MAI Binciken Kuɗi na 2 (Auditor 2) na Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Ƙasa (MOPPAN), Malam Bello Achida, ya yi kira ga ‘yan takara da su yi aiki tare idan aka kammala zaɓen ƙungiyar reshen Jihar Sokoto da za a yi a ranar Lahadi mai zuwa, 11 ga Disamba, 2022.
Uwar ƙungiyar ta ƙasa ce ta naɗa Achida domin ya wakilce ta a wurin zaɓen don tabbatar da an yi zaɓen a cikin nasara.
A tattaunawar sa da mujallar Fim, Alhaji Bello ya ce, “Ina godiya ga Allah da ya nuna mana wannan lokaci da za a gudanar da wannan zaɓe. ‘Tenure’ na shugabannin MOPPAN na Jihar Sokoto ta ƙare tun a watan Agusta na shekarar 2021, ana ta kai ruwa rana, ana ta fitintunu, amma yanzu an kai ƙarshe, har na ba da dama na a je a yi zaɓe, kuma har an kai an sa rana.
“Duk abubuwan da su ka gudana tsawon shekara ɗaya da aka yi, ni uwar ƙungiya ta wakilta, har aka yi nasara.”
Achida ya ƙara da cewa, “Ina roƙo, idan aka yi zaɓe, waɗanda su ka yi nasara su riƙe waɗanda ba su yi nasara ba a yi tafiya tare, su kuma waɗanda Allah bai ba nasara ba, sai su yi haƙuri nasu lokacin ya na nan tafe. Ina fatan a yi wannan taron lafiya, a ƙare lafiya.”
A sanarwar da shugaban kwamitin zaɓen, Sharif Usman Baban Umma ya fitar, ya ce, “A madadin kwamitin zaɓen MOPPAN na Jihar Sokoto, mu na sanar da duk wani mamba wanda ke da rajista da cewa za a gudanar da zaɓen sababbin shugabanni da kuma tantance mambobi haɗi da rantsar da sababbin shugabanni. Amma za a fara tantance mambobi da misalin ƙarfe 9:00 na safe, da fatan za a zo a kan lokaci.”
Za a gudanar da zaɓen a ɗakin taro da ke sakatariyar Ƙaramar Hukumar Sokoto ta Kudu, da misalin ƙarfe 11:00 na safe.
Allah ya ba da ikon zuwa, ya kuma sa a yi lafiya.