• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zaɓen 2023: Mawaƙi Muddassir Ƙasim ya haska wa ‘yan Arewa hanyar samun mafita

by DAGA ALI KANO
June 25, 2022
in Labarai
0
Malam Mudassir Ƙasim

Malam Mudassir Ƙasim

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCEN mawaƙi a masana’antar Kannywood, Malam Mudassir Ƙasim, ya yi kira ga ‘yan Arewa da kada su yi sakaci wajen sama wa Arewa mafita ta hanyar zaɓuɓɓukan da za a yi a shekara mai zuwa.

Ya ce wajibi ne kowa ya mallaki katin zaɓe domin samar da shugaban da zai taimaki yankin “ko daga wace jam’iyya ya ke.”

Mawaƙin ya bayyana haka ne a wani tsokaci da ya rubuta mai taken “Arewa Mu Na Tsaka-Mai-Wuya”, wanda ya tura wa mujallar Fim.

Mudassir ya fara tsokacin sa ne da bayyana cewa, “Arewa a zaɓen 2023 an bar kari tun ranar tubani.”

Ya ci gaba da cewa: “Da farko dai da yawan mu ‘yan Arewa gwiwar mu ta yi sanyi a kan makomar Nijeriya, musamman makomar Arewa a yau sakamakon raunin ingancin ‘yan takarkaru, musamman na jam’iyyu masu ƙarfi.

“Tabbas, ba ma shakkar Yarbawa wajen iya mulki da ‘international test’ wajen ayyukan gina ƙasa domin sun ƙware a kan wannan, amma babban abin tsoro da ƙalubale gare mu shi ne mu Arewa a yanzu manyan matsalolin mu uku ne:

1) rashin tsaro sakamakon da aka taɓo Fulanin da ɗaukar fansar su ba ya ƙarewa har abada;

2) rashin ilimin ƙananan yara da mata da matasa;

3) Kama hanyar durƙushewar harkokin noma da kasuwanci.”

A yayin da ya ke juyayi kan ƙalubalen da yankin ke fuskanta,  Mudassir ya ce: “Tambayar a nan, mu da aka ba mu dama shekara takwas ba mu iya magance waɗannan matsaloli ba, sai dai ma ƙara haɓaka su mu ka yi, ta yaya waɗanda ake zargin cewa su na da hannu wajen waccan tsokanar Fulanin da aka yi kuma su ka ƙi bada damar yin burtali don shawo kan matsalar, su ne za su zo su magance mana matsalolin mu? Wallahi abin tabbas akwai ban-tsoro a Arewa!” 

Ya yi nuni da cewa su kuma manyan Arewa, yanzu ba wannan matsalar ce su ka sa gaba ba, “kawai rikicin shugabanci ne a gaban su, ba yadda za a ceto Arewar ba.”

Mawaƙin ya ƙara da cewa babu wani tabbas da yaƙini a kan cewa duk ‘yan takarar nan da su ka fito daga yankuna daban-daban na ƙasar nan za su iya magance matsalar Arewa. 

“Dama-dama wanda ya fito daga yankin Arewa-maso-yamma ma, domin akwai kyakkyawan zato a kan shi na kishin Arewa, amma kuma matsalar ita ce tuni ya yi wa Arewar baƙin cikin samun wannan hazaƙa tashi da ya je ya shiga ƙaramar jam’iyya da a wani yanki kawai ta ke, ba lallai ta iya mamaye ƙasar a wannan zango na zaɓe ba.” 

Da ya koma kan inda za a samu mafita, Mudassir ya ce, “Ni ma kam kai na ya kulle a nan, domin har yanzu ba mu shirya kare kan mu daga yaudarar da ake mana ba. Mun ƙi fita mu yi rajistar katin zaɓe, kowa sai ka ji ya na cewa shi ya daina zaɓe.

“Shin ɗan’uwa idan ka daina fa? Ita ƙasar taka ba za ta daina don ka daina ba, za a zaɓa maka ko ka na so ko ba ka so. To gara ka fito ka yi katin zaɓe, mu yi rubdugu mu jefa ma wanda mu ke ganin zai ba mu mafita mai ma’ana a Arewa ko daga wace jam’iyya ya ke. 

“Ƙuri’a ɗaya tak za ta canja mulkin kama-karya. Haka nan ƙuri’a ɗaya tak ke jawo kama-karya.”

Loading

Tags: 'yan takara.2023 electionsArewamafitaMudassir KasimsiyasazabeZaɓen 2023
Previous Post

Furodusa Isma’il FKD ya zama angon A’isha Umar

Next Post

Na tuba, ba zan ƙara ba – Mawaƙi Sufin Zamani a wasiƙar bai wa ‘yan fim haƙuri

Related Posts

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry
Labarai

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry

June 15, 2025
Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
Next Post
Sufin Zamani da takardar tuba da ya aika wa MOPPAN

Na tuba, ba zan ƙara ba - Mawaƙi Sufin Zamani a wasiƙar bai wa 'yan fim haƙuri

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!