• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, July 20, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yadda aka yi jana’izar Umar Yahaya Malumfashi Bankaura

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
September 28, 2022
in Labarai
0
Dandazon jama'a a wajen jana'izar Alhaji Umar Yahaya Malumfashi a maƙabartar Tarauni a Kano yau da safe

Dandazon jama'a a wajen jana'izar Alhaji Umar Yahaya Malumfashi a maƙabartar Tarauni a Kano yau da safe

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

DA safiyar yau Laraba aka gudanar da jana’izar fitaccen jarumin Kannywood, Alhaji Umar Yahaya Malumfashi (Bankaura), wanda Allah ya yi wa rayuwa a daren jiya.

Bankaura, wanda ake yi wa laƙabi da Ka-fi-gwamna,  ya rasu ne a wani asibiti mai suna Pinnacle Special Hospital, Kano, bayan ya shafe tsawon watanni ya na fama da rashin lafiya.

An gudanar da jana’izar a gidan sa da ke unguwar Hotoro Tsamiyar Boka da misalin ƙarfe 9 na safe.

Taron jana’izar ya samu halartar jama’a masu yawan gaske daga ciki da wajen masana’antar Kannywood.

An kai shi makwancin sa a maƙabartar Tarauni.

Ana saka marigayi Bankaura cikin kabarin sa

Cikin fitattun jaruman da su ka halarta akwai Alhaji Isa Bello Ja, Alhaji Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama, Malam Alhassan Kwalle, Malam Aminu Baba Ari, da Malam Ado Ahmad Gidan Dabino.

Marigayin dai tsohon ɗan wasan kwaikwayo ne na talbijin da rediyo sama da tsawon shekara arba’in, sannan tsohon ma’aikaci ne a Hukumar kula da Shige da Fice ta Nijeriya (Customs) inda ya yi ritaya a cikin 2020.

Iyalin sa sun faɗa wa mujallar Fim cewa ya rasu ya na shekara 66, ya bar mace ɗaya da ‘ya’ya 15 – mata huɗu, maza goma sha ɗaya.

Bayan an yi jana’izar, mujallar Fim ta ji ta bakin ɗaya daga cikin ‘ya’yan sa, wato Abubakar Umar Yahaya, kan wannan babban rashi da mu ka yi.

Abubakar ya ce: “To, gaskiya mu a matsayin mu na ‘ya’yan sa mun samu kulawa sosai, irin kulawar da mahaifi nagari ya ke yi wa ‘ya’yan sa. Ya ba mu tarbiyya, ya ba mu ilimi, ya koyar da mu zumunci a cikin ‘yan’uwa, da sauran mutane na kusa da shi.

“Kuma ya haɗa kan mu a matsayin mu na ‘ya’yan sa duk da yake mun kasance ‘ya’yan mata uku ne mu ‘ya’yan sa  Ya koya mana haɗin kai da girmama juna.

Allahu Akbar! Kabarin Alhaji Umar Yahaya Malumfashi

“Mu na fatan Allah ya jiƙan mahaifin mu, don mun yi rashin da ba za mu taɓa mantawa da shi ba.”

A game da irin ciwon da baban nasu ya yi, Abubakar, wanda ya na cikin waɗanda su ka yi zaman jinyar sa, ya ce ya sha fama da rashin lafiya wanda ya kai shi ga kwanciya na tsawon wata shida kafin Allah ya karbi abin sa. 

Da mujallar Fim ta tambaye shi yanayin rashin lafiyar, sai ya ƙara da cewa: “Tun a watan Ƙaramar Sallah ya ke kwance daga lokacin da jikin sa ya matsa masa. Da farko an je asibiti ba a gano abin da ya ke damun sa ba, sai aka dawo gida aka ci gaba da magani.

“Sai kuma daga baya aka sake yin bincike, sai aka gano wani ƙari ne ya fito a mafitsarar sa, don haka sai aka shirya za a yi masa aiki. Sai kuma aka gano shi wannan ƙarin idan ya na mataki na 40 ne za a iya cire shi, to shi kuma nasa ya kai har 200 da wani abu, don haka su ka ce sai an fara yin wani aiki a mataki na farko sannan za a yi na biyun da shi ne za a cire. 

“To kuma an yi na farko, kafin a kai ga yin na biyun, sai Allah ya yi masa cikawa.”

To, mu ma a mujallar Fim mu na addu’ar Allah ya jiƙan sa, ya kyautata makwancin sa, amin.

Jama’a su na yi wa mamacin addu’ar samun gafara a bakin kabarin sa
Abubakar Umar Yahaya Malumfashi da mahaifin sa

Loading

Tags: Bankaurajana'iza.jarumaiKannywoodKanomutuwaPinnacle Specialist Hospitalrashin lafiyarasuwaUmar Yahaya Malumfashi
Previous Post

Sadiya Umar Farouq Bazamfariyar ƙwarai ce – Gwamna Matawalle

Next Post

Hotunan ‘aure’ a Kannywood: Me ya sa mutane ba su ganewa?

Related Posts

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu
Labarai

Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu

July 7, 2025
MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 
Labarai

MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 

June 29, 2025
Next Post
Umar Gombe da Hauwa Ayawa a hoton da su ka ɗauka don latsa mutane

Hotunan 'aure' a Kannywood: Me ya sa mutane ba su ganewa?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!