An yi kira ga ‘yan fim da su haɗe kan su domin su samo hanyoyin da za su ciyar da masana’antar gaba ta yadda za su amfana da damammakin da ake samu a cikin harkar fim ta duniya a yanzu da ake tafiya da ci gaban zamani.
Wannan kira ya fito ne daga bakin Farfesa Abdallah Uba Adamu a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron rantsar da shuganin Ƙungiyar Daraktoci ta PROFDA da aka yi a ranar Lahadi 24 ga Nuwamba a Tahir Guest Palace dake Kano.
Farfesa Abdallah Uba Adamu ya ce “Babu wani ci gaban da za a samu in dai ba a haɗa kai ba. Kuma shi ne abin da ya cutar da harkar fim ɗin Hausa tun da aka fara yin ta. Kowa yana ganin sai shi, idan ba shi ba kowa ma ya rasa. Sai kuma Ninanci wato ni kaɗai na iya. Darakta yana ganin shi ne ya iya, Furodusa yana ganin shi ne ya iya, Jarumi yana ganin shi ne ya iya, don haka Ninanci ya sa harkar fim ɗin kullum take komawa baya, ba don ta mutu ba.”
Ya ci gaba da cewa “Duk yadda kake ganin ka iya ina iyawar taka take da a yanzu an daina yayin ka, saboda an samu ci gaban da ba irin aikin ka ake buƙata ba, kai kuma ka tsaya ninanci. Ina tabbatar muku da cewa duk masu tunƙahon sun iya kuma sai da su za a yi, babu wanda yake da ƙarfin mabiyan da suka kai na Murja Ibrahim Kunya. Kuma tun da aka kafa masana’antar fim ba a taɓa samun wanda ya yi sunan Murja Ibrahim Kunya ba. Ita a wanne fim ta fito?
“Saboda a yanzu harkar ta koma onlayin kai kuma ka ƙi tafiya da zamani ka na kallon ka fi kowa iyawa. Kana nan gefe yaron da yake ƙauye da wayar dubu talatin ya fi ka suna a duniya, saboda kullum yana saka abubuwan da mutane suke kallon sa. Amma ku da kuke da labarai masu inganci da za a tsara shi na minti biyu zuwa uku a fahimtar da mutane kuma saƙon ya isa kun kasa yin amfani da damar da kuke da ita kun tsaya kuna nuna kun fi kowa iyawa. Kuma duk lokacin da aka nemi a gyara muku sai ku ce ana yi muku hassada.
Ni an sha cewa ba ɗan fim bane. To ni ɗan fim ne ina yin fim amma ba irin naku ba, fim nake yi wanda zan amfana da shi, masu kallon sa a duniya su amfana da shi, don haka ni ɗan fim ne babu wanda ya isa ya yi mini gorin fim.”
Ya ƙara da cewa “Har yanzu saboda koma baya an takure harkar fim ana kiran ta da finafinan Kannywood, ni kuma ban yarda da hakan ba, domin tun farkon harkar fim ana cewa finafinan Hausa, daga baya aka samar da Kannywood, wannan kuma takure harkar fim ɗin Hausa ne. Yanzu idan ka ce finafinan Kannywood, ka tsayar da harkar fim iya Kano. To amma ana yin fim a Kaduna, Katsina, Jos. Ana yi a Ghana, Nijar. To su kuma ya za a kira su? Don haka finafinan Hausa shi ne abin da ya kamata a kira sunan ba Kannywood ba.”
Ya ci gaba da cewa “Haɗa kai da samar da daidaito da kuma neman ilimin harkar shi ne zai kawo ci gaba da kuma arziki a cikin harkar finafinan Hausa, domin duk duniya babu inda mutum ɗaya yake yin fim sai mu, shi ya sa harkar fim ɗin kullum ba ta ci gaba. Don haka a yanzu lokaci ya yi da za mu tabbatar da mafarkin marigayi Abdu Haro Mashi na samar da ingantaccen haɗin kai a tsakanin ƙungiyoyin da suke cikin masana’antar finafinan Hausa,” inji Farfesa Abdallah Uba Adamu.