• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yadda yaro ɗan shekara 17 ya kashe mawaƙiyar Annabi, Hauwar Aleebaba

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
September 11, 2023
in Labarai
1
Marigayiya Hauwa Shu'aibu (Hauwar Aleebaba)

Marigayiya Hauwa Shu'aibu (Hauwar Aleebaba)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A  DAREN jiya Lahadi, 10 ga Satumba, 2023 Allah ya ɗauki ran mawaƙiya Hauwa Shu’aibu (wadda aka fi sani da Hauwar Aleebaba).

Mujallar Fim ta samu labarin yadda Hauwa ta rasu sakamakon wani mummunan haɗari da ya ritsa da ita. Mujallar ta gano cewa a daren shekaranjiya Asabar, 9 ga Satumba ne mawaƙiyar da yarinyar da ke yi mata amshi su ka je gidan shehun su, wato Sharu Uba, a unguwar Hotoro a cikin garin Kano. 

Bayan sun fito daga gidan, su na bakin titi za su tare abin hawa, sai ƙarar kwana ta zo inda wani yaro ɗan shekara 17 baban sa ya ba shi makullin mota don ya gyara mata waje, shi kuma sai kawai ya ɗauki motar ya tafi yawo da ita. A nan ne ya haɗu da su Hauwa a bakin titi ya buge su ya tura su cikin kwalbati, inda nan take Hauwa ta samu karaya biyu a ƙafafun ta da mummunan rauni a kan ta. 

Hauwar Aleebaba bayan ta yi haɗarin da ya yi sanadiyyar rasuwar ta

Majiya ta shaida wa wakilin mu cewa ita ma ‘yar amshin ta samu rauni a kan ta wanda ya sa har yanzu ba ta san inda ta ke ba.

Tun a lokacin dai aka kai su asibiti amma a daren jiya Allah ya karɓi ran Hauwa. An yi jana’izar ta a gidan su da ke Jakara, Kano, da misalin ƙarfe 9 na safiyar yau Litinin.

Ita dai Hauwar Aleebaba, tsohuwar mawaƙiya ce a Kannywood, wadda tun ana Sabon titin Mandawari ta ke situdiyon ‘Iyan-Tama Multimedia’ inda Aleebaba Yakasai ya ke kiɗan fiyano, kuma a nan ta samu laƙabin ta na ‘Hauwar Aleebaba’. Muryar ta ta fito a finafinan Hausa da dama.

Daga baya ne ta koma ta na yin waƙoƙin yabon Manzon Allah (s.a.w.).

Allah ya rahamshe ta, amin.

Hauwar Aleebaba (a hagu) tare da Maryam A. Baba a lokacin bikin Maryam ɗin

Loading

Previous Post

Rarara ya ɗauki nauyin gyara hanyoyi a karkarar su ta Jihar Katsina

Next Post

Ban ga amfanin MOPPAN ta Kaduna ba, inji sakataren tsare-tsaren ta tare da aje aiki

Related Posts

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
Next Post
Malam Abubakar Hunter

Ban ga amfanin MOPPAN ta Kaduna ba, inji sakataren tsare-tsaren ta tare da aje aiki

Comments 1

  1. Pingback: Yadda Yaro Ɗan Shekara 17 Ya Kashe Mawaƙiyar Annabi, » HausaMini.Com.Ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!