• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yanzu waƙa ce ke riƙe da Kannywood, ba fim ba – Darakta Aminu S. Bono

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
September 22, 2022
in Labarai
1
Aminu S. Bono

Aminu S. Bono

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

AN bayyana cewa yawan waƙoƙi da ‘yan fim su ke yi a yanzu su ne su ka kasance abin da masana’antar Kannywood ta ke da shi a matsayin abin yi tun bayan mutuwar kasuwancin sidi da ake bugawa a lokacin baya ana kaiwa kasuwa.

Darakta a masana’antar, Malam Aminu S. Bono, shi ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da mujallar Fim ta yi da shi kan yanayin harkar fim a yau.

Daraktan ya ba mu ƙwarya-ƙwaryan nazarin da ya yi wa harkar fim, ya ce, “A can baya kowa ya sani kasuwar kaset ce ta riƙe masana’antar, har kuma aka dawo  sidi da dibidi su ka zama su ne mu ke sayarwa. Da haka masana’antar Kannywood ta bunƙasa, aka samu arziƙi mai ɗimbin yawa a cikin harkar.

“To, daga baya kuma sai harkar sidi da dibidi ta mutu, mutane su ka karye, kowa ya riƙa ji a jikin sa.

“Ana haka, a daidai wannan lokacin sai kuma jama’a su ka yi ta shigowa cikin masana’antar duk da cewa babu fim ɗin, don haka sai kuma aka juya da yin waƙa, wadda ita kuma waƙar sai ya zama ana yin ta ne ba tare da an samar da kasuwar da za a kai ta a sayar ba. Amma dai duk da hakan sai ya zama matasa, musamman waɗanda su ka shigo harkar a lokacin da dan kuɗin su, sai su ka riƙa yin waƙoƙi, har kuma tunanin saka waƙar a ‘YouTube channels’ ya zo, kowa sai ya yi waƙa ya ɗora a ‘YouTube channel’ ko Facebook ko Instagram don kawai duniya ta san shi a matsayin jarumi, amma dai ba fim ya yi ba.

“Wannan ta sa a yanzu akwai jarumai da dama da su ka yi suna a wannan masana’antar, amma ba fim ne ya saka su ka yi suna ba, kuma kowa ya san su.”

S. Bono ya ci gaba da cewa: “Babbar matsalar da ita wannan harkar waƙar ta ke da ita shi ne ba harka ce da za ka zuba kuɗin ka kuma ka ci riba ba. Ita sai dai ka nemi suna, don haka idan ma ka zuba kuɗin ka yi waƙar, to sai dai su waɗanda su ka hau kan waƙar su yi suna, a riƙa gayyatar su wajen taro.

“Wannan ce ta sa su jaruman su ka riƙa ɗaukar nauyin waƙar su; sai su samo ‘yanmata da su ma su ka zo da son su yi fim kuma ba su samu ba, sai kawai a ƙare da waƙar.

“Hakan ya sa masana’antar Kannywood ta dogara da waƙoƙin, sai ya zama waƙar ce ta ke riƙe da masana’antar, in ban da a ɗan lokacin nan da aka fara yin finafinai masu dogon zango, amma ina tabbatar maka da cewa har yanzu waƙa ce ta ke riƙe da masana’antar Kannywood.”

Daraktan ya yi kira ga mawaƙan Kannywood da su riƙa kiyaye lafazi da kuma shigar da su ke yi a cikin waƙoƙin da su ke yi don gudun ɓata wa masana’antar Kannywood suna.

Loading

Tags: Aminu S. Bonodaraktafim mai dogon zangoFinafinaimawaƙasoshiyal midiyawaƙawaƙoƙiYouTube channel
Previous Post

Furodusa Maishadda zai buɗe katafaren wurin sayar da tufafi a Kano

Next Post

Cewar jarumar Kannywood Ladidi Fagge: Ban san ana yaɗa mugun labari game da ni a soshiyal midiya ba

Related Posts

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry
Labarai

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry

June 15, 2025
Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
Next Post
Hajiya Ladidi Fagge

Cewar jarumar Kannywood Ladidi Fagge: Ban san ana yaɗa mugun labari game da ni a soshiyal midiya ba

Comments 1

  1. Pingback: Yanzu waƙa ce ke riƙe da Kannywood, ba fim ba – Darakta Aminu S. Bono - LastNg

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!