A YANZU haka dai za a iya cewa komai ya tsaya cak a masana’antar finafinai ta Kannywood, a sakamakon tunkarowar babban zaɓen 2023.
Binciken da mujallar Fim ta gudanar ya nuna cewa hakan ya faru ne saboda hada-hadar siyasa da ‘yan fim ɗin Hausa su ka shiga ciki dumu-dumu, ana damawa da su.
Duk da yake ba yanzu ba ne karo na farko da ‘yan fim su ka shiga cikin harkokin siyasa, amma ana ganin babu wani lokaci da su ka shi ƙwan su da kwarkwatar su kamar yanzu.
A baya, za ka ga su Sani Danja da yaran su ne kaɗai su ke siyasar waɗanda su ka bayyana duniya ta san da su a cikin harkar siyasa, ko da wani ma ya na yi to sai dai ta ƙarƙashin ƙasa. Amma a yanzu kusan kowane jarumi – ƙarami ko babba, mace ko namiji – ya na cikin harkar siyasa, kuma ba tare da ya ɓoye ba, sai dai idan bai samu damar da zai bayyana ba ya laɓe a bayan wani yadda idan an samo za a ɗan ba shi nasa kason.
Wannan ta sa a yanzu duk wata harka ta fim da waƙa ta tsaya, in dai ba ta fim ba ce. Idan ka na neman wani jarumi ku yi wata mu’amala da shi wadda ba ta shafi siyasa ba, to fa ka haɗa kan ka da aiki, saboda idan ka kira shi za ka ji ko dai wayar sa a kashe ko kuma bai ɗaga ba, domin kila ya na wajen taron siyasa ko ya tafi ganawa da wani ɗan siyasa.
Kuma idan ka je ofisoshin su da wuya ka same su, musamman a Kano.
Wani salo da siyasar wannan shekarar ta zo wa da ‘yan Kannywood shi shi ne duk ƙarfin ka sai dai ka raɓu da wani, ba dai ka ci gashin kan ka ba.
Mujallar Fim ta gano cewa siyasar Kannywood a yanzu ta kasu gida uku zuwa huɗu ne kawai, kuma idan ba ka cikin wannan rukunin to fa sai dai ka zama ɗan kallo.
Gidaje masu ƙarfi a siyasar Kannywood su ne ƙungiyar 13+13 ta Dauda Rarara da kuma ‘Yahaya Bello Network’ (YBN) ta Abdul Amart. Su ne su ka haɗa duk wasu manyan jarumai da mawaƙa a cikin su.
Misali, a YBN akwai Ali Nuhu, Sadiq Sani Sadiq, Umar M. Shareef, da Fati Nijar.
Mata ‘yan fim ma sun ja tasu dagar inda su ka kafa sansanoni. Akwai ɓangaren Mansurah Isah da su ka zo su ka haɗe a cikin tafiyar tallar Asiwaju Bola Tinubu da Dakta Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC a Kano.
Ita kuma ƙungiyar 13+13 ta haɗa ‘yan fim da mawaƙa irin su Baban Chinedu, Hannatu Bashir, Aminu Ala, Yakubu Muhammad da sauran jarumai da mawaƙa, kuma su ma ɗin tallar Tinubu su ke yi. Sai dai a Kano ba su yin ɗan APC, sai a wasu jihohin.
Shi ma mawaƙi Jadda Garko ya yi tasa tungar, su na tallar Tinubu.
A ɓangaren Atiku Abubakar na PDP kuma akwai Naziru Sarkin Waƙa da magoya bayan sa irin su Isah A. Isah a matakin ƙasa. Amma a Kano su na yin APC a takarar gwamna.
A ɓangaren rundunar Kwankwasiyya ta Dakta Rabi’u Musa Kwankwaao, akwai manyan jarumai da mawaƙa irin su Sani Danja, Abba Al-Mustapha, Tijjani Gandu, da Abubakar Sani da su ke tallar jam’iyyar NNPP.
Wata matsala da ake ganin Kannywood za ta iya fuskanta bayan zaɓe ita ce a yanzu ‘yan siyasa sun gane cewa ‘yan fim ba su da wani buri na cigaban masana’antar su, kowa buƙatar da ya sa a gaba ita ce ya samu abin da zai samu ya je ya yi harkar gaban sa.
Sannan ‘yan fim a wannan lokacin sun dunƙule a waje ɗaya kuma duk an gane neman kuɗi ne ya kai su.
Hakan ya sa masu lura da al’amuran industiri su ke ganin cewa idan har jam’iyyar da ‘yan Kannywood su ka fi bai wa ƙarfi ba ta ci zaɓe ba, musamman a Kano, to fa su na da ƙalubale a gaban su. Wanda ya ci zaɓen zai iya gasa masu gyaɗa a hannu, su ma su ji a jikin su.
Gaskiya babban abin takaici ne irin yadda ‘yan Film Na kannywood suka maƙalƙalewa siyasa don kuɗi, ba wai don cigaban al’ummar ba..