ƘWARARREN editan finafinai a Kannywood, Rabi’u The King, ya bayyana cewa asarar da ya yi a lokacin tarzomar da masu murnar cin zaɓe su ka yi kwanan nan a Kano ta shafi ba shi kaɗai ba har ma ita kan ta masana’antar Kannywood.
Idan kun tuna, masu tarzomar sun ƙone gidan mawaƙi Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara) da ofishin sa da kuma wasu ofisoshi na ‘yan fim jim kaɗan bayan an bayyana cewa ɗan takarar zama gwamna a jam’iyyar NNPP, Abba Gida-Gida, shi ya lashe zaɓen. Sun kai harin saboda su na ganin su Rarara magoya bayan abokin adawa ne,
Da yake ofishin Abba The King ya na kusa da na Rarara ne, shi ya sa shi ɓarnar ta shafi shi ya shafi situdiyo ɗin sa, inda su ka ƙone shi tare da kwashe duk wani abu da ya ke cikin sa.

A lokacin da mujallar Fim ta tambaye shi yadda labarin ya faru, Rabi’u ya ce, “To ni lokacin da abin ya faru ba na wajen, sai kawai aka kira ni a waya ake sanar da ni masu murnar cin zaɓe sun zo ofishin Rarara. To ni kuma situdiyo na ya na kusa da shi.
“Sai kuma ake sanar da ni ai ‘yan sanda sun kore su, amma daga baya sun dawo su na ta fashe-fashe su na fito da kayan mu waje su na kwashewa su na cinna musu wuta. To sai na ji ba zan iya zama ba, don haka sai kawai na taho. Kuma na zo na samu wajen duk an fito da kayan an saka wa situdiyo ɗin wuta ya na ta ci. Haka kawai na tsaya ina kallo ya na ta cin wuta amma babu yadda zan yi.
Ya ƙara da cewa, “Duk waɗanda su ke kusa da ni su ma abin ya shafe su; da Baban Chinedu da yake sama da Rarara duk an kwashe komai amma nawa situdiyo ne aka ƙone shi ƙurmus, babu wani abu da za a dauka.”
Rabi’u The King ya lissafa irin asarar da ya yi, inda ya ce, “Gaskiya na yi asara sosai, don ka ga akwai kwamfutoci guda huɗu manya, duk an ƙone. Sannan akwai manyan kyamarori guda uku duk sun ƙone, ban da ƙananan kwamfutoci da kyamarori. Sannan kuma akwai finafinai masu dogon zango sama da guda 12 da aka kawo mini aikin su, duk an ƙone su, ban da ma wasu da sai daga baya idan waɗanda su ka ba ni aikin sun yi mini magana na ke tunawa da su.
“Don haka a gaskiya an yi mini asara mai yawan gaske. Kuma ba ni kaɗai ba har ita kan ta masana’antar Kannywood, saboda manyan finafinan da aka ƙone su kuma babu yadda za a yi a same su. Don haka mun yi asara tarin yawa.”



