DARAKTA a Kannywood, Aminu S. Bono, ya bayyana wa mujallar Fim dalilin ƙonewar motar sa ƙurmus a daren jiya Juma’a, 9 ga Disamba, 2022.
Malam Aminu ya ce ibtila’in ya faru ne a garin Jos, Jihar Filato, lokacin da ya je can bikin aure daga Kano.
A labarin da ya ba wakilin mu, daraktan ya ce: “A daren jiya Juma’a ne a garin Jos na je bikin wani yaro na. To bayan mun dawo daga wajen dina mu na shirin tafiya wajen ƙwallon ƙafa, duk a cikin shagalin bikin, sai kawai motar ta kama da wuta kuma nan take ta ƙone ƙurmus.”
Ya ci gaba da bayyana irin asarar da ya yi da cewa, “Motar tawa ƙirar Marsidi C180 ƙonewar ta ya taƙaita ni. Duk da dai ba a yi asarar rai ko jin ciwo ba, amma duk wasu muhimman abubuwa nawa da su ka ƙunshi takardun makaranta da na motar da katin zaɓe da na ɗan ƙasa duk su na cikin motar.”
Jama’a da dama su na ta aika wa da fitaccen daraktan da saƙon jaje, cikin su har da Majalisar Ƙoli da babban zauren dattawan masana’antar, wato Kannywood Foundation, waɗanda sun aika da saƙo.
Daraktan hulda da jama’a na majalisar, Malam Kabiru Maikaba, ya tura masa da saƙo inda ya ce: “Na jajanta wa Malam Aminu S. Bono dangane da wannan iftila’i da Allah ya jarabce shi da shi.
“Mu na roƙon Allah SWA ya tsayar a nan. Mu na fatan Allah ya saka maka da mafificin alkhairi. Allah ya mayar maka da sabon arziki, don darajar mafificin halitta, Manzo SAW.”