin da na faɗa, ba ma ni kaɗai ba, a unguwar mu da jama’ar da ke tare da mu sun yi jimamin rasuwar wannan yaro. 

“Yaro ne mai neman ilimi, yaro ne mai haƙuri, yaro ne mai son cigaba da neman ilimi, don a wancan satin mu ka gama tsari da makarantar da zan sa shi na haddar Alƙur’ani, amma ga shi Allah ya ɗauki abin sa. Wannan yaro ya yi shahada.

“Mu na roƙon Allah ya amshi shahadar sa, Allah ya ba mu haƙuri ga baki ɗaya, da ni mariƙin sa da mahaifin sa da al’ummar Annabi Muhammadu (s.a.w.), baki ɗaya.” 

Alhaji Magaji Sulaiman, Shugaban Sulson Production… mahaifin Muhammadu Mubarak

Maikano, wanda babban furodusa ne, ya bayyana wani abu da ke faruwa a kowane mako, ya ce, “A wannan Juma’ar da mu ke magana, hankali na a tashe ya ke, domin kowace Juma’a, haka na ke sanya su a gaba da sauran ‘ya’ya na, tun wurin ƙarfe 10:00 na safe, tun daga Kabala Costain za mu taka a ƙafa har masallacin Al-Manar, mu je mu zauna mu yi ta ibada, mu yi ta zikiri, har liman ya zo ya yi huɗuba, sannan mu dawo gida. Yau ita ce Juma’a ta farko da zan tafi Juma’a ba tare da Mubarak ba da sauran ‘ya’ya na a gaba ba. 

“Ina roƙon Allah ya amshi shahadar sa, ya kuma gafarta masa, in tamu ta zo, Allah ya sa mu cika da kyau da imani.”

A labarin rasuwar Mubarak da mujallar Fim mujallar Fim ta buga, mahaifin marigayin, Alhaji Magaji Sulaiman, wanda shi ma babban furodusa ne da ke zaune a Zariya, ya shaida mana cewa ba a ga gawar yaron nasa ba. To Allah cikin ikon sa, a ranar Laraba, 7 ga Disamba, wato bayan kwana uku, aka ga gawar. 

An yi masa sutura a gidan Maikano a nan Kabala, kuma Alhaji Magaji Sulaiman da ‘yan’uwan sa da ɗimbin jama’a sun halarta.

Allah ya jiƙan Mubarak, amin.

Loading

Tags: Abdullahi Maikano UsmanalhiniKabala CostainKogin KadunaMagaji SulaimanMOPPANMubarakSulson Production
Previous Post

Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya ta karrama mawallafin Blueprint, Mohammed Malagi

Next Post

Batun ‘mutuwar’ Kannywood: Darakta Hafizu Bello ya yi wa Salisu Officer martani

Related Posts

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
Next Post
Sir Hafizu Bello

Batun 'mutuwar' Kannywood: Darakta Hafizu Bello ya yi wa Salisu Officer martani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!