• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zaɓen 2023: Ba za mu take umarnin kotu ba – INEC

by DAGA WAKILIN MU
November 9, 2022
in Nijeriya
0
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya na gabatar da jawabi ga manyan alƙalan

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya na gabatar da jawabi ga manyan alƙalan

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa za ta ci gaba da bin umarnin da kowace kotu ta bayar a dukkan hukunce-hukuncen da su ka shafi zaɓe.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke jawabi wurin buɗe Taron Alƙalai na Ƙara wa Juna Ilmi Kan Zaɓen, wanda aka yi ranar Litinin a Cibiyar Inganta Harkokin Shari’a (NJC), a Abuja.

Ya ce: “An shirya irin wannan zama kafin zaɓen 2019, inda aka yi bitar rikice-rikicen ƙararrakin da za su taso bayan zaɓe. Kuma wancan taron da mu ka yi ya yi tasiri sosai a lokacin.

“Saboda an samu raguwar hukunce-hukuncen da kotuna ke bayarwa masu cin karo da juna. Kuma an samu raguwar yawan zaɓen da kotuna ke sokewa masu yawan gaske.” 

Yakubu ya gode wa manyan alƙalai da Hukumar Kula da Shari’a ta Ƙasa dangane wannan taro mai muhimmanci, wanda ya ce babu shakka zai rage yawan ƙararrakin zaɓe a kotuna.

Dangane da muhimmancin taron, Yakubu ya buga misali da irin matsalolin da ake samu a kotuna dalilin yanke hukunci masu karo da juna da kotuna ke yi.

Alƙalan su na sauraren jawabin shugaban INEC, Farfesa Yakubu

Ya ce, “An samu wata kotu ta yi fatali da hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke, ta umarci INEC ta bayar da satifiket ɗin nasarar zaɓen fidda gwani ga ɗan takarar da Kotun Ƙoli ta soke zaɓen sa. To kun ga wannan cikas ne sosai ga hukumar zaɓe.

“Irin wannan kuma shi ke haifar da cinkoson shari’un zaɓe a kotu. Kuma an maida hannun agogo baya, tunda an sake shari’ar kenan wataƙila ma har sai an kai ga komawa Kotun Ƙoli.” 

Haka kuma shugaban na INEC ya nuna damuwa dangane da yawaitar ƙararrakin da aka haɗa da aka da sunan INEC aka maka kotu har sama da 600, a zaɓen fidda gwanin ‘yan takarar jam’iyyu daban-daban.

Yakubu ya bayyana cikin damuwa cewa: “Ko kwanan nan wata jam’iyya ta zo a rana ɗaya ta kawo mana sunayen sabbin ‘yan takara 70 da ta ke so a cire sunayen na farkon da aka aiko mana, a maye gurbin su da sabbin da su ka kai mana.”

Loading

Tags: 'yan takaraalkalaiDokar ZaɓeINECKotun Ƙolikotunamahmood yakubuZaɓen 2023
Previous Post

Zaɓen 2023: Atiku ya mai da hankali kan kamfen, ya rabu da su Wike ‘yan bulkara – Rundunar Yaƙin Atiku

Next Post

‘Yan sanda sun kama Imam Abdullahi Indabawa saboda yaɗa kalaman ɓatanci a kan jarumin Kannywood

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Indabawa (a hagu) da Abdul'aziz

'Yan sanda sun kama Imam Abdullahi Indabawa saboda yaɗa kalaman ɓatanci a kan jarumin Kannywood

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!