A RANAR Talata, 23 ga Nuwamba, 2021, za a yi taron ƙaddamar da sabon bugu na wani sanannen littafin tarihin Daular Usmaniyya a garin Abuja.
Kamfanin Premium Times Books ne ya ɗauki nauyin fito da bugun Nijeriya na littafin mai suna ‘The Sokoto Caliphate’.
A sanarwar da mujallar Fim ta gani, masu shirya taron sun ce a Cibiyar Tunawa da Shehu Musa Yar’Adua da ke Abuja za a yi taron ƙaddamarwar, kuma Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamali, shi ne zai shugabanci taron.
Akwai ɗimbin manyan Nijeriya da aka gayyato. Sun haɗa da Ministan Matasa da Wasanni, Mista Sunday Dare, wanda zai zama babban baƙo na musamman, yayin da Alhaji Nasiru Danu, shugaban kamfanin Casiva Limited, zai zama babban mai ƙaddamarwa.
Babban Editan jaridar’21st Century Chronicle’, Malam Mahmud Jega, shi ne zai gabatar da sharhi kan littafin, inda daga nan wasu zaɓaɓɓun mutane za su yi tattaunawa kan littafin a kan maudu’in muhimmancin tarihin Daular Usmaniyya ga Nijeriyar mu ta yau (wato “The Relevance of the History of the Sokoto Caliphate to Present-day Nigeria.”
Waɗanda aka zaɓa su yi tattaunawar a kan jigon su ne Farfesa Mukhtar Umar Bunza, Kwamishinan Ilimin Gaba da Firamare na Jihar Kebbi; da Farfesa Mohammed Junaid na Tsangayar Ilimi ta Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto; da kuma shi Malam Jega.
Babban Janar Manajan Hulɗa da Jama’a na kamfanin man fetur na Nijeriya, wato NNPC, Mista Ohi Alegbe, shi ne mai tsawatarwa a lokacin tattaunawar. Hasali ma dai shi ne zai yi aikin sanƙira a taron.

Tun a ranar 1 ga Nuwamba ne dai aka gudanar da ɗan ƙaramin bikin ƙaddamar da littafin a Sakkwato a wani sashe na bikin murnar zagayowar ranar da aka naɗa Alhaji Abubakar Sa’ad a matsayin Sarkin Musulmi na 13.
Shi dai wannan littafi mai taken ‘The Sokoto Caliphate’, kamfanin Longmans ne ya fara buga shi a tun a cikin 1967, sakamakon zurfin bincike da Farfesa Denis Murray Last ya yi a lokacin da ya ke ɗalibin digiri na uku (PhD) a Jami’ar Badun.
Jigon littafin shi ne Daular Usmaniyya da aka kafa a ƙarni na 19 miladiyya a ƙarƙashin Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo.
An bayyana cewa a lokacin da ta ke kan ganiyar ta, wannan daula ta malala tun daga ƙasar Kamaru ta yau, ta yi yamma zuwa Burkina Faso, sannan daga arewa zuwa gabas tun daga Agadas har zuwa Ilori.
Turawan mulkin mallaka, musamman ‘yan Birtaniyya da Faransa, sun riƙa kiran yankin da sunan Daular Fulani.