• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zaɓen 2023: Fiye da mutane miliyan 3 za su yi zaɓe a sansanin ‘yan gudun hijira – INEC

by DAGA WAKILIN MU
September 8, 2022
in Nijeriya
0
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A ƘOƘARIN da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ke yi don ganin ta yi shirin gudanar da zaɓen 2023 da wuri, Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce aƙalla fiye da ‘yan gudun hijira miliyan uku ne za su yi zaɓe a sansanoni daban-daban a ƙasar nan.

Ya ce tuni hukumar sa ta fara aikin tsame sunayen waɗanda su ka yi rajista sau biyu ko fiye da haka.

Shugaban ya bayyana fara aikin tsame sunayen waɗanda su ka yi rajistar mallakar katin zaɓe sau biyu ko fiye da haka cikin wannan makon a Abuja.

Ya bayyana haka lokacin da ya ke jawabi a wurin taron masu ruwa da tsaki kan bitar  fayyace ƙa’idojin zaɓe a sansanin masu gudun hijira, wanda aka shirya a ranar Talata a Abuja.

A taron, Yakubu ya ce sake nazarin tsare-tsaren ya zama wajibi domin rabon da a sake bibiyar sa tun na ƙarshe da aka yi a 2018, kafin zaɓen 2019.

Ya ce ana nan ana kuma ci gaba da tsame sunayen da aka yi rajista sau biyu ko fiye da haka ana zubarwa, domin a tabbatar da cikakkun adadin yawan waɗanda za su mallaki katin rajistar zaɓe guda ɗaya tilo, kamar yadda doka ta tanadar.

Ya ce sai an kammala tsame sunayen masu rajistar fiye da sau ɗaya sannan za a bayyana ranar da za a liƙa sunayen masu rajista, kowa ya gani a faɗin ƙasar nan.

Ya ce: “A tsarin ganin an gudanar da zaɓuka cikin sansanin ‘yan gudun hijira, mu na so mu tabbatar cewa wannan tsari kamar yadda doka ta tanadar, ba a bar kowa a baya ba.

“Za mu tabbatar kamar yadda dokar zaɓe ta shimfiɗa cewa an gudanar da zaɓe a sansanin masu gudun hijira, kuma naƙasassu sun samu damar yin zaɓe da kuma waɗanda wani ibtila’i na barin gidajen su ya shafe su, kamar ambaliya.”

Shigaban ya ce akwai aƙalla mutane miliyan uku a sansanonin ‘yan gudun hijira daban-daban a ƙasar nan.

Ya ce taron sake nazarin su ya zama wajibi a yanzu, saboda masu gudun hijira ɗin sun ƙaru, sakamakon wasu dalilai, kamar ambaliya.

Ya ce a yanzu kuma za a bayar da himma wajen ganin an wayar da kan mazauna sansanonin gudun hijira dangane da muhimmancin zaɓe da kuma ƙa’idojin da doka ta shimfiɗa wajen gudanar da zaɓe a cikin masu gudun hijira.

Shugaban na INEC ya musanta zargin da Gamayyar Ƙungiyoyin Kare Haƙƙin Jama’a (CSO) su ka yi wa INEC cewa ta karya dokar Sashe na 19(1) na Dokar Zaɓe, sashen da ya fayyace yadda INEC za ta liƙa sunayen waɗanda su ka yi rajista domin kowa ya gani a ƙasar nan.

Ya ce, “Ba mu karya wata doka ba, saboda har yanzu ana kan tantancewa da tsame sunayen waɗanda su ka yi rajista sau biyu ko fiye da biyu tukunna. Idan lokacin da za mu liƙa sunayen ya yi, za mu sanar kowa ya sani, kuma ya gani.”

Ya ce za a liƙa sunayen a dukkan mazaɓu 8,809 da ake da su a ƙasar nan a dukkan ƙananan hukimomi 774 a Nijeriya, kamar yadda Sashe na 19(1) na Dokar Zaɓe ta 2022 ya tanadar.

Ya ce za a haɗa sunayen da aka yi rajista a baya-bayan nan tare da adadin miliyan 84 da ake da su a baya.

Loading

Tags: Dokar ZaɓeINECmahmood yakubuZaɓen 2023
Previous Post

Batun Gwanja: In gaskiya ne, NBC ta soke soshiyal midiya mana – mawaƙi Ɗayyab Maiɗa’a

Next Post

Masu tattakin Rarara daga Kaduna sun isa Kano

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Anas M. Lawan da Mustapha Iliyasu tare da Ayshatulhumaira a ofishin Rarara a ranar Alhamis

Masu tattakin Rarara daga Kaduna sun isa Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!