LABARIN rasuwar fitacciyar jarumar Kannywood Hajiya Binta Ola Katsina ya yi matuƙar girgiza ‘yan fim, musamman waɗanda su ka yi magana da ita ‘yan awanni kafin komawar ta ga Allah.
Da sanyin safiyar yau Laraba aka wayi gari da labarin rasuwar tsohuwar ‘yar wasan kwaikwayon kuma uwa. Ta rasu ta na da shekaru 78 a duniya kuma ta rasu ta bar ɗiyar ta Amina, wadda da man ita kaɗai ta haifa a tsawon rayuwar ta ta duniya, tare da jikoki da dama.
Hajiya Binta, wadda kusan kowa ke kira da Mama, ta kai kusan ƙarfe 2 na dare ta na gayyatar jama’a zuwa wurin taron Mauludin Manzon Allah (s.a.w.) da ta saba shiryawa a duk shekara.
Iyalan marigayiyar sun shaida wa Mujallar Fim a Katsina cewa har kusan ƙarfe 2 na dare ana ta hidimar yin abinci wanda za a raba a wajen Mauludin, kuma komai da ita aka yi.
Ɗiyar ta, Amina, ta faɗa wa wakilin mu: “Bayan kammala ayyukan baki ɗaya sai ta kwanta ta ce kan ta ya na yi mata ciwo, kuma ta bada umarni da wasiyyar cewa ko da ba ta tashi ba (wato idan Allah ya yi mata cikawa) kada a fasa wannan taro na Mauludi.”
Amina ta ci gaba da cewa, “Daga nan sai mu ka ce mata in-sha Allahu ma da ita za a yi komi, amma sai ta ce ita kaɗai ta san yadda ta ke ji shi ya sa ta ke faɗin haka. Allah da ikon sa wannan kwanciya da ta yi sai dai gobe kiyama.”
A kan wannan rashin da aka yi, ta ce, “Haƙiƙa mun yi babban rashi na uwa wadda ba ta nuna bambanci tsakanin ɗiyar ta da kuma waɗanda ba ‘ya’yan ta ba. Sai dai mu ce Allah ya jiƙan Mama, ya gafarta mata kurakuran ta, ya sada ta da Annabin Rahama.”
Wasu da marigayiyar ta yi magana da su sun bayyana wa mujallar Fim cewa Hajiya Binta ta kira su ta na sanar da su cewa gobe Laraba (yau kenan) akwai taron Mauludin Manzon Allah (S) wanda ta saba shiryawa a duk shekara.

“Ashe wannan gayyata da aka yi mana, sai ta koma gayyatar jana’izar ta. Mu dai nan da ka gan mu, taron Mauludi mu ka zo, kuma an yi Mauludin kamar yadda ta bada wasiyya, bayan an kammala aka yi mata sutura sannan aka kai ta makwancin ta,” inji wani da aka gayyata.
An yi jana’izar Hajiya Binta Ola Katsina da misalin ƙarfe 10 na safe bayan an kammala taron Mauludi a gidan ta da ke Sabuwar Unguwa cikin birnin Katsina.
Mawaƙa da ‘yan fim da kuma abokan sana’ar ta na wasan kwaikwayon rediyo da talbijin tun shekaru talatin da su ka gabata sun samu halartar wannan jana’iza inda aka rufe ta a maƙabartar Filin Kanada da ke cikin Sabuwar Unguwa.
Wakilin mu da ya halarci jana’izar ya lura da yadda ‘yan fim da mawaƙa da sauran jama’a su ka kaɗu da labarin rasuwar ta.
Mawaƙa da ‘yan fim na Katsina ɗaiɗai ne ba su halarci jana’izar ba, musamman da yake su na da labarin taron Mauludi da marigayiyar ta shirya.
Wasu daga cikin waɗanda su ka halarci jana’izar sun haɗa da Alhaji Surajo Mai-Asharalle, Sunusi Anu, Balarabe Kabir, Usman UNM da darakta Aminu Mannir K-Eza.
Sauran sun haɗa da abokan wasan kwaikwayon ta tun asali da su ka haɗa da Alhaji Sani Mande Dutsin-ma (Nayalli), Mansur Ya’u (Alhaji Baba), Alhaji Bilis, Sarkin Fawa, Kawo Shumo, Kabir Nadaƙila da sauran su.

Ita dai Hajiya Binta Ola, ta shafe kimanin shekaru 30 a harkar fim, domin tun ana yayin diramar talbijin ta fara har aka zo finafinan bidiyo, har kuma yau da ake yin finafinai masu dogon zango. Kuma ta fito a wasannin kwaikwayo na rediyo masu yawa.
A ‘yan shekarun nan ta yi fice a shirye-shiryen rediyo, musamman ma a matsayin Iyan Fegi (yar babar Iro) a shirin rediyo ɗin nan mai suna ‘Shugabanci’ wanda kamfanin Moving Image, Kano, ya ke shiryawa, da kuma matsayin Hajiya Sabuwa a cikin shirin ‘Ga-ta-nan Ga-ta-nan-ku’ na BBC Media Action.
Har ila yau akwai ta a cikin fim ɗin ‘Daɗin Kowa’ na tashar Arewa 24.


Welldone! Allah ya jikana da rahama! Amin!