(Mun ciro daga gidan yanar BBC Hausa – Edita)
KAMAR yadda ya faru a shekara ɗaya zuwa biyu da su ka gabata, a bana ma mawaƙan Hausa na zamani su ne kan gaba wajen fito da sababbin waƙoƙi tare da mamaye zukata da kuma kafafen yaɗa labarai, musamman gidajen rediyo da soshiyal midiya. Hakan ya sa su ne aka fi yayi fiye da waƙoƙin makaɗan gargajiya irin su Shata, Ɗanƙwairo, Uji, Uwaliya, Barmani ko Ɗan’anace.
Su mawaƙan gargajiya, babu wata sabuwar waƙa da ta fito daga gare su a bana har ta yi suna tare da mamaye zukata. Hasali ma dai yawancin mawaƙan gargajiya sun mutu, ‘yan ƙalilan ɗin da su ka rage – irin su Atta Dabai, Musa Ɗanbade, Shehu Ajilo Ɗanguziri da Babangida Kakadawa – ba su yi wata sabuwar waƙa da za a ce ana zancen ta ba a cikin wannan shekara. Yawanci a kan saka su a rediyo ne saboda sabo, kuma ana jin su a kafafen soshiyal midiya irin su Facebook, WhatsApp, YouTube da Telegram inda aka buɗe dandali daban-daban domin su. Yawancin masu sauraren su ɗin ma manya ne ko matasan da ke gab da shiga da’irar dattijai. Hasali ma dai, in ban da Musa Ɗanbade da ya yi wa Sarkin Jiwa waƙa, da kuma Gwaggo Marka daga Jihar Nassarawa, babu wani mawaƙin gargajiya da za a ce ya yi wata sabuwar waƙa da aka saurare ta sosai a bana.
Wani abin lura kuma shi ne, mawaƙan zamani (kusan dukkan su masu amfani ne da fiyano wajen kiɗa) waɗanda su ka ciri tuta a shekara ɗaya ko biyu baya, yawanci su ɗin ne dai su ka riƙe kambin su na jagaban mawaƙa a 2019. Sun yi waƙoƙi masu yawan gaske waɗanda su ka yi fice, ta yadda aikin zaƙulo guda goma kacal mafi shahara a cikin su ya kasance babban tasku. Duk da haka, mun yi bincike mai zurfi a masana’antar finafinai ta Kannywood tare da bibiyar wasu gidajen rediyo na FM da na talabijin da masu sayar da waƙoƙi, inda bayan mun tace sai mu ka zaƙulo goma da aka fi so ko aka fi saurare a wannan shekara ta 2019. Ga su kamar haka:
1. ‘Hafeez’ – UMAR M. SHAREEF (tare da Khairat Abdullahi):
Waƙar ‘Hafeez’ ta fito ne a fim ɗin ‘Hafeez’ na furodusa Abubakar Bashir Maishadda, wanda Ali Nuhu ya bada umarni. Fitaccen mawaƙi kuma jarumi, wanda ya na kan gaba a cikin jerin matasan jaruman da tauraron su ke haskawa a wannan zamani, wato Umar M. Shareef, shi ne ya rubuta waƙar tare da rera ta tare da Khairat Abdullahi, kuma shi ne ya hau waƙar a fim ɗin tare da jaruma Hassana Muhammad.
Waƙa ce tsakanin masoya biyu. A cikin ta, Umar da Khairat sun nuna ƙwarewa wajen zuba kalaman soyayya da kuma raushin murya. Waƙar ta yi fice matuƙa, musamman a wurin bukukuwa.
Waƙar ta ƙara shiga zuciyar masoyan mawaƙin bayan an nuna fim ɗin a gidan sinima na Film House da ke Ado Bayero Mall, Kano. Ita ce waƙar da ta fi kowace waƙar fim yin fice a shekarar 2019.

2. ‘Hafeez’ – NURA M. INUWA (tare da Zuwaira Abdulsalam):
Fitaccen mawaƙi Nura M. Inuwa shi ma ya yi waƙa da aka saka a fim ɗin ‘Hafeez’ na furodusa Abubakar Bashir Maishadda. Kamar yadda aka sani, kusan dukkan finafinan Maishadda daga Umar M. Shareef, Nazifi Asnanic, sai Abdul D. One ne su ke yi masa waƙoƙin su, to amma a wannan karon, kwatsam, sai aka ji Nura M. Inuwa ya yi masa waƙoƙi a wasu finafinan sa, waɗanda su ka haɗa da ‘Hafeez’.
Waƙar ta soyayya ce, inda mawaƙin ya yi amfani da kalamai masu ratsa zuciya kamar yadda aka san shi da yi. Fitaccen mawaƙi kuma jarumi Umar M. Shareef ne ya hau waƙar a fim ɗin tare da Maryam A.B. Yola, A’isha Humaira, Maryam Yahya, Bilkisu Shema, Firdausi Muhammad, Hassana Muhammad da Amal Umar, inda dukkan su kowacce ta na neman soyayyar Hafeez.
Mawaƙin ya canza salo a ƙarshen waƙar, kamar yadda ya kan yi a wasu waƙoƙin sa. Waƙar sai ta zama kamar kishiya ga wadda Umar M. Shareef ya rera, wadda sunan su ma ɗaya. Hakan ya sa masoyan mawaƙan su ka dinga musu kan wacce ce ta fi daɗi.
3. ‘Kar Ki Manta Da Ni’ – ABDUL D. ONE (tare da Murja Baba):
Wannan waƙa ta fito ne a fim mai sunan ta, wato ‘Kar Ki Manta Da Ni’.
Fitaccen matashin mawaƙi Abdul D. One, wanda tauraruwar sa ke haskawa a wannan zamani, shi ne ya rubuta ta kuma ya rera ta, inda nan da nan ta yi farin jini musamman a fim ɗin ‘Kar Ki Manta Da Ni’ na darakta Ali Nuhu.
Duk da cewa shi ma ubangidan Abdul ɗin, wato Umar M. Shareef, ya yi waƙoƙi a fim ɗin, amma sai mutane su ka fi son ta Abdul ɗin.
Waƙar ta soyayya ce wadda a cikin ta mawaƙin ya ba soyayya haƙƙin ta yadda ya kamata. Ya baje basira da hazaƙa ta yadda idan masoya su na sauraren ta za su ji kamar babu wani abu da ya kai soyayya daɗi a duniya, musamman masoyan da su ka yi wa juna alƙawarin ba za su taɓa mantawa da juna ba. Mata, musamman sababbin shiga zarafin soyayya, su na son waƙar matuƙa.
4. ‘So Na Amana’ – GARZALI MIKO – (tare da Zuwaira Isma’il)
Jarumi Garzali Miko, wanda a bana ya rikiɗe zuwa mawaƙi, ya shigo dandalin waƙa da ƙafar dama. Ana kiran Garzali sabon mawaƙi ne domin bai daɗe da fara waƙa ba. Duk da haka cikin ƙanƙanin lokaci ya yi fice.
Sai dai kuma masu saurare da dama ba su san cewa shi da kan shi ne ya rera waƙoƙin ba, saboda murya da salon waƙoƙin sa sun yi kama da na mawaƙi Hamisu Breaker Ɗorayi ko Adam A. Zango.
Wani abu da ya ƙara yayata waƙar shi ne bayan an sake ta a YouTube, shi ne kama daraktan waƙar, Sunusi Oscar 442, da hukuma ta yi har ya yi zaman gidan yari na ‘yan kwanaki. Daga nan sai ta kasance kowa ya na so ya ga abin da aka yi a cikin waƙar da har ya yi sanadin sakaya daraktan. Dalilin kamun da aka yi wa Sunusi Oscar ya sa duk inda ka bi a arewacin Nijeriya ko ka saurari kafafen sadarwa na zamani, za ka ji kawai ana ta yaɗa waƙar.
5. ‘Na Yi Sa’a’ – HAMISU BREAKER ƊORAYI:
Hamisu Sa’id Yusuf, wanda aka fi sani da Hamisu Breaker Ɗorayi, fitaccen mawaƙi ne wanda ke kan ganiyar sa. Tauraron sa ya na haskawa yadda ya kamata, domin da wuya ka ga ya fitar da sabuwar waƙa ba ta yi tashe ba. A wannan shekara ta 2019, waƙar sa ta ‘Na Yi Sa’a’ ita ce waƙar sa da ta zagaya ko’ina, ta kasance waƙar da mata su ka yi ta ɗaukar bidiyon kan su da wayar su, su na bin ta su na ɗorawa a shafukan su na Instagram. Har ta kai ga wasu yara ƙanana, mace da namiji, su ka kwaikwayi rawar da Hamisun da jaruma Rakiya Moussa Poussi su ka yi. Waƙar ta ɗau hankalin matasa sosai.
6. ‘Abba Gida-Gida Abba’ – TIJJANI GANDU:
Tijjani Gandu ya fara yin tashe ne da waƙar ‘Yar Maye’ a ‘yan shekarun baya, amma kuma daga bisani sai aka ji shi tsit, kamar ba a taɓa yayin sa ba a masana’antar Kannywood. A baya ya yi waƙoƙi masu zafi da aka yi finafinai da su.
Kwatsam, a bana sai ga mawaƙin ya faso fage da waƙa mai taken ‘Abba Gida-Gida Abba’ gab da zaɓuɓɓukan shekarar 2019. Waƙa ce ta yaƙin neman zaɓen Alhaji Abba Kabir Yusuf wanda aka tsayar a matsayin ɗan takarar zama gwamnan Jihar Kano a jam’iyyar PDP. Lokaci guda waƙar ta bazu a jihohin Arewa kamar wutar daji. Duk lungu da saƙon da ka shiga za ka ji ana jin waƙar. Maza da mata, yara da manya su na rera ta. ‘Yan mata daga jihohi daban-daban sun yi ta ɗaukar bidiyon kan su, su na bin waƙar, su na sakawa a shafukan su na Instagram don nuna ƙaunar su ga waƙar da kuma ɗan takarar. A Gombe, wani mawaƙi ya ɗau samfur ɗin waƙar ya yi ‘Inuwa Gida-Gida’.
Dalilin waƙar ta Tijjani Gandu ne aka daina kiran ɗan takarar na PDP da cikakken sunan sa, sai Abba Gida-Gida.
Mawaƙin ya kambama gwanayen sa a cikin waƙar. An tabbatar da cewa waƙar ta taimaka wa ɗan takarar wajen samun ƙarin magoya baya a zaɓen.
7. ‘Baban Abba Ganduje’ – DAUDA ADAMU KAHUTU (RARARA):
Mawaƙin siyasa Dauda Adamu Kahutu, wanda ake yi wa laƙabi da Rarara, ya maida martani ga mawaƙin ‘Abba Gida-Gida’, wato Tijjani Gandu. Rarara ya yi waƙar ne bayan Tijjani Gandu ya fitar da waƙar ‘Abba Gida-Gida Abba’, inda shi kuma ya kira tasa waƙar da ‘Baban Abba Ganduje’.
Waƙar kusan daga farkon ta har ƙarshen ta habaici ce. Wannan ya sa masoyan ‘yan takarar su ka samu abin da su ke so; masoyan Gwamna Ganduje su ka riƙa yaɗa waƙar don ɓata wa masoyan Abba rai. Waƙar ta yi fice, ta inda ko’ina ka shiga za ka ji ta. Har a gidajen biki ana saka ta don a nishaɗantar da mahalarta bikin.
Waƙar ta ƙara tashe ne bayan zaɓe da aka sanar da cewa Ganduje ne ya sake lashe zaɓe.
8. ‘Sabada’ – UMAR M. SHAREEF da KOREDE BELLO:
Waƙar ‘Sabada’ ta zo da wani sabon salo da ba a saba ji daga mawaƙan Hausa na wannan zamani ba. Umar ya yi tattaki tun daga Kaduna zuwa Legas ya yi waƙar tare da fitaccen matashin mawaƙi Korede Bello na kamfanin waƙoƙi mai suna Mavin Records, mallakin fitaccen mawaƙi Don Jazzy. Korede Bello ya yi waƙar ne cikin harshen Turanci, inda shi kuma Umar M. Shareef ya gwamutsa Turanci da Hausa. Umar ya nuna waƙa burin sa ce, kuma ya kama da wuta. Shi kuma Korede ya kama sunan Khadija ne ya na cewa ya na son yadda ta ke rawa shi ma.
Waƙar ta yi daɗi matuƙa, ta inda masoyan Umar su ka yi ta tururuwar neman ta. Haka kuma Umar ya ƙara samun masoya daga Kudu saboda saka Korede da ya yi a waƙar.
Waƙar dai salon hip-hop ce, ba ta nanaye da su Umar su ka saba yi ba. To amma fa ba wannan ba ce waƙar da fara yi da mawaƙan Kudu ba, don kuwa a 2017 ya yi waƙa da fitaccen makaɗi kuma mawaƙi Selebobo. Sai dai wannan da ya yi da Korede ta fi yin fice fiye da waccan, domin ita ‘Sabada’ har bidiyo an yi mata.
9. ‘Cypher’ – YARAN NORTH SIDE
DJ AB, TEESWAGG, LIL PRINCE, JIGSAW
DJ AB, TEESWAGG, LIL PRINCE, da JIGSAW mawaƙan salon hip-hop ne da ke zaune a garin Kaduna. Sun yi waƙoƙi da dama, sai dai wannan waƙar ta haɗaka ce, inda aka nuna su a wani wurin cin abinci su na hira, daga nan ɗaya bayan ɗaya kowannen su ya fara ba junan su labarin sabuwar budurwar da ya yi, har ya ke nuna masu hoton ta a wayar sa a bidiyon waƙar. Nan take duk su ka gane cewa ai yarinya ɗaya su ke nema.
Waƙar ta yi fice wurin samari da ‘yan mata, musamman masu sauraren waƙoƙin hip-hop. Hatta wasu manyan da ƙananan yara su na son ta.
Waɗannan mawaƙa dai tauraruwar su na hasakawa a ɓangaren waƙoƙin hip-hop. Sai dai shi DJ Abba ya ɗauki shekaru ya na jan zaren sa, domin ya yi waƙoƙi da su ka yi suna a baya irin su ‘Su Baaba Ne’, ‘Kumatu’, ‘Kowa Ya Ɓace Don Babar Sa’, ‘Totally’, ‘Babban Yaya’ da sauran su.
10. ‘Tsaya’ – LILIN BABA da UMAR M. SHAREEF:
‘Tsaya’ waƙar haɗaka ce da fitattun mawaƙa su ka rera. Ta bambanta da wasu waƙoƙin da Lilin Baba ke yi, duk da cewa ita ma samfurin ta hip-hop ce, sai dai saka Umar M. Shareef cikin ta ya ƙara mata karsashi domin sun yi amfani da kalamai na soyayya. Duk yarinyar da ta saurari kalaman mawaƙan za ta ji kamar da ita ake yi, domin kalamai ne masu ratsa zuciya.
Mawaƙan sun yi bidiyon waƙar ne da fitacciyar jaruma Rahama Sadau, inda aka nuno su a cikin kantin saida kayayyaki, sun yi ƙoƙarin yi mata magana a dalilin karin waƙar kenan ‘Tsaya’. Bidiyon waƙar ya yi kyau sosai. Har sai da ta kai waƙar ta zama abar maimaitawa a shirin “Top 10” wanda mawaƙi Nomiis Gee ke gabatarwa a tashar talabijin ta Arewa 24.