WANI bincike da mujallar Fim ta yi ya gano cewa masu sana’ar tura finafinan Hausa a waya ko komfuta, waɗanda ake kira ‘yan dawunlodin (downloading), su na kashe kasuwar finafinan da ake ɗorawa a manhajar YouTube, amma furodusoshi ba su lura ba.
Tun bayan da kasuwancin finafinan da ake sakin su a faifan sidi ko dibidi ya taɓarɓare, furodusoshi sa dama su ka koma YouTube su na saka finafinan su a ciki.
Manufar saka finafinan a YouTube ita ce don masu kallo su je su kalla, ta yadda kamfanin YouTube zai ba furodusoshin kamasho daga tallar da ya ke sakawa a finafinan.
Bakin yawan ziyartar masu kallon fim bakin tallar da YouTube za su saka, kuma bakin kuɗin da furodusa zai iya samu.

Hakan ya sa furodusoshi su ke yawan tallata finafinan a wajen abokan su da kuma mabiyan su a soshiyal midiya domin a je a kalla.
Yawancin finafinan dai masu dogon zango ne, wato ‘series’, domin su ne za su riƙe zuciyar mai kallo har ya dinga komawa ya na kallo.
Tuni dai haƙar furodusoshin ta fara cimma ruwa saboda mutane sun karɓi wannan tsarin na kallon finafinai masu dogon zango a YouTube.
To sai dai mujallar Fim ta gano cewa inda gizo ke saƙar shi ne rawar da ‘yan dawunlodin ke takawa a wannan tsarin ba za ta haifa wa furodusoshi ɗa mai ido ba.
Shekarar da mu ka yi bankwana da ita, wato 2020, ta zo da wani tsaiko sakamakon zaman gida da aka yi dalilin ɓullar annobar korona, wanda ya sa masu tura finafinai a waya ko komfuta, wato ‘yan dawunlodin, su ka samu ƙarin masu tururuwar zuwa wajen su domin a tura masu irin waɗannan finafinai masu dogon zango a wayar su fiye da irin waɗanda ake shiryawa a da waɗanda ke tsayawa iya kashi na 1 da na 2.
Masu wannan sana’a da dama, waɗanda yawancin su a Kano su ke, sun bayyana wa mujallar cewa a kowane mako mutane na neman finafinai masu dogon zango sama da kala 25, wanda hakan ya ba su damar bugun ƙirji wajen bayyana cewa zuwan “series film” – kamar yadda su ke kiran su – ya farfaɗo masu da kasuwar su.
Mujallar Fim ta gano cewa ashe kuma kura ce da shan bugu, gardi da karɓe kuɗi, domin kuwa abin da ya sa masu kallo su ke kwafar finafinan a waya shi ne maimakon su biya kuɗin data su kalla a YouTube, gwamma idan sati ya zagayo su kai kuɗin da bai fi N30 ba ga ‘yan ‘downloading’ su saka masu a wayar su ko komfutar laptop ko tablet.
Su ‘yan dawunlodin ɗin su kan sauko da finafinan ne daga YouTube ko su karɓa kai-tsaye daga hannun furodusa, su riƙa sayar wa masu kallo.
Maimakon furodusa ya samu ƙarin masu ziyartar tashar sa ta YouTube, inda zai ci riba, sai mutanen su je kasuwa kawai a saka masu fim ɗin a waya, su kalla ba tare da hawa YouTube ɗin ba.
Akwai finafinai masu dogon zango sama da 20 da mutane ke yawan kallo. Kun kasu kashi biyu: waɗanda gidajen talbijin ke shiryawa da waɗanda furodusoshi masu zaman kan su ke shiryawa.
Finafinan da masu kallo su ka fi so a tura masu waɗanda tashar talbijin ta Arewa 24 ke yi su ne: ‘Labari Na’, ‘Kwana Casa’in’, ‘Daɗin Kowa’ da ‘Gidan Badamasi’.
Akwai kuma finafinai kamar 10 na furodusoshi masu zaman kan su waɗanda aka fi tura wa mutane a waya.
Binciken mujallar Fim ya nuna cewa fim mai dogon zango na furodusa mai zaman kan sa da mutane su ka fi so a cikin 2020 shi ne ‘Izzar So’.
Fim ɗin, wanda darakta Nura Mustapha Waye ya rubuta labarin shi kuma ya ke bada umarni, an shirya shi ne a kan yadda ‘ya’yan masu kuɗi da su ke da madafun iko su ke wulaƙanta waɗanda na ƙasa da su ba tare da sanin abin da ka iya zuwa ya dawo ba.
Lawan Ahmad ne jarumin fim ɗin sannan shi ne ya ɗauki nauyin shirya shi a ƙarƙashin kamfanin sa na Bakori Entertainment.
Fim mai suna ‘A Duniya’ kuma ya zo da wani salo wanda al’umma su ka yi na’am da shi, musamman yadda ya ke haska rayuwar wasu daga cikin matasa da ake amfani da su wajan cimma wani burin siyasa da kuma yadda wasu malamai su ke cin karen su ba babbaka.
Wanda ya rubuta labarin kuma ya zama furodusan sa shi ne jarumin fim ɗin, Tijjani Asase.
Fim ɗin ya samu karɓuwa a wajen masu kallo saboda yadda ake amfani da wasu kalamai masu sarƙaƙiya a cikin sa.
Na uku shi ne ‘Sirrin Kyau’ wanda shi ma ya sha sharafin sa wurin ‘yan kallo a ƙarshen shekarar.
Fim ɗin ya bai wa matasa sabuwar fuska domin su baje kolin basirar da Allah ya ba su, kuma aka yi sa’a jama’a su ka karɓe shi.
Mustapha Aphala shi ne wanda ya bada umarni a wannan fim, sannan Malam Hudu Mazaje ne ya shirya shi.
Shi ma ‘Bugun Zuciyar Masoya’ ya ja hankalin masoya musamman yadda ya ke nuno rayuwar wasu masoya biyu, kuma bayyanar jarumi Lawal Ahmad a cikin sa ya sa ya ƙara karɓuwa a wurin jama’a.
Kamfanin Alrahuz Film Production da ke Kano ne ya ke shirya shi.
‘Burin Rai’ kuma fim ne da Adam A. Zango ya fito a cikin sa a matsayin jarumi, tare da Isah Adam (Feros Khan).
Kamfanin White House Family, mallakar Adam A. Zango, shi ne ya ke shirya shi.

‘Ruhin Tausayi’ fim ne wanda mutane su ke yaba wa aikin sa sakamakon yadda masoya su ke baje kolin su a ciki.
‘Ruhin Miji Na’ shi ma ya na ɗaya daga cikin finafinan da aka fi tambaya a wajen ‘yan dawunlodin a shekarar ta 2020.
Fim ɗin ‘Macen Sirri’, wanda ya fara fitowa a ƙarshen shekarar, ya samu karɓuwa saboda yadda ya zo da abubuwa masu rikitarwa.
Kamfanin SirrinSu Media na Maje El-Hajeej Hotoro ne ya ke ɗaukar nauyin shirya shi.
Akwai kuma ‘Rayuwar Amina’ wanda ya shiga cikin jerin finafinan da ke ɗaukar hankali, har ya kasance ake neman sa ruwa a jallo a kowanne sati.
Shi ma ‘Zaman Aure’ fim ne da ya yi nuni a kan zamantakewar aure a ƙasar Hausa. Matan aure na tururuwar zuwa wajen ‘yan dawunlodin domin a tura masu shi.
Su dai ‘yan dawunlodin sun zama kamar hanta da jini a Kannywood. An sha famar yadda za a kawar da su tun a zamanin finafinan sidi da dibidi, amma abin ya ci tura.

Yanzu da harkar ta rikiɗe zuwa YouTube, su ma sun bi zamani, ana tafiyar kaska da sa tare da su.
A yanzu dai kusan babu mai shirya fim wanda ya damu da su.
Ko furodusoshi za su ɗauki wani mataki a kan su nan gaba, ganin yadda su ka yi ƙarfi a kasuwa, Allah kaɗai ya sani.