SHUGABAN Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), Dakta Ahmad Sarari, ya yi kira ga ‘yan Kannywood da ke cacar baki kan maganar nan ta ‘yar wasa Ladin Cima (Tambaya) da su dakata haka nan domin a yi gyara a al’amarin.
Sarari ya faɗi haka ne a yau a cikin wata takarda ga manema labarai wadda kakakin ƙungiyar na ƙasa, Malam Al-Amin Ciroma, ya rattaba wa hannu.
Idan kun tuna, muhawara ta ɓarke ne a Kannywood a ranar Alhamis da ta gabata sakamakon iƙirarin da Hajiya Tambaya ta yi a hirar ta da BBC Hausa cewa ba a taɓa biyan ta sama da N5,000 a aikin fim ba.
Jarumi Ali Nuhu da darakta Falalu Ɗorayi da ma wasu ‘yan fim sun fito sun ƙaryata iƙirarin nata, su ka ce su kan su sun yi aiki da ita inda su ka biya ta N40,000 ba ma sau ɗaya ba.
Fitaccen mawaƙi a Kannywood, Naziru M. Ahmad (Sarkin Waƙa), ya mayar da martani ga Ali da Falalu inda ya ce babu Allah a ran su.
Haka kuma mawaƙin kuma jarumi ya yi nasa iƙirarin inda ya ce ba a sanya mata a fim a Kannywood sai an kwanta da su, abin da ya hayaƙa Ƙungiyar Matan Kannywood (K-WAN) har ta sha alwashin za ta gurfanar da shi a kotun Musulunci a kan tuhumar ɓata suna idan har bai janye wannan ƙazafi daga yau zuwa ranar Alhamis ba.
Amma a sanarwar da MOPPAN ta bayar a yau, ƙungiyar ta lura da cewa “lamarin na ɗaukar hanya ta daban” kuma “zancen na ci gaba da jan hankalin al’umma, musamman mabiya lamurran finafinan Hausa, inda kowa ke tofa albarkacin bakin sa dangane da zancen.”
Kakakin MOPPAN, Ciroma, ya ce, “Hakan ta sa wasu masu ruwa da tsaki su ka fara kiraye-kiraye ga shugabannin MOPPAN da su shiga su magance muhawarar.”
A cewar sa, kiraye-kirayen sun sa MOPPAN “ta ɗauki ƙwararan matakai, da haɗin gwiwar sauran ƙungiyoyi kamar ƙungiyar masu shirin fim ta Arewa, wato AFMAN, dangane da lamarin.”
Ya ce, “Kaɗan daga cikin matakan su ne MOPPAN ta jawo hankalin dukkanin ɓangarorin da su dakata da musayar yawu, kuma sun dakatar.
“Haka kuma MOPPAN za ta cimma matsaya ta musamman kan lamarin, bayan shirye-shirye da dama da ta gudanar.
“A ƙarshe, shugabannin ƙungiyoyin su na ƙara kira ga dukkanin ‘ya’yan Kannywood da su kasance masu kishin masana’antar, su kuma daina bin son zuciya, da zai iya kawo manyan matsaloli ga sana’ar fim baki ɗaya.”
Ciroma ya ƙare da cewa, “MOPPAN za ta cimma matsaya bayan kammala tattaunawa (da) sauran ƙungiyoyi da masu ruwa da tsaki a harkar da kuma ‘elders’.”