JARUMAN Kannywood biyu, Ali Nuhu da Rabi’u Rikadawa, su na daga cikin gwarzaye ‘yan Arewa waɗanda za a karrama da kyautar girmamawa mai suna ‘2023 Arewa Heroes’ and Philanthropic Award of Excellence’.
Mujallar Fim ta ambato labarin da kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya bayar cewar jaruman su na daga cikin waɗansu fitattun mutanen da masu shirya bikin su ka fitar a yau Juma’a a Abuja.
Mashirya bikin, ‘MACA Peace Ambassadors & Unity Affair Africa’, sun ce za a yi bikin karramawar ta taurarin lardin a ranar 30 ga Satumba, 2023 a Gidan Arewa da ke Kaduna.
A cewar su, sauran waɗanda za a karrama ɗin sun ƙunshi mutane irin su kyaftin ɗin ƙungiyar wasan ƙwallon ƙafa ta Super Eagles, wato Ahmed Musa, da Bishop ɗin Cocin Katolika ta shiyyar Sakkwato, Matthew Kukah, da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu; Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna; Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum, da Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule.
Har ila yau dogon jerin sunayen waɗanda za a karrama ɗin ya ƙunshi Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli; Gwamna Hyacinth Alia na Binuwai; ‘yar kasuwa Hajiya Laylah Ali Othman; Rabaran Mathias Yashim; Prince Bala Audu, Dakta Emmanuel Omale, da wasu.
Shugaban shirya bikin, Nyam Terry, ya yi bayanin cewa za a shirya bikin na shekara-shekara ne don a karrama mutanen da su ka ba da gudunmawa ga ci-gaban yankin Arewa.
A cewar sa, an zaɓi mutanen a tsanake ne saboda ayyukan da su ke yi babu gajiyawa wajen sadaukar da kai ga agajin jama’a, da tasirin su mai kyau kan al’umma da ƙarfafa wa matasa gwiwa, da kuma samar da zaman lafiya.
Ya ce: “Bikin karrama gwarzayen na bana mai taken ‘Taya Gwarzayen Mu Murna’, ya na da burin karrama masana’antu, ma’aikatu, jami’an gwamnati, ‘yan wasa, ƙungiyoyi, da ɗaiɗaikun mutane waɗanda su ka taimaki al’umma ta hanyoyi daban-daban.
“Waɗannan ‘yan Nijeriya daga lardin arewa sun ba da gudunmawa, ta hanyoyi daban-daban, ga cigaban ta da samar da zaman lafiya.
“Mun yi imani da cewa wannan karramawar a ko yaushe zai ƙarfafa masu gwiwa a ko yaushe domin su ƙara himma wajen aikin da su ke wa al’umma.”