FITACCEN jarumin Kannywood Ubale Ibrahim (‘Wanke-Wanke’) ya rasu ne a daren jiya ba tare da wani ciwo ko jinya ba, wani ƙanen sa ya faɗa wa mujallar Fim.
Mutuwar ta girgiza ‘yan fim ɗin Hausa, musamman da yake ba a ji labarin ko ya yi rashin lafiya ne ba.
Yau da safe, 1/5/2020, aka yi jana’izar jarumin wanda ya rasu wajen ƙarfe 11 na dare.
An yi taron jana’izar a gidan sa da ke unguwar Rangaza da ke Ƙaramar Hukumar Ungoggo a cikin garin Kano, kuma aka binne shi a maƙabartar Tudun Murtala.
Ɗimbin ‘yan fim da sauran jama’a sun halarta.
Cikin manyan ‘yan fim da su ka halarta akwai aminan marigayin, wato Sani Musa Danja da Yakubu Muhammad, sai kuma Mustapha Nabraska, Abdul Amart, T.Y. Shaban, da Jamilu Ibrahim.
Marigayin, mai kimanin shekaru kusan 50, ya rasu ya bar matar sa ɗaya da ‘ya’ya shida -biyar maza ɗaya mace – da kuma mahaifin sa.
Hamisu Ibrahim, wanda ƙane ne ga Ubale, ya shaida wa mujallar Fim cewa: “To shi rasuwar Ubale mun same ta ne kawai cikin yanayi na bazata, saboda ba gida ɗaya mu ke da shi ba.
“Amma dai kamar yadda abin ya faru, cikin daren jiya, kamar misalin 10:30 su na zune a ƙofar gidan sa su da maƙotan sa, su na hira, sai kawai ya tashi ya je ya saka wayar sa a caji, ya dawo.
“Bayan ya dawo ne sai kawai aka ga ya faɗi. To dai daga faɗuwar nan da ya yi sai Allah ya karɓi ran sa.
“Amma duk da haka an ɗauke shi an kai shi asibitin Nassarawa, amma da su ka auna shi sai su ka ce ai ya daɗe da rasuwa. Daga nan aka dawo gida.”
Mun tambaye shi ko da man ya yi wani rashin lafiya a ‘yan kwanakin nan?
Sai ya ce, “To gaskiya dai a kwana kusa babu wata rashin lafiya da ya yi domin ko a kwana uku baya mun je wata ta’aziyya da shi ta wata ‘yar’uwar mu da ta rasu, kuma ko jiya ma bayan an kai azumi da shi aka yi sallar Isha, har ma an yi Asham da shi.
“Kawai dai mutuwar ta zo masa ne lokaci guda saboda lokacin ya yi. Domin idan cuta mutuwa ce.
“Ubale tun shekarun baya da ya rasu, don kuwa a baya ya sha fama da rashin lafiya har ya kwanta a asibiti tsawon lokaci, amma da ya ke lokaci bai yi ba sai yanzu Allah ya karɓi abin sa ba tare da ya kwanta jinya ba.”
Dangane da yadda su ka ji game da wannan rashi kuwa, Hamisu ya bayyana rashin ɗan’uwan nasa da wani babban giɓi a rayuwar su.
Ya ce, “Gaskiya rayuwar mu mun samu giɓi sosai, domin kuwa shi ne babban ɗa a gidan mu. Don haka ni da ‘yan’uwa na mu na jin wannan rashin sosai.”
Ubale Ibrahim dai jarumi ne da ya daɗe ana damawa da shi a cikin masana’antar finafinai ta Kannywood, kuma ya bayar da gudunmawa sosai wajen fitowa a cikin manyan finafinai tun a shekarun baya.
An fi sanin sa a kamfanin ‘Two-Effects Empire’ na su Yakubu da Sani Danja. Kusan duk wani fim da kamfanin ya shirya, da sa hannun sa a ciki.
Hasali ma dai ana yi masa laƙabi da Ubale Two-Effects.
Biyu daga cikin finafinan kamfanin da ya fito a ciki su ne ‘Daham’ da ‘Buri Uku A Duniya’.
Kusan dukkan ‘yan fim sun yi juyayin mutuwar sa, sun masa addu’a.
Mu na fatan Allah ya jiƙan sa da rahama.
Ana addu’a a gaban kabarin Ubale Wanke-Wanke jim kaɗan bayan an kammala rufe shi