• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yunƙurin kutsawa a baddala alƙaluman bayanan INEC bai yi nasara ba – Farfesa Yakubu

by DAGA WAKILIN MU
September 11, 2022
in Nijeriya
0
Farfesa Mahmood Yakubu ya na gabatar da jawabi a taron

Farfesa Mahmood Yakubu ya na gabatar da jawabi a taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHUGABAN Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa sababbin dabarun killace alƙaluman zaɓe ta hanyar na’urori da manhaja sun tabbatar da cewa zamanin baddala sakamakon zaɓe ko yin kutse cikin rumbun tattara bayanai ya wuce.

Yakubu ya bayyana haka ne a wani taron masu ruwa da tsaki kan harkokin zaɓe da ƙungiyar YIAGA Africa ta shirya a Abuja.

Ya ce ko a zaɓen gwamna na jihohin Ekiti da Osun da aka yi a baya-bayan nan, ‘yan kutse daga ƙasashe daban-daban, har da wasu daga nahiyar Asiya, sun yi ƙoƙarin kutsawa rumbun tattara bayanai na INEC ta cikin manhaja domin su baddala alƙaluman zaɓen, amma ba su yi nasara ba.

Ya ƙara jan kunnen ma’aikatan hukumar da masu sa-ido cewa tilas sai an ƙara sa ido sosai kuma an ƙara ƙarfafa hanyoyin hana ‘yan kutse shiga manhaja domin baddala sakamakon zaɓe.

Ya ce: “Kuma mun ƙara jaddadawa da ƙara ɗora nauyin kulawa ga injiniyoyin mu cewa kada su yi sanyin jiki wajen hana duk wata ƙofar da ‘yan kutse za su iya kai farmaki a manhajar tattara sakamakon zaɓe.

“Waɗannan hanyoyi biyu da mu ka shigo da su yanzu su na da ingancin da babu yadda masu baddala sakamakon zaɓe ko masu kutse za su iya yin nasarar shiga rumbun tattara bayanai ko manhajar alƙaluman zaɓe.

Wani sashe na mahalartan taron

“Hanyoyin biyu, wato tsarin amfani da na’urar BVAS da kuma manhajar IReV, su na da ingancin killace dukkan bayanai da alƙaluman zaɓe ba tare da shakkun an kutsa an baddala su ba.

“Ita na’urar BVAS aikin ta shi ne tura hoton tambarin yatsan mai dangwala ƙuri’a da kuma tantance fuskar wanda ya dangwala yatsa bisa na’urar, sannan kuma ta kwafi fom na sakamakon zaɓe (EC8A) ta tura cikin manhajar IReV.”

A nasa jawabin, Babban Daraktan YIAGA Africa, Mista Samson Itodo, ya yi kira ga INEC da ta ƙara wayar wa da jami’an ta da waɗanda za a ɗauka aikin zaɓe nan gaba kai sosai domin su ƙara fahimta tare da samun ƙwarewa a dukkan hanyoyin da za a bi domin tattarawa, turawa da killace sakamakon zaɓe sun gudana a sauƙaƙe.

Shugaban YIAGA Africa, Mista Samson Itodo, ya na gabatar da jawabin sa a taron
Jami’ai riƙe da kwafen rahoton Yiaga Africa kan zaɓuɓɓukan gwamna na Ekiti da Osun (Hotuna daga: INEC)

Loading

Tags: 'yan kutsealƙaluman zaɓeBVASHukumar Zaɓe ta ƘasaINECIReVmahmood yakubuna'ura.Samson ItodoYiaga Africazaɓe
Previous Post

Masu tattakin Rarara daga Kaduna zuwa Kano sun yi tozali da gwanin su

Next Post

Dalilin mu na ƙirƙirar Kadawood daga cikin Kannywood – Nura MC Khan

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Nuradden Muhammad Usman (MC)

Dalilin mu na ƙirƙirar Kadawood daga cikin Kannywood - Nura MC Khan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!