• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

‘Yan siyasa ne ke tafka maguɗin zaɓe ba hukumar zaɓe ba – INEC

by DAGA WAKILIN MU
December 28, 2022
in Nijeriya
0
Onyeka Pauline Ugochi

Onyeka Pauline Ugochi

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi kira ga kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyi cewa su wayar wa jama’a kai don su fita su karɓi katin shaidar rajista, ana saura kwanaki 60 a yi zaɓen shugaban ƙasa.

Ta kuma jaddada cewa ba ta yin katsalandan wajen shiga harƙallar murɗe zaɓen kowane ɗan takara ko wata jam’iyya.

Da ta ke jawabi yayin ganawa da manema labarai da ƙungiyoyin kare haƙƙi, Kwamishanar INEC ta Tarayya da ke Jihar Ebonyi, Onyeka Ugochi, ta bayyana cewa ‘yan siyasa ne ke shirya maguɗin zaɓe ba hukumar zaɓe ba.

Ugochi ta ce, “A mma da ya ke a wannan zaɓe mai zuwa INEC ta fito da tsauraran matakan hana maguɗin zaɓe kwata-kwata, musamman ta hanyar amfani da na’urar tantance katin ɗan takara, wato BVAS, da sauran matakai, babu yadda za a yi ‘yan siyasa su ci kasuwar maguɗin zaɓe.”

Kwamishinar ta yi kira ga kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin kare haƙƙi su tashi tsaye sosai wajen taya INEC tabbatar da ganin cewa ‘yan siyasa ba su samu wata kafar yin maguɗi ba, komai ƙanƙantar ta.

Ta ce: “Za mu yi dukkan abin da doka ta tanadar da abin da ya wajaba domin mu kauce wa masu so mu haɗa baki da su. Saboda hakan ba zai yiwu mu ba da kai borin ‘yan siyasa ya hau ba.

“Kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin kare haƙƙi ku tashi tsaye a matsayin ku na masu ruwa da tsaki a harkar zaɓe, ku taya INEC tabbatar da ganin an gudanar da sahihin zaɓe a ƙasar nan. Ku taimaka wajen tabbatar da cewa mun yi abin da doka ta wajibta mana mu yi. Kuma ku taimaka wajen hana masu maguɗi su aikata maguɗi.”

Ta sake jan kunne da gargaɗin cewa masu ƙoƙarin sayen ƙuri’u su sani duk wanda aka kama, to zai yi zaman gidan kurkuku na shekara ɗaya.

Kwana 60 kenan kafin a gudanar da zaɓe, amma tuni har INEC ta jibge jami’an tsaro da su ka haɗa da sojoji, ‘yan sanda, SSS da NSCDC a dukkan ofisoshin hukumar a yankunan da ake ganin akwai barazanar tsaro.

Idan ba a manta ba, a cikin wata biyu da su ka gabata, an banka wa ofisoshin INEC har bakwai wuta a wasu jihohi na Kudu-maso-yamma da Kudu-maso-gabas.

Loading

Tags: 'yan siyasaBVASINECmaguɗin zaɓeOnyeka Pauline UgochitsaroZaɓen 2023
Previous Post

Sukar da aka riƙa yi wa ‘yan zaman shahada ce aka kwaso aka yaɓa wa ‘yan Kannywood – Zulai Bebeji

Next Post

Bikin Yusuf Saseen da Amina ya ƙayatar, har Rarara ya ba amarya kyautar N400,000

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Amarya da ango tare da Hadiza Kabara (a hagu) da Hadizan Saima a wajen dina a Kano

Bikin Yusuf Saseen da Amina ya ƙayatar, har Rarara ya ba amarya kyautar N400,000

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!