• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Umar M. Shariff: Nasihar mahaifin mu kafin ya rasu jiya

by DAGA ABBA MUHAMMAD
March 3, 2020
in Labarai
0
Marigayi Malam Muhammad tare da ɗan sa Umar M. Shariff a wani lokaci can baya

Marigayi Malam Muhammad tare da ɗan sa Umar M. Shariff a wani lokaci can baya

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
FITACCEN jarumi kuma mawaƙi Umar M. Shariff ya bayyana cewa ba zai taɓa mantawa da nasihar da mahaifin sa ya riƙa yi masa ba kafin rasuwar sa a jiya.
 
Ya faɗi haka ne a lokacin da ya ke zantawa da mujallar Fim a yau a wajen zaman makokin rasuwar mahaifin nasa da ake yi a gidan su da ke Layin ‘Yankifi, unguwar Rigasa, cikin garin Kaduna.
 
Shi mahaifin na su Umar, wato Malam Muhammad Shariff, ya rasu ne a daren jiya Litinin,  2 ga Maris, 2020 a Asibitin Sultan da ke Titin Maƙarfi, a Rigasa, Kaduna.
 
Marigayin, mai kimanin shekara  75 a duniya, ya rasu ne bayan ya sha fama da rashin lafiya.
 
An yi masa sallah da misalin ƙarfe 8:30 na safe a gidan sa.
 
Mamacin ya rasu ya bar mata ɗaya da ‘ya’ya takwas – maza 3, mata 5. 
 
A cikin ‘ya’yan akwai fitattun ‘yan fim su uku, wato Umar M. Shariff, Abdul M. Shariff da Mustapha M. Shariff. 
 
Umar dai mawaƙi ne jarumi. Haka shi ma yayan sa Abdul jarumi ne yayin da babban yayan su, Mustapha, shi kuma darakta ne, kuma mai koyar da rawa a Kannywood. 
 
‘Yan fim da mawaƙa da dama sun halarci jana’izar dattajon, kuma sun je gaisuwa.
 
Sun haɗa da Abdullahi Abbas, Malam Yahaya Makaho, Abu Sarki, Sulaiman Sir Zeesu,  Abdul D. One, Sadiqu Atis, Sabi’u Gidaje, Haruna Gidaje, Nafi’u Gidaje, Ubale 2-Effects, Ɗanladiyo Mai Atamfa,  Ibrahim Shasha, Alfazazi Muhammad, Mai Gala, Yusuf Lazio, Abdul FKD, Tukur Musa TK, Abdullahi Jiya Da Yau, Ibrahim Usman (Liti), da sauran su.  
 
A wajen zaman makokin ne mujallar Fim ta yi wa Umar M. Shariff ta’aziyya tare da tambayar sa abin da zai ce game da wannan babban rashi.
 
Sai ya amsa da cewa: “Da farko dai ina yi wa Allah godiya, wanda shi ne ya tsara wannan al’amari, kuma babu wanda zai iya canzawa.
 
“Kuma mu na farin ciki da hakan, musamman ganin ta hanyar rashin lafiya ne, kuma mun yi iya ƙoƙarin mu don ganin cewa mun ceto rayuwar sa, amma tun da Allah ya nufa, haka ya tsara masa rayuwar sa, to mu na farin ciki da dukkan hukuncin da Allah ya ɗauka a kan sa. 
 
“Don haka mu na yi masa addu’ar Allah ya yi masa rahama, ya kuma gafarta masa.”
Ana rufe Malam Muhammad a kushewar sa
Da wakilin mu ya tambaye shi abin da mahaifin nasu ya ke yawan faɗa masa wanda ba zai taɓa mantawa da shi ba, sai Umar ya ce, “Gaskiya, abubuwan da yawa. Saboda  kullum idan za mu zauna da shi nasiha ce kawai tsakanin mu, nasiha ta yadda za mu zauna da kowa lafiya, yadda za mu gudanar da al’amuran rayuwa  da kuma yadda za mu bi sauran abubuwa yadda su ka da ce. 
 
“Kullum nasihar sa kenan a gare mu. 
 
“Hatta lokacin da ya ke kwance a kan gadon asibiti, sai da ya yi mana wannan nasiha ta mu zauna da kowa lafiya, mu ji tsoron Allah, kuma duk abin da za mu yi mu nemi halal ɗin mu. 
 
“Wannan shi ne abin da ba zan taɓa mantawa ba in na tuna da mahaifin mu.”
 
To, Allah ya jiƙan Malam Muhammad, ya sa mutuwar sa hutu ce, amin.
Ana yi wa Umar, Abdul da Mustapha gaisuwa jim kaɗan bayan an kammala rufe mahaifin su
Abdul da Umar M. Shariff su na yi wa mahaifin su addu’a a jikin kabarin sa

Loading

Previous Post

Na samu harkar fim ba yadda na ke jin ta ba – Fatima Fulani

Next Post

Irin Tatsunniyoyin Da Aliyu Kankara Ke Yaɗawa Game Da Shata

Related Posts

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry
Labarai

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry

June 15, 2025
Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
Next Post
Aliyu Kankara da littafin sa mai cike da almarori game da Shata

Irin Tatsunniyoyin Da Aliyu Kankara Ke Yaɗawa Game Da Shata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!