‘YAN sanda a Kano sun kama wani matashi mai suna Imam Abdullahi Indabawa bisa zargin yaɗa kalaman ɓata suna tare da neman wasu kuɗaɗe daga hannun Abdul’aziz Shu’aibu, wanda aka fi sani da Malam Ali na cikin shirin ‘Kwana Casa’in’.
Ana tuhumar Indabawa da yi masa barazanar ci gaba da ɓata masa suna idan har bai biya shi wasu kuɗaɗe ba.
Hakan na ƙunshe cikin wani jawabi da kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya yi a yammacin shekaranjiya Talata, a hedikawatar ‘yan sanda ta jihar da ke Bompai, Kano.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa wanda ake zargin ya amsa laifin sa a gaban lauyan sa, amma ya roƙi a yi masa afuwa bisa abubuwan da ya aikata na kuskure.
Ya yi nuni da cewa shi mai wa’azi ne wanda ya samu zamiya yayin wa’azin sa, har ta kai shi ga wallafa rubutun da ya taɓa mutunci da ƙima ta jarumin na Kannywood.
A nasa ɓangaren, mai ƙarar, wato Abdulaziz Shu’aibu, ya koka matuƙa da yadda matashin ya cutar da shi da rubutun da ya wallafa.
Ya ƙara da cewa Indabawa ya nemi ya ba shi kuɗi don ya dakatar da yaɗuwar wannan rubutu na cin mutunci da ya ke yi masa, tare da yi masa barazanar ci gaba da yaɗa wasu rubuce-rubucen a wasu kafafen muddin bai ba shi kuɗi ba.
Tuni dai ‘yan sanda sun kammala bincike kuma za su miƙa wanda ake tuhuma zuwa kotu.
Shi dai Imam Aliyu Indabawa, shi ne wanda tsohon shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Arewa (AFMAN), Alhaji Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama, ya taɓa kaiwa kotu kan wani rubutu da ya yi a Facebook a kan ‘yan fim, ya na mai iƙirarin cewa su na ɓata tarbiyyar mutane, don haka bai kamata ‘yan siyasa su yi masu kyautar alheri ba.
Mujallar Fim ta labarta maku a farkon Satumba 2022 cewa sakamakon rubutun nasa, Iyan-Tama, wanda fitaccen jarumi ne kuma mai shirya finafinai, ya shigar da ƙara a Babbar Kotun Jihar Kano da ke garin Kano a kan zargin ya ɓata wa ‘yan fim suna.