• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, May 18, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yadda Hajiya Sadiya ta kai tallafin gwamnati ga Sokoto saboda ambaliya

by DAGA WAKILIN MU
October 19, 2020
in Nijeriya
0
Tarin kayan abinci da aka raba a Sakkwato

Tarin kayan abinci da aka raba a Sakkwato

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
Gwamnan Jihar Sokoto, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari saboda agajin gaggawa da ya kai wa al’ummar jihar sakamakon bala’in ambaliyar ruwan sama da aka yi a jihar.
 
Ambaliyar ta shafi ƙananan hukumomin Gwadabawa, Illela, Sokoto ta Arewa,  Wammako, Boɗinga da Tambuwal inda ta lalata gonaki da  amfanin gona masu yawan gaske.
 
Gwamnan ya yi yabon ne a ƙarshen makon jiya lokacin da Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta ziyarci jihar domin rarraba kayan agaji tare da ƙaddamar da Shirin Bada Lamuni Ga Matan Karkara, wato ‘Rural Women’s Grant Project’.
 
Ya ce: “Tilas ne in yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari saboda saƙon alheri, jajantawa da tausayawar da ya yi mana tun farko a kan bala’in da ya faru a garuruwan mu masu yawa, da kuma tallafin da ya ba waɗanda abin ya shafa. 
 
“Mu na aikin fito da wani kasafin kuɗi na musamnan da za mu kai wa Shugaban Ƙasa don ya ga yadda za mu sake gina gidaje, asibitoci da makarantu da ambaliyar ta shafa. 
 
“Mu na kuma yaba wa mai girma Shugaban Ƙasa saboda ayyukan sa na agaza wa jama’a. Akwai su da dama kuma mu na godiya kan yadda Jihar Sokoto ta amfana daga waɗannan shirye-shirye.
 
“Mu na tabbatar maku da cewa al’umma da gwamnatin Jihar Sokoto a shirye mu ke mu haɗa gwiwa da ku a kowane shiri da zai amfani jama’a.”
 
Gwamnan, wanda ya bayyana Jihar Sokoto a matsayin jiha mai tanyon mata, ya yi alƙawarin ƙara azama wajen ƙarfafa wa mata, musamman waɗanda ke zaune a yankunan karkara.
 
Tun da farko, sai da Minista Sadiya Umar Farouq ta jajanta wa gwamnatin jihar a kan bala’in ambaliyar.
 
Ta ce, “Mai Girma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, GCFR, ya damu da ɓarnar da ambaliyar ta jawo kuma ya bada umarni ga Ma’aikar Harkojin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya da ta sa Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta yi azama wajen samar da taimakon da mutanen da abin ya shafa ke buƙata. Ga ni na zo tare da Darakta Janar na NEMA domin mu kawo kayan agaji da aka amince a rarraba don taimakon waɗanda abin ya shafa.”
 
Kayan agajin da aka kai wa jihar sun haɗa da buhun masara 1,502, buhun shinkafa 1,502, buhun wake 1,502, garwar manja 107, garwar man girki 43, katan-katan na kayan haɗin girki guda 202, katan 141 na tumatirin gwangwani da kuma buhu 22 na gishiri. 
 
Sauran sun haɗa da bargo 3,868, katifa 3,868, gidan sauro 3,004, buhun siminti 3,780, bandir ɗin kwanon rufi 3,780, buhun ƙusa 723, fakitin ƙusar kwano 200 da kuma katan 72 na omo.
 
Ministar ta yi la’akari da cewa tun ma kafin a raba waɗannan kayan agajin, Gwamnatin Tarayya ta riga ta tura wasu kayan agajin ga al’ummar Ƙaramar Hukumar Goronyo da ambaliyar ta shafa, ta hanyar NEMA. 
Minista Sadiya Umar Farouq na raba N20,000 a Jihar Sokoto a ƙarƙashin Shirin Bada Lamuni ga Matan Karkara
Ta ce, “Ofishin NEMA da ke Sokoto ya gudanar da binciken gani da ido a ƙananan hukumomin Binji da Silame. An amince a kai masu kayan agaji kafin ƙarshen satin nan kamar haka:
 
i.   buhun shinkafa 455 (kilo 12.5)
ii.   buhun masara 455 (kilo 12.5)
iii.   buhun wake 455 (kilo 25) 
iv.   katan 76 na kayan haɗin girki 76
v.   jarka 46 (lita 20) ta man girki
vi.   katan 38 na tumatirin gwangwani
vii.   bargo 910
viii.  katifa 910
ix.  gidan sauro 910 
x.  buhun siminti 600
xi.  bandir 600 na kwanon rufi
xii.  fakiti 200 na ƙusar kwanon rufi 
xiii.  buhu 67 na ƙusa inci 3
 
Hajiya Sadiya
ta kuma bayyana cewa za a riƙa biyan N5,000 a kowane wata ga gidaje 3,465 na mabuƙata a Jihar Sokoto, yayin da ana shirin rubuta gidaje 29,676 na mabuƙata cikin wannan shirin. 
 
Ta yi kira ga gwamnan da ya taimaka wa jihar domin ta shigar da ƙarin mutane cikin shirye-shiryen bada tallafin da ma’aikatar ta ke gudanarwa.

Loading

Previous Post

Yadda Aisha Buhari ta hasko tasirin ‘yan Kannywood a gwagwarmayar ceton talakawa

Next Post

An kafa kwamitin tantance sha’iran Jihar Kano

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Alhaji Isma'il Na'abba (Afakallah), Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano

An kafa kwamitin tantance sha'iran Jihar Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!