MAWAƘIN Kannywood, Ado Isa Gwanja, ya samu zuwa ƙasar Amurka domin gabatar da waƙa a gaban masoyan sa da ke zaune a can bayan ya samu gayyatar su, inji wani abokin sa.
Hotuna da bidiyon Gwanja a Washington DC, babban birnin Amurka, sun ɓulla a soshiyal midiya a ranar Litinin. Mawaƙin ya yi tafiyar ne a ranar Juma’a da ta gabata.
Wani makusancin mawaƙin, Abubakar H. Kura, ya shaida wa mujallar Fim cewa an shirya mako ɗaya Gwanja zai yi.

Abubakar ya ƙara da cewa wasu masoyan Gwanja, Hausawa ‘yan Nijeriya da Nijar, mazauna Amurka, su ne su ka gayyace shi domin ya gabatar da waƙoƙin sa a can.
An shirya tafiyar ne ta ƙasar Nijar saboda alaƙar Gwanja da Jakaden Nijar a Amurka wanda ta hanyar sa ya taso daga Nijar zuwa Nijeriya inda ya hau jirgi ya tafi Amurka ɗin.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa Gwanja ya samu tarba daga wasu ‘yan Nijar da ke Washington DC, ciki har da wasu mawaƙa.
Masoyan Gwanja da dama sun taya shi murnar wannan dama da ya samu ta zuwa Amurka a karo na farko, su na cewa wannan wani babban cigaba ne a sana’ar sa ta waƙa.

