A’ISHA Isah Usman, wadda aka fi sani da Ummi Kano, ta na daga cikin matasan mawaƙa waɗanda Allah ya yi wa nasibi a wannan zamanin. Ta yi waƙoƙi masu yawa waɗanda su ka shafi zamantakewa da yabon Manzon Allah (s.a.w.). Sai dai an fi sanin ta a waƙoƙin siyasa, musamman a ɓangaren Kwankwasiyya. Domin jin irin faɗi-tashin da ta sha kafin ta kai ga duniya ta san ta, wakilin mu ya tattauna da ita kwanan nan a Kano.
FIM: Da farko za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatun mu.
UMMI KANO: To da farko dai suna na A’isha Isah Usman, amma dai an fi sani na da sunan Ummi Kano wanda asalin sunan kaka ta ne wadda ta haifi baba na. Kuma a Kano aka haife ni a Rafin Kuka, nan ce mazaɓa ta. Shekaru na a yanzu 25.
Ta ɓangaren karatu kuma, na yi makarantar firamare ta Ja’oji, da na gama na shiga sakandare ta Gandun Albasa. Ban gama ba aka cire ni aka yi mani aure. Daga nan kuma ban ci gaba ba.
FIM: To yaya aka yi ki ka fara harkar waƙa?
UMMI KANO: E to, gaskiya sha’awa ce, don tun kafin na yi aure ina ɗan jin daɗin waƙar har ya zama na fara. Amma dai asalin waƙar da na fara yi ta yabo ce. Don a lokacin ba zan manta ba na kan je wajen maigida na, Tijjani Gwandu, ya rubuta mani, sai na ɗora. Amma dai akwai marubucin waƙa ta wanda har yanzu shi ne ya ke rubuta mani waƙa, wato Aliyu Musa Nassarawa. To bayan aure na ya mutu ne sai na ci gaba da yin waƙar, wanda kuma na fi karkata ga waƙoƙin siyasa da na soyayya.
Waƙar da ta yi fice aka san ni da ita a fannin soyayya ita ce ‘So Da Ƙauna’. A waƙar siyasa kuma wadda aka san ni da ita waƙar ‘Mai Amana’ daga tafiyar Amana, wadda na yi wa Abba Kabir Yusuf, wato Abba Gida-Gida. Sai kuma waƙar da mu ka hau mu biyu ni da Ali Artwork, ita ce ‘Ga Zaki Maci Abokan Gaba’.
Akwai waƙoƙi na na siyasa masu yawa da ba za su lissafu ba. Haka ma na soyayya.
FIM: Ku mawaƙan siyasa ba ku damu da yin kundi na waƙa ba. Ko me ya sa?
UMMI KANO: To saboda ka san ita waƙar siyasa ana yin ta ne a daidai lokacin da ake yaƙin neman zaɓe, don haka ne za ka ga ba mu damu da mu yi kundin waƙa ba, sai dai mu yi ta tura wa mutane. Amma waƙoƙi na na soyayya a yanzu ma ina ɗora su a YouTube.

FIM: To ko yaya Ummi Kano ta ɗauki harkar waƙa?
UMMI KANO: Gaskiya waƙa sana’a ce kuma mun samu alheri a cikin ta, don ta sanadiyyar waƙa an ba ni mota, kuma na samu alheri mai yawa, har yanzu ma ina ci gaba da samu. Don ba zan manta ba, da wani tsautsayi ya same ni duk manyan ‘yan siyasar nan babu wanda bai taimaka mani ba. Abba Gida-Gida, jagoran mu Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, da sauran jama’a duk sun tallafa mani. A nan na ƙara tabbatar da cewa ina da ƙima a wajen mutane.
FIM: Waɗanne irin matsaloli ki ka samu a harkar ki ta waƙa?
UMMI KANO: To babbar matsalar da na samu ita ce wadda ina tafiya a kan hanya mutane su ka tare ni su ka sassare ni, su ka sace mini wayoyi na. Allah ne ma ya yi da sauran rai na! Amma dai, cikin ikon Allah, Abba Gida-Gida ya sa aka kai ni asibiti na samu lafiya. Amma duk wanda ya ga yadda aka ji mani ciwo ya san na sha wahala. Amma cikin sati biyu na warke.
FIM: Menene saƙon ki na ƙarshe?
UMMI KANO: To saƙo na na ƙarshe dai shi ne ina kira ga mawaƙa su riƙe sana’ar su ta waƙa da muhimmanci, domin sana’a ce da ta ke da rufin asiri, don ni na ga hakan. Kuma ina fatan Allah ya haɗa kan mu.