WATA sabuwa, inji ‘yan caca! Fitattun mawaƙan nan Ado Isa Gwanja da Mubarak Abdulkarim (Mr. 442) sun nuna aniyar su ta fitar da sabuwar waƙar ‘Chass’ ta haɗaka duk da yake su na fuskantar ƙalubale daga kotu da ‘yan sanda da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano.
Mujallar Fim ta ba da labarin yadda wasu lauyoyi su ka shigar da ƙara a kan Gwanja, shi kuma Mr 442 da abokiyar aikin sa Safara’u ana neman su ruwa a jallo domin a kama su a kai su kotu.
Da alama mawaƙan ba su daddara ba, shi ya sa za su fitar da sabuwar waƙar wadda ake ta ce-ce-ku-ce a kan ta.
Mr. 422 shi ne ya fara ɗora fostar waƙar a Instagram mai ɗauke da hoton Gwanja daga gaba da kuma shi a bayan sa, dukkan su sun sanya manyan kaya na Haussawa, sannan daga gaban hoton an rubuta ‘Remix Chass’, a can sama kuma daga hagu aka rubuta “Ado Gwanja x Mr. 442”.
Wakilin mu ya ruwaito cewa a waƙar ‘Chass’ babu kalmomin batsa, sai dai wasu sun ɗauki kalmomin “a sosa” batsa ce.
Shi kuwa Mr. 442, yawancin waƙoƙin sa na batsa ne, shi ya sa yanzu za a jira a ji idan sabuwar waƙar ta ‘Chass’ an canza mata salo zuwa irin waƙoƙin da ya ke yi ko kuma ta kauce wa haka don gudun shiga matsala da hukuma.
Tuni wasu daga cikin abokan sana’ar mawaƙan sun ɗauki fostar su na wallafawa a shafukan su na soshiyal midiya.
Amma dai Gwanja bai ɗora ta a shafin sa ba har yanzu.
Idan kun tuna, mawaƙin ya faɗa wa mujallar Fim cewa shi ba zai ce komai a kan muhawarar da ake tafkawa ko matakin da hukuma ta ɗauka a kan sa ba.
Comments 1