A JIYA Asabar aka yi taron fahimtar juna tsakanin ‘yan takarar shugabancin ƙasa na MOPPAN su biyu da ciyamomin ƙungiyar na jihohi.
‘Yan takarar dai su ne Alhaji Adamu Bello Ability da Alhaji Umar Maikuɗi Cashman, waɗanda duk ‘yan Jihar Kaduna ne.
An yi taron ne domin a san abin da kowane ɗan takara yake da burin kawo wa ƙungiyar na cigaba.
An keɓe kowane ɗan takara aka ba shi damar yi wa ciyamomin bayani kan ajandar da yake da ita.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa an yi zaman daban-daban ne, kuma kowane ɗan takara ya yi bayani mai ban-sha’awa tare da ƙoƙarin samun goyon bayan ciyamomin.

Kwamared Lawal Rabe Lemo, Ciyaman ɗin MOPPAN na Katsina, ya lura da cewa wannan zama shi ne na farko a tarihin ƙungiyar da aka taɓa yi.
Ciyamomin da suka wakilci sauran jihohin a taron su ne na Katsina, Sokoto, Zamfara, Adamawa, Taraba, Nasarawa da Neja.
Akwai kuma wasu daga cikin membobi da jami’an ƙungiyar da suka halarta daga Kaduna.
An yi zaman a ɗakin taro na Nuhu Bamalli Polytechnic da ke Zariya, Jihar Kaduna.
