AIKIN sabunta rajistar ‘yan fim da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta bijiro da shi bayan dawowar Isma’ila Na’abba Afakallahu kan kujerar shugabancin ta a karo na biyu ya tayar da ƙura a masana’antar fim.
Rabon da a samu irin wannan tada ƙurar tun lokacin da Malam Abubakar Rabo ya shugabanci hukumar.
Babban abin da ya jawo wannan tashin ƙurar shi ne baƙar adawar siyasa da ta shiga cikin ‘yan fim a zaɓen gwamna da ya gabata, wanda ya sa kowa ya ja daga a nasa ɓangaren.
Abu na biyu kuma shi ne mugun talauci da ke cin masu harkar, domin ana wani irin zama ne na kai-kuka-ni-tagumi, sai kuma ga sabon tsari ya zo cewar duk wanda ke cikin harkar dole ne ya je ya yi rajista da hukumar, idan kuma ya na da ita tun lokacin Rabo, to dole ya sabunta ta.
A tsarin rijistar wanda mujallar Fim ta gani, an ƙayyade cewa duk furodusa sai ya sayi fom na N5,000, kuma idan ba shi da rijista da ƙungiyar furodusoshi, to sai ya je ya yi rijista, ita ma a kan N5,000.
Kowane darakta zai yi rijista a kan N5,000, sannan zai yi rijista da ƙungiyar su a kan N3,000.
Kuɗin rajistar jarumi a hukumar N3,000, a ƙungiya kuma N3,000, sai fom ɗin ƙungiya 2,000.
Marubucin labarin fim zai yi rijista ta N2,000, sai fom ɗin ƙungiya N1,000, yayin da edita zai biya N3,000, sai fom na ƙungiya N2,000.
Jin irin waɗannan kuɗaɗen da za a biya ya sa aka yi ta hayaniya da tayar da jijiyar wuya, don haka a farkon shirin aka samu turjiya da bore mai zafi a cikin ‘yan fim.
Hakan ya mayar da lamarin wani filin daga, kowa ya fito da makaman sa, aka yi ta gwabza yaƙin cacar baka tsakanin Afakallahu da ‘yan fim ɗin da ba su yarda da tsarin ba.
Ana cikin haka ne har aka zo lokacin fara yin rijistar a tsakiyar watan Agusta, kuma aka kammala a ranar 20 ga Satumba, 2019.
A tsawon lokacin da aka shafe ana aikin, an yi wa ‘yan fim da dama rijista tare da tantance su.
Duk da haka, da mujallar Fim ta dubi yawan masu gudanar da aiki a Kannywood, ta ga cewa ko kashi 2 cikin ɗari na ‘yan fim ɗin ba su je sun yi rijistar ba.
A binciken da wakilin mu ya yi a ranar ƙarshe ta rijistar, ya gano cewar cikin marubuta labarin fim da ake da su a masana’antar, duka mutum 40 ne su ka yi rijista.
Daraktoci kuwa an samu 76 da su ka yi, sai kuma editoci an samu 100 da kaɗan da su ka yi. Su ma furodusoshi guda 77 ne su ka yi rijistar.
Jarumai kuwa, waɗanda su nesu ka fi kowa da yawa, kuma kullum ƙara shigowa su ke, an samu adadin 600 da su ka yi rijista.
Ba mu samu cikakken bayani ba a kan mawaƙa da makaɗa.
Mujallar Fim ta tambayi shugaban ƙungiyar jarumai kuma memba a kwamitin tantance ‘yan fim da yi masu rijista, wato Alhasan Kwalle, yadda su ke gudanar da tsarin, sai ya ce, “Shi wannan tsarin abu ne da gwamnati ta bijiro da shi, kuma mu a matsayin mu na masu bin doka dole ne mu karvi abin yadda ya zo. Kuma a tsarin qungiyar mu akwai wannan dokar, don haka mu taimaka mana aka yi. Wannan ta sa mu ka karɓi abin yanzu. Dole ne ‘yan fim su bi doka.
“Mu a matsayin mu na shugabannin ƙungiya, duk wanda bai bi wannan tsarin ba, to ba ɗan ƙungiyar mu ba ne, sai dai ya je ya yi abu a karan kan sa.”
Shi ma Aleebaba Yakasai, wanda ya ke jagorantar mawaƙa da makaɗa, ya ce, “Dole ne masu waƙa da masu kiɗa su zo su bi doka; idan ba su yi haka ba to ba su da ikon gudanar da sana’ar su a Kano. Ko da sun yi a wani garin, to ba za su kawo shi Kano ba.”
Shugaban hukumar, Afakallahu, ya shaida wa Fim cewa, “Wannan tsarin doka ce ta samar da shi tun (shekarar) 2000, don haka ba ni na kawo shi ba, kuma duk wanda ya ke ganin ya fi ƙarfin doka, to kada ya yi rijistar kuma ya zo ya yi aiki a masana’antar ya gani!”
Da mu ka tambaye shi ko ba ya ganin sati biyu da aka ware dom yin rijistar bai yi kaɗan ba kuwa, sai ya ce, “Duk mutumin da ya ke kishin sana’ar sa aka ce ya zo ya yi rijista, kuma aka ba shi wannan lokacin, duk inda ya ke ai zai samu damar ya zo ya yi.
“Wanda duk ka ga bai yi ba, to da man ba shi da niyya ne. Don haka da zarar an gama an rufe kenan, sai bayan shekara biyu za a buɗe.
“Waɗanda aka yi wa sun isa, da man ba son yawan mu ke ba, kaɗan mai amfani sun fi don mu na so mu tsarkake harkar ne.”
A wata ziyara ta ba-zata da ya kai lokacin ana gudanar da aikin rijistar, Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya jinjina wa Afakallahu a kan yadda ya ke gudanar da aikin sa, kuma ya yi alƙawarin ba shi dukkan goyon bayan da ya ke buƙata don kawo gyara a harkar fim.
Haka kuma ya raba katin shaida ga wasu daga cikin ‘yan fim da su ka haɗa da Alhassan Kwalle, Saratu Giɗaɗo, Shehu Hassan Kano, Ruƙayya Dawayya da Hauwa Edita.
To amma da alama an bar baya da ƙura. Har aka gama aikin tantancewar akwai manyan jaruman da ba su je sun yi rijistar ba.
Hakan ba a bin mamaki ba ne, ganin yadda tun farko su ka nuna adawar su ga tsarin.
Cikin waɗanda su ka nuna adawar su, kuma su ka ƙi zuwa rijistar akwai Adam A. Zango, wanda kwanan baya ya shelanta wa duniya ficewar sa daga cikin Kannywood, sai mai bi masa, wato Mustapha Nabraska, da su Aminu Saira, Falalu Ɗorayi, Baban Chinedu, Sani Danja, Yakubu Muhammad, Aminu Ala, Naziru M. Ahmad da Misbahu M. Ahmad.
A ɓangaren marubuta kuma akwai Fauziyya D. Sulaiman da Nazir Adam Salih.
A ɓangaren mata kuwa, kusan duk jaruman da ke tashe sun je sun yi rijistar, in ban da A’isha Tsamiya wadda kuma ba ta bada wani uzuri ba.
Amma dai Nafisa Abdullahi, Hadiza Gabon, Fati Washa da mawaƙi Ali Jita duk sun yi waya sun sanar da cewa ba sa ƙasar, amma da zarar sun dawo za su je su yi, don haka a hukumance an ɗaga masu ƙafa.
Wani abu da ya zo da ba-zata a wajen tantancewar shi ne zuwan Tijjani Gandu (mai waƙar “Abba Gida-Gida”) tare da Sadiq Zazzaɓi wanda har ɗaure shi hukumar ta taɓa yi, sai kuma Abba El-Mustapha waɗanda dukkan su ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP ne da wasu su ke ƙin zuwa saboda su ba ‘yan wajen gwamnati ba ne.
Lokacin da Tijjani ya zo, an masa tambayar dalilin sa na zuwa, shi kuma ya kada baki ya ce, “Harkar sana’a daban, kuma siyasa daban.”
Wani abu da wakilin mujallar Fim ya lura da shi a wajen tantancewar shi ne akwai wasu mata da su ka riƙa zuwa ana yi musu masu rijista, waɗanda ka na ganin su ka san masu zaman kan su ne, wasu ma daga Sabon Gari su ka zo saboda ɗaurin gindin da su ke da shi a wajen wasu furodusoshin don a yi masu rijista.
To yanzu dai an riga an gama yin rijista, kuma in dai ba waɗanda su ka bayar da uzuri aka ɗaga masu ƙafa ba, ba za a ƙara yi wa kowa ba.
Rahoton da mu ka samu daga Hukumar Tace Finafinai ya nuna cewa nan gaba kaɗan za a fara yin rangadin wajen da ake yin duk wani aiki da ya shafi fim, kuma duk wanda aka kama ya na aiki ba tare da rijista ba, to za a ɗauki matakin hukunta shi.
Hakan ya sa ake tambayar makomar jaruman da su ka ƙi yin rijista. Shin za su canza sana’a ne ko kuma wata jihar za su koma da yin sana’ar?