ƘUNGIYAR Furodusoshi ta Arewa (Arewa Film Makers Association of Nigeria (AFMAN), reshen Jihar Kano, ta gudanar da zaɓen sababbin shugabannin ta inda duk wanda ya tsaya takara ya ci babu hamayya.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa an rantsar da shugabannin domin gudanar da shugabanci na tsawon shekara biyu.
An gudanar da zaɓen ne a yau Asabar, 3 ga Disamba, 2022 a Majalisar Matasa ta Tarauni da ke unguwar Gyaɗi-Gyaɗi, Kano, cikin kwanciyar hankali da lumana.
Tun da farko, ‘yan kwamitin zaɓen sun bayyana yadda su ka bi mataki na sayar da fom tare da tantance ‘yan takarar, wanda har zuwa lokacin da za su gudanar da zaɓen kujeru 10 da za a yi takarar duk akwai waɗanda su ka tsaya neman muƙamin, sai dai kuma dukkan su ba a samu wata kujera da mutane biyu su ka sayi fom don neman matsayi ɗaya ba.
Duk da haka an shiga zaɓen, amma da sharaɗin dai duk wanda ya kasa samun goyon baya ƙasa da kaso 50 bisa 100 to ya zama bai ci zaɓen ba, saboda haka dokar zaɓen ta ke.
Haka dai aka shiga zaɓen tare da amincewar ‘yan ƙungiyar da kuma ‘yan takarar. Don haka dukkan ‘yan takara sun ci zaɓen ba hamayya.
Shugabannin da aka zaɓa su ne:
* Musa Gambo a matsayin Shugaba
* Mansurah Isah – Mataimakiyar Shugaba
* Mustapha Anwar – Sakatare
* Abubakar Adamu G. Boy – Ma’aji
* Hassan Maiwada – Sakataren Kuɗi
* Zaharaddeen Muhammad – Sakataren Yaɗa Labarai
* Abubakar Alaramma – Sakataren Yaɗa Labarai na Biyu
* Ali Watch Me – Jami’in Yaɗa Labarai na Ɗaya
* Rahama M.K. – Jami’ar Yaɗa Labarai ta Biyu
* Maimuna Muhammad (Wata Yarinya) – Jami’ar Walwala.