• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ubalen Danja ya zama angon Nana A’isha

by DAGA ABBA MUHAMMAD
October 31, 2020
in Ranar Murna
0
Haruna Shu'aibu (Ubalen Danja) tare da amaryar sa Nana A'isha Isah a wurin dinar auren su

Haruna Shu'aibu (Ubalen Danja) tare da amaryar sa Nana A'isha Isah a wurin dinar auren su

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
RANA ba ta ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, inji Hausawa. To, wannan uwar ɗiyar dai ba ta ji kunya ba, domin kuwa ta taimaka wa matashin jarumin nan na kamfanin 2-Effects Empire mazaunin Kaduna, wato Haruna Shu’aibu, ya yi bankwana da kwanan shago. 
 
Jarumin, wanda aka fi sani da Ubalen Danja, ya yi sa’ar samun auren sahibar sa, wacce ta yi nasarar shiga gaban tarin ‘yanmatan da ke kokuwar samun Ubale a matsayin miji. 
 
An dai ɗaura auren Ubalen Danja da Nana A’isha Isah a ranar Juma’a, 30 ga Oktoba, 2020 da misalin ƙarfe 1:15 na rana, bayan an idar da sallar Juma’a a Masallacin Juma’a da ke layin Ɗanfodiyo, Unguwar Sanusi, Kaduna, a kan sadaki N80,000.
 
Waɗanda da su ka a halarci ɗaurin auren sun haɗa da ubangidan angon, Sani Musa Danja, da Wassh Waziri Hong, Tukur Musa (TK), Sadiƙu Atis,  Abdullahi Jiya Da Yau, Alhaji Ahmad Maiyaƙi, Alhaji Sabo Maiyaƙi, Hamza Isah (Super), Ibrahim Baba Iro, Salisu Loto, Auwal D.G., Muhammad Yaro, Muhammad Busra, Isah Idris, Abdulrasheed Muhammad, Abubakar Alim, da Musa Ahmad.
 
Kafin ranar ɗaurin auren, wato ranar Laraba, 28 ga wata, an yi wasan ƙwallon ƙafa a Filin Wasa na Ahmadu Bello inda aka buga tsakanin ‘yan Kannywood da Sardauna Crescent FC. ‘Yan Kannywood su ne ɓangaren ango, Sardauna Crescent FC kuma ‘yan ɓangaren amarya waɗanda su ka lallasa ‘yan ɓangaren ango da cin biyu ba ko ɗaya.  
 
Wasu daga cikin ‘yan fim da su ka halarci wasan ƙwallon sun haɗa da Umar M. Shariff, Abdul M. Shariff, Ummah Shehu, Khairat Abdullahi, Umar MB, Ɗanladiyo Mai Atamfa, Ibrahim Mai Gala, Tukur Musa (TK), Sabi’u M. Gidaje, A.A. Rasheed Kabala da sauran su.  
Daga hagu: KB 2-Effects, Sani Danja, Umar M. Shariff da Wassh Waziri Hong a wurin dina
A  daren Juma’a da misalin ƙarfe 8:00 na dare kuma aka shirya bikin dina a wani filin makarantar Betty Queen da ke Layin Damask a Sardauna Crescent. 
 
‘Yan fim da mawaƙa sun yi wa Ubale kara, domin sun baje kolin su. Bayan shigowar ango da amarya cikin filin, an buɗe taro da addu’a, daga nan aka shiga nishaɗantar da taron. 
 
Mawaƙa da su ka haɗa da Tukur Musa (TK), Hamza Super da Abdullahi Jiya da Yau sun nishaɗantar da taron da waƙar da su ka rera wa ango da amarya. 
 
Umar M. Shariff, Sani Musa Danja, Yusuf Lazio da sauran mawaƙa da ‘yan fim su ka halarci bikin sun ci gaba da nishaɗantar da taron har zuwa ƙarfe 10:00 na dare, inda a lokacin ne aka sallami kowa.
Umar M. Shariff da Amal Umar su na nishaɗantar da taron
‘Yan fim da mawaƙa da su ka halarci bikin sun haɗa da Sani Danja,  Umar M. Shariff, Wassh Waziri Hong, Abubakar Hunter, Sadiƙu Atis, Ibrahim Saminaka, Yusuf Lazio, Ibrahim Mai Gala, Auta Waziri, S.S. Danko,  Auwal D.G., A.A. Rasheed Kabala, Amal Umar, Ummah Shehu, Fati S.U. Garba, Ummi B.Y., Hadiza Jully, Hauwa Ayawa,  Teema Yola, Karima Dikko da sauran su.
 
Mu na addu’ar Allah ya ba ma’auratan zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.
 
Bayan an tashi daga dina, wakilin mujallar Fim ya ɗan zanta da ango don jin irin yadda ya tsinci kan shi a wannan rana. Sai Ubale ya ce, “Ina godiya ga Allah da ya nuna min wannan rana ta farin ciki a gare ni. Tun ana cewa saura rana kaza, yau ga shi Allah ya sa mun ga wannan rana cikin ikon sa da yardar sa.
 
“Abin da ya fi burge ni da ɗaukar hankali na a yau shi ne yadda masoya na da ‘yan’uwa na su ka nuna min cewa ni ma ɗan dangi ne, domin na yi mamakin yadda na ga taron jama’a tun daga wurin ɗaurin aure har zuwa nan inda mu ka yi dina. Wannan ba ƙaramin abin alfahari ba ne a gare ni, wanda ba zan taɓa mantawa da wannan rana ba. 
 
“Kuma Allah cikin ikon sa an yi an gama lafiya.
“Sannan kuma ‘yan’uwa na, abokan sana’a na ‘yan fim da su ka taso daga Kano, wasu ma daga Jihar Neja, wasu daga nan Kaduna, babu abin da zan ce masu sai Allah ya saka masu da alheri. Allah kuma ya maida su gidajen su lafiya.
Daga hagu: Teema Yola, Fati S.U. Garba, Sadiƙu Atis, Ummah Shehu da Hauwa Ayawa
“Sai kuma ubangida na, Sani Musa Danja, babu abin da zan ce masa sai godiya domin ya na shigowa Kaduna babu abin da ya fara yi sai ziyartar mahaifiya ta; ya je sun gaisa da ita. Kuma a wannan rana duk abin da aka yi shi ne a kan gaba. Wannan ya nuna min cewa ni da shi mu na zama na amana. Ina godiya a gare shi matuƙa.
 
“Sai kuma abokai na da su ka tsaya ka’in da na’in don ganin cewa an yi wannan al’amari ba tare da an samu matsala ko jin kunya ba, ina miƙa godiya ta a gare su, domin sun yi min komai, sun nuna min ƙauna. Babu abin da zan ce masu sai dai Allah ya saka masu da alheri. 
 
“Masu mata ɗaya a cikin su Allah ya sa su ƙara, waɗanda ba su yi ba kuma Allah ya ba su su ma su yi auren. 
 
“Ku ma kuma mujallar Fim ina yi maku godiya da irin gudunmawar da ku ke ba ni. Na gode, Allah ya bar zumunci.”
Sani Musa Danja ya na waƙa a wurin dina

Loading

Previous Post

An karrama minista Sadiya da kyauta mafi daraja kan aikin agajin korona

Next Post

Rahama Sadau ta yi tir da masu saɓon Annabi da masu zagin ta

Related Posts

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
An ɗaura auren darakta a Kannywood, Al-Amin Ciroma da ‘yar’uwar sa Sharifatu
Ranar Murna

An ɗaura auren darakta a Kannywood, Al-Amin Ciroma da ‘yar’uwar sa Sharifatu

May 2, 2025
Ƙarshen tika-tika, tik! A’ishatulhumaira ta zama matar Rarara ta huɗu
Ranar Murna

Ƙarshen tika-tika, tik! A’ishatulhumaira ta zama matar Rarara ta huɗu

April 25, 2025
Darakta Al-Amin Ciroma zai yi amarya a watan gobe, shekaru biyu bayan mutuwar auren sa da Wasila Isma’il 
Ranar Murna

Darakta Al-Amin Ciroma zai yi amarya a watan gobe, shekaru biyu bayan mutuwar auren sa da Wasila Isma’il 

April 20, 2025
Ahlan tare da 'yar sa Hassana, amaryar mako mai zuwa
Ranar Murna

Jarumi a Kannywood, Ahlan zai aurar da ‘yar sa Hassana

February 16, 2025
Daɗi kan daɗi: Marubuciya Bilkisu Yusuf Ali ta samu jika da digirin digirgir
Ranar Murna

Daɗi kan daɗi: Marubuciya Bilkisu Yusuf Ali ta samu jika da digirin digirgir

December 20, 2024
Next Post
Biyu daga cikin hotunan Rahama Sadau da su ka jawo ka-ce-na-ce

Rahama Sadau ta yi tir da masu saɓon Annabi da masu zagin ta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!