BABBAR Kotun Shari’ar Musulunci da ke Hausawa Filin Hoki a cikin garin Kano ta sanya ranar Talata, 7 ga Nuwamba, 2023 domin ci gaba da sauraron shari’ar da jarumar Kannywood ɗin nan Sadiya Haruna (Sayyada), ta shigar, inda ta ke neman mijin ta, wato mawaƙi Abubakar Ibrahim (G-Fresh), da ya sake ta.
Sai dai kuma shi G-Fresh da lauyan sa babu wanda ya halarci zaman kotun na yau Alhamis, 26 ga Oktoba.
A zaman kotun na yau, lauyan mai ƙara, Barista A.B. Saka, ya roƙi kotun ta ci gaba da sauraron shari’ar sakamakon rashin zuwan lauyan wanda aka yi ƙara kuma ya bayyana wa kotun cewa waɗanda aka yi ƙarar ba su aiko da wani dalili na rashin zuwan su kotun ba.
Kotun, a ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Alhaji Abdullahi Halliru,
ta karɓi koken sa kuma ta amince, inda ta sanya ranar Talata, 7 ga Nuwamba, domin ci gaba da shari’ar.
Idan za kun tuna, mujallar Fim ta ruwaito yadda Sadiya Haruna ta yi ƙarar G-Fresh inda ta ke neman ya sauwaƙe mata saboda ta gaji da zama da shi.