• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yaushe Sarkin Rano ya zama Sarkin Kano?

by RABI'U NA'AUWA
August 21, 2021
in Al'adu
9
Mai Martaba Sarkin Rano, Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa

Mai Martaba Sarkin Rano, Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

KOWACE masarauta ta na da wasu keɓantattun kayan tarihi na al’ada waɗanda su ke manne da kujerar sarautar masarautar, wato babu wanda zai iya amfani da su ko iko a kan su sai wanda ya zama jigon wannan masarauta, wato wanda Allah ya naɗa a matsayin Sarki. Waɗannan kayan sarauta su ne ake kira da Alar Sarauta. 

Su waɗannan kaya, masarauta ta na samar da su ne ta hanyar wasu tsofaffin sarakuna da su ka yi shuhura a wannan masarauta, ko su ka kafa masarautar. 

Idan sarkin da ya kafa masarauta ya na da wani keɓantaccen abu da ya ke amfani da shi, misali mashi ko takobi ko wata wuƙa ko takalmi ko ƙaho, ko kuma wani abu da ake kaɗa masa kamar tambari ko kakaki, ko wani kirari wanda shi kaɗai ake yi wa, ko kuma wani nau’in kayan kiɗa wanda shi kaɗai ake kaɗa wa, kuma bayan rasuwar sa wanda ya gaje shi shi ma ya ci gaba da amfani da shi. 

Sarkin da ya yi shuhura a masarauta in akwai wani abu da ya yi shuhura a kan sa ko ake alaƙanta shi da shi, to ire-iren waɗannan abubuwa su ne masarauta ta ke taskancewa ta haɗa su da kujerar sarauta, sai ya zamto duk sarkin da ya gaji sarauta to shi zai gaji waɗannan kaya, idan abin sakawa ne, shi ne zai riƙa saka shi, haka idan abin kiɗa ne ko na busa, shi kaɗai za a kaɗa wa ko busa wa. Duk ƙasaitar hakimi a wannan masarauta bai isa ya yi amfani da wannan abin da ya ke cikin ala ta wannan masarauta ba, sai dai in Allah ya yi masa Sarki.

Haka kuma Sarkin da aka tuɓe, shi ma abin da ake fara ƙarba daga hannun sa su ne waɗannan kaya na ala. 

A taiƙaice dai, su ne su ke tabbatar da sarauta, su ne cikar sarautar kowane sarki. Wannan ya sa a kowace masarauta za ka samu su na da tasu alar. Misali, a Masarautar Daura kayan da su ke nuna kai ne Sarkin Daura su ne: Wuƙa da Takobin Bayajida da Siradan Doki guda biyu, ɗaya ya na da wuƙa mai kube da ƙaho a jikin sa na azurfa, shi ne wanda Bayajida ya zo da shi ƙasar Hausa. Sai likkafa ta tagulla da sarƙa,sai kayan sulke, da zobban azurfa guda biyu, babba da ƙarami, da carbi, da tambura guda biyu na Magajin Turu da kuntukuru, sai kuma wasu guda uku waɗanda ake kiran babban su da Gamariga.

Waɗannan su ne kayan ala na masarautar Daura, saboda haka duk wanda ya ke Sarkin Daura shi kaɗai ne zai iya riƙe wuƙa ko rataya takobin Bayajida. Duk ƙasaitar hakimi ba zai riƙe su ba, sai dai Sarkin da ya ke sarauta. 

Haka abin ya ke a Masarautar Kano. Akwai waɗannan kayayyakin ala guda bakwai a Masarautar Kano waɗanda dole sai wanda ya gaji Gidan Rumfa ne kawai zai iya amfani da su:

1. Tagwayen Masu:Tagwayen Masu sun samo asali ne tun a zamanin wasu sarakuna ‘yan biyu, Nawata da Gawata, ɗiya ga Sarkin Kano na uku a jerin sarakuna Haɓe, wato Sarki Gajimasu. Waɗannan tagwayen sarakuna sun yi mulki a Kano a lokaci ɗaya duk da cewa ɗayan su ya mutu ya bar ɗaya. Ɗaya ya yi wata bakwai ya rasu, sai ɗayan ya ci gaba da mulki, shi ma ya ƙara shekara ɗaya da wata biyar ya rasu. Gaba ɗaya dai tsawon shekarabiyu su ka yi su na mulki a Kano. 

Waɗannan sarakuna kowane cikin su ya na da mashi, wannan ya sa bayan rasuwar ɗayan sai ɗan’uwan sa ya haɗe waɗannan masuna guri ɗaya, shi ne su ka zamto Tagwayen Masu,sannan aka keɓe su ga Sarkin Kano, wato sun zama cikin abin da ake kira ala.

2. Takalmin Gashin Jimina: Takalmi ne da ake yi masa ado a saman sa da gashin jimina, kuma Sarkin Kano Muhammadu Rumfa, sarkina 20 a jerin sarakunan Haɓe, shi ne ya fara amfani da wannan takalmin. Shuhurar Rumfa ta kai matuƙa. Ana iya cewa ba a yi sarki a Kano kamar Rumfa ba. Shi ne ya gina gidan sarautar Kano na yanzu da wasu abubuwa da yawa na al’ada da addini da kuma cigaba. 

Saboda haka daga kan Rumfa sarakunan Haɓe na Kano su ka gaji Takalmin Gashin Jimina, kuma shi ma sai ya zamto an taskance shi ya zama cikin kayan ala na Sarautar Kano. 

Bugu da ƙari, a lokacin da Dabo ya zama Sarkin Kano, ya rubuta wa Sarkin Musulmi Bello cewa ya na son ya dawo da kayayyakin Hausawa na sarauta, shi kuma ya amince masa.Takalmin Gashin Jimina shi ya fara sakawa a cikin kayayyakin sarauta da Hausawa su ka bari.

3. Kwari da Bakan Dabo:Shi ma wannan Ibrahim Dabo ne ya fara amfani da shi, kuma Sarki ya na fita da shi a matsayin sanda ya riƙa dogara shi musamman in za shi wani abu da ya shafi addini, kamar Sallar Idi, Sallar Juma’a da makamantan su. 

Shi ma wannan kwari da baka bayan rasuwar Sarkin Kano Malam Dabo ya shiga cikin ala ta sarautar Kano, saboda haka babu wani Sarki da zai rataya kuma ya dogara su face Sarkin Kano wanda ya ke kan gado.

4. Wuƙar Yanka: Ita kuma ta samo asali ne a lokacin mulkin Fulani a Kano. Sarkin Kano na farko a jerin Fulani, Sulaimanu, a lokacin sa an ce wasu daga cikin Fulani sun yi masa bore, saboda wasu na ganin ya yi ƙanƙanta da zama Sarki, saboda a lokacin bai fi shekara 30 ba, amma saboda ilmin sa Ɗanfodiyo ya amince da naɗin sa. Wannan ya sa ba duka Fulanin su ka bi shi ba.

Da ya ga haka sai ya rubuta takarda zuwa gaShehu Usman Ɗanfodiyo ta neman ɗauki. Sai Ɗanfodiyo ya ba shi wuƙar yanka da takobi a kan duk wanda ya bijire masa ya yanka shi. 

Wannan ya sa tun daga lokacin Sarkin Kano Sulaimanu Wuƙar Yanka ta shiga cikin ala. Ko da yake akwai tababar cewa har da ita kan ta takobin ta na cikin kayan ala na sarauta ta Kano.

Waɗannan kayayyaki su ne waɗanda Sarki ne kaɗai zai yi amfani da su. Akwai kuma sauran gudu uku da su kuma sarki kaɗai ake yi wa amfani da su. 
Waɗannan abubuwa ana samun su a sauran masarautu kuma su na iya shan bamban a yanayin ko muhallin da ake amfani da su:

Mai Martaba Sarkin Rano, Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa, sanye da Takalmin Gashin Jimina

1. Kakaki: Kakaki shi ma ya na cikin ala ta Kano kuma shi ma Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ne ya fara amfani da shi. saboda haka shi ma sai ya kasance Sarki ne kawai ake busa wa kakaki a Kano, saboda sun saka shi cikin jerin abubuwan da su ka keɓanta da Sarki.

2. Figini: Shi ma wani kalar abin fifita ne da dogarawa su ke yi wa sarki fifita da shi. Su ma waɗannan dogarai ana kiran su Figini. 

Ana yin shi ne da gashin jimina da kuma ado na alfarma. Shi ma kamar Kakaki, Sarkin Kano Rumfa ne ya fara amfani da shi kuma shi ma daga lokacin sa ne ya shiga cikin ala ta sarautar Kano.

3. Tambari: Shi ma ya samo asali ne tun a lokacin mulkin Haɓe, kuma shi ma ba a kaɗa wa kowa shi face Sarki. To shi ma tambari ya na cikin kayan ala ta Masarautar Kano wacce ta keɓanta ga Sarki shi kaɗai.

4. Sandar Girma:Wannan wata sanda ce da ta ke ɗauke da wani ado mai kama da na azurfa, mai zubin kan sarki a saman ta. Ita kuma ta samo asali ne tun lokacin da Turawa su ka ci sarakunan mu da yaƙi. Idan za a naɗa sabon sarki, a ranar bikin naɗi Gwamna ko Di’o zai damƙa ta ga Sarki. Alama ce da ta ke nuna ka zama sarki mai cikakken iko a gwamnatance. Wannan ya sa ake kiran ta Sandar Girma kuma shi ya sa ta shiga cikin ala ta kowace masarauta.

Waɗannan su ne kayayyakin ala na Kano, kuma duk sarkin da aka yi a Kano waɗannan su ne abin da yake gada kuma da su ne za ka shaida Sarkin Kano a ko ina, ko da kuwa taron sarakuna ne su ke zaune za ka iya shaida Sarkin Kano in ka dubi ƙafar sa ka ga takalmin gashin jimina ko idan ya na tafiya ka gan shi riƙe da tagwayen masu ko kwari da baka.

MASARAUTAR RANO DA ALAR SARAUTAR KANO: 

Lokacin da aka yanke Masarautar Ringim daga Kano, Sarkin Ringim ya fara amfani da Tagwayen Masu, ganin cewa shi ma tsatson Gidan Dabo ne, saboda jikan Sarkin Kano Usman ne. To amma saboda ganin idan an ƙyale shi ya ci gaba da amfani da shi, to ba shakka wannan alar ta Kano za ta samu tasgaro babba. Wannan dalilin ya sa a lokacin Sarkin Kano Ado Bayero ya yi masa magana a kan ya yi haƙuri saboda a kare al’adar. Haka a zamanin Sarkin Kano Sanusi II shi ma a wannan lokacin Sarkin Ringim ɗin ya sake sabon yunƙurin riƙe Tagwayen Masun. A wannan lokacin ma Sarkin Kanon ya yi masa magana a kan ya yi haƙuri, ba don bai gada ba, sai don a kare alar Masarautar Kano.

Bayan Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yanka Masarautar Kano zuwa gida biyar, yaƙara masarautu gudu hudu: Bichi da Gaya da Ƙaraye da kuma Rano a shekarar 2019. Sarkin Rano ya fara saka wannan takalmi na gashin jimina, wanda hakan abu ne da zai saka mutum cikin ruɗani domin alar Kano ce, ba ta Rano ba. Hakan zai iya saka mutane tunanin cewa shin Sarkin Rano ma Magajin Rumfa ne? 

Mu ɗauka cewa Sarkin Rano Magajin Rumfa ne, to ko da hakan ne babu wata hujja da zai saka Takalmin Gashin Jimina in ba shi ne ya gaji Gidan Rumfar ba. Misali, sarakunan Bichi ba su taɓa amfani da wannan takalmi ba in ba sun shigo Gidan Dabo ba, kamar yadda mu ka gani a wajen Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda har ya bar ƙasar Bichi a matsayin Sarki bai taɓa amfani da Tagwayen Masu ko Takalmin Gashin Jimina ba. 

Wannan ya yi nuni da cewar in har Sarkin Rano ya ci gaba da saka Takalmin Gashin Jimina, babu abin da zai hana Sarkin Bichi ya saka ko ya riƙe Tagwayen Masu. Haka shi kan shi Sarkin Ringim, babu abin da zai hana shi riƙe Tagwayen Masu ko saka Takalmin Gashin Jimina. 
Sarkin Kano murabus, shi ma babu abin da zai hana masa saka Takalmin Gashin Jimina ko ya riƙe Tagwayen Masu, saboda da man sun haramta a gare shi ne saboda su na cikin kayan alar masarautar da ya bari. To idan kuwa alar ta rushe, babu abin da zai hana shi yin amfani da su. 

Ina mai bada shawara cewa ya kamata waɗanda abin ya shafa su yi duba cikin wannan al’amari su samar da mafita tun kafin salwantar alar Masarautar Kano. 

A nan ma Mai Martaba Sarkin Rano ne, Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa, tare da dogarai, kuma ya na sanye da Takalmin Gashin Jimina

Allah ya kare mana masarautun mu da mutuncin sarakunan mu gaba ɗaya, amin.

Malam Rabi’u Na’auwa marubuci ne kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum. I-mel: naauwa1@gmail.com

Loading

Tags: Alhaji Ado BayeroEmir of Rano Alhaji Kabiru Muhammad InuwaNorthern emiratesSarkin KanoSarkin Rano
Previous Post

Hotuna: Fatima Ali Nuhu sanye da zoben hanci

Next Post

Me ya farraƙa Adam Zango da Ummi Rahab?

Related Posts

Al'adu

Kare Sabbin Kalmomin Hausa “Saskiyā” (Synonym) da “Gīɗiyā” (Antonym) ta Hanyar ‘Yancin Binciken Ilimi

May 22, 2025
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II kadara ne mai daraja ga Jihar Kano
Al'adu

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II kadara ne mai daraja ga Jihar Kano

January 28, 2024
Minista Hannatu Musawa ta ƙudiri aniyar kafa Gidan Tarihi da Gidan Wasanni na Ƙasa a Abuja
Al'adu

Minista Hannatu Musawa ta ƙudiri aniyar kafa Gidan Tarihi da Gidan Wasanni na Ƙasa a Abuja

December 14, 2023
Khalifa Muhammadu Sanusi II
Al'adu

Sanusi: Magajin Sanusi da Kukuna

June 23, 2023
Shugabannin ƙasashen Afrika a wajen wani babban taron su a Habasha
Al'adu

Ƙungiyar Tarayyar Afrika ta zaɓi Swahili a matsayin harshen da za ta riƙa aiki da shi

February 10, 2022
Marigayi Alh. Mamman Raba-Gardama. Hoto daga: Abdulaziz Abdulaziz
Al'adu

Ta’aziyyar Muhammadu Ɗan Sanyinna (Raba-Gardama)

January 11, 2022
Next Post
Me ya farraƙa Adam Zango da Ummi Rahab?

Me ya farraƙa Adam Zango da Ummi Rahab?

Comments 9

  1. Nazirun Jarumi Rano says:
    4 years ago

    Kaje kasake binchike Kan Masarautar Rano Amma Wannan sharshin naka Akwai kuskure kazo Akaranta maka daga yadda muka samo Asalin Sanya takalmin gashin jimina wadda harkokuwa da idan Mukasaka har Gidan Sarki Sai Munzo da ita lokachin Sarkin Kano Alwali wadda yayan Mahaifiyar Sarkin Rano jibir ne Kuma mahaifiyar Sarkin Rano jibir ce tasanar dashi idan zaisa Yasaka Aiya iyakar sa Amma karyakara Dan Haka daganan mukasami sunan Sarkin karkakara .Sauran bayani saikazo kayi biyaya saikasamu Har Inda Masarautar Rano ta Riga Kano kafuwa .

  2. Hassan musa katsina says:
    4 years ago

    Masha Allah , Allah yakara basira
    Ina tambaya, Alar masarautar Rano guda nawace, dawace Alar ce Masarutun da Duke cin gashin Kansu , Duke Amfani dasu, ahalin yanzu..

  3. Rabiu Na'auwa says:
    4 years ago

    Malam Naziru, Da hujja ake karyata mutum ba da rubutun da baya karantuwa ba. Kana da damar futo da hujjojin kare Sarkin Rano ko masarautar Rano, sai Jama’a su yi alkalanci.
    Duk abinda na fada na ina da cikakkiyar hujjar kare rubutuna in halin hakan ya taso.

    Malam Hassan Musa Katsina.
    Ina ganin ga wani Shaihun Malami nan daga Rano, wato Malam Naziru kila zai karar da mu ta wannan fannin wajan zayyano mana Alar Masarautar Rano da lokacin Samuwarsu sai mu karu

  4. Muhammad Musa rano says:
    4 years ago

    Malam Rabi’u na’awu, ina ganin Kaine kafi cancanta da kakawomana su tun da kace basa ciki, to ya akai kasan baya ciki ba tare da ka lissafo waɗanda ake dasu a ranon ba, wannan bincike naka haƙiƙa akwai gyararraki a cikin sa. Kuma kamar yadda ya kamata shi me kayi takakkiya Ina dai nufin kayi takanas ta wannan gari da kake karewa domin zuwa wajen WAKILIN TARIHIN RANO domin ci kasa lalitarka ta ilimi tinda dai akwai giɓi atare da ita. Haaza wasalam

  5. Nasiru Ibrahim Rano (maso Rano) says:
    4 years ago

    Ba iya Sarkin kano ne yake da aladar saka takalmin jimina ba yakamata maabota tarihi Ku rika fadada bincike saboda tun kafin Sarkin kano ya fara saka takalmin jimina akwai sarakunan da suke saka takalmin jimina

  6. Ibraheem Abubakar Hussain says:
    3 years ago

    Ƴan masarautar Kano kaɗai ke da ƙahon busawa. Shi ya sa duk sai su cikawa mutane kunne da sokiburutsu, sa dagula tarihi. Sun mai da Rano kamar ba wani cikakkiyar masarauta mai cin gashin kanta ba. Ba za ka taɓa jin wata kalmar yabo da akai ga masarautar Rano ba, ko a bayyana wani tarihinta. Wato wai suma irin sunyi mana yanda sarauniyar Ingila ta yiwa namu masarautun lokacin mulkin-mallaka. Sun manta cewa mu Ranawa muka taimaki Kanawa daga sharrin Ningawa, waƴanda sukai ta so su huce su kawo hari, muka tare musu hanya muka ceci Kano daga abin fargabar ta.

    Duk kayayyakin tarihi mallakim mu sun kwashe. Har akwai wurin da ba’a bari ƴan Rano su shiga a Gidan-makama da ke Kano. An rubuta littafi na tarihi, sun haɗa conspiracy sun hana a wallafa—wai duk nan dan kar a san Rano a yanda muke.

    Har shas-han-shan yaran Kanawa ka kan ji suna mamaki in aka faɗa musu cewa Rano masarauta ce mai cin gashin kanta, me taƙama da iko nata ma ƙashin kanta, wacce ta kafu a garin da yake kafe kafin a haƙa fandishin ɗin Kano kwanakin baya.

    We are aware. And, eventually, we’ll do away with all the lies and replace them with plain truthes about Rano. Tafin hannu ba zai iya kare rana ba.

  7. Ibraheem Abubakar Hussain says:
    3 years ago

    Ƴan masarautar Kano kaɗai ke da ƙahon busawa. Shi ya sa duk sai su cikawa mutane kunne da sokiburutsu, sa dagula tarihi. Sun mai da Rano kamar ba wani cikakkiyar masarauta mai cin gashin kanta ba. Ba za ka taɓa jin wata kalmar yabo da akai ga masarautar Rano ba, ko a bayyana wani tarihinta. Wato wai suma irin sunyi mana yanda sarauniyar Ingila ta yiwa namu masarautun lokacin mulkin-mallaka. Sun manta cewa mu Ranawa muka taimaki Kanawa daga sharrin Ningawa, waƴanda sukai ta so su huce su kawo hari, muka tare musu hanya muka ceci Kano daga abin fargabar ta.

    Duk kayayyakin tarihi mallakim mu sun kwashe. Har akwai wurin da ba’a bari ƴan Rano su shiga a Gidan-makama da ke Kano. An rubuta littafi na tarihi, sun haɗa conspiracy sun hana a wallafa—wai duk nan dan kar a san Rano a yanda muke.

    Har shas-han-shan yaran Kanawa ka kan ji suna mamaki in aka faɗa musu cewa Rano masarauta ce mai cin gashin kanta, me taƙama da iko nata ma ƙashin kanta, wacce ta kafu a garin da yake kafe kafin a haƙa fandishin ɗin Kano kwanakin baya.

    Mun fa san cewa ‘Ado·ya’ shi ne ya hana a yi mana state tare da sauran jihohin da aka ƙirƙirar daga baya.

    We are aware. And, eventually, we’ll do away with all the lies and replace them with plain truthes about Rano. Tafin hannu ba zai iya kare rana ba. Allah zai kai mu lokacin da mu ma za mu zama ma su murya ta ƙashin kanmu.

  8. Baffa Galadima RANO says:
    2 years ago

    Yakamata masu bincike da bayyana tarihi surinka fadada bincike .don duniya tasani masarautar RANO tanada kayan alar ta tundaga zamanin kwararrafawa,zuwa hausawa(habe), harzuwa Fulani… Munada kayan ala wadanda sukafi na sauran masarautun kasashen hausawa da Fulani ,yawa da tarihi …….. Kabiyoni don’t ingama kayan alar mu da tarihinsu….Wanda nasan da yardar ALLAH kana jinsu zakasake Sabin rubutu nagaskiya kan kayan alar masarautar RANO da KANO. SAI NAJIKA

  9. Yusuf Garba CLN says:
    1 year ago

    Masha Allah. Allah ya Saka da alkairi.

    Kayi kokari sosai Kuma Allah ya saka Maka da alkairi wajan karar da masu karatu ilimi to amma har yanzu Ina ganin tarihi da girman masarautar Rano ya wuce haka kamar yadda ka labarto shi. Don haka zai zama rashin adalci ga kasar Rano wadda a bisa tarihi ance ita ma kamar takwarar ta ta Gaya duk sun girmi ita Kanta Kano din. Hakazalika gidan da kake magana kan shi kar ka manta da cewar ba fa su ne suka fara sarauta a Kano ba.

    Allah ya sa mu dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!