Sabon Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Kano kan Masana’antar Kannywood, Malam Sunusi Hafiz (Oscar 442), ya sha alwashin kawo cigaba da kuma bunƙasa harkar ta fim a ƙarƙashin ofishin sa.
Ya ce za su gyara “tarwatsawar” da gwamnatin da ta gabata ta Dakta Umar Ganduje ta yi a masana’antar.
Sunusi Oscar ya yi wannan kalamin ne a yayin wata tattaunawa da ya yi da mujallar Fim a Kano.
Tun da farko sai da fitaccen daraktan ya yi cikakken bayani kan irin aikin da ofishin sa ya ƙunsa. Ya ce: “Wato shi wannan muƙami da mai girma gwamna ya ba ni, muƙami ne a kan ta ita masana’antar; wato shi gwamna ya na buƙatar mutum da zai riƙa ba shi shawara da gudunmawa na labaran cikin ta, musamman abin da ya shafi ci-gaba da kuma abubuwan da aka samu naƙasu a cikin su, domin a tallafa mata zuwa gaba daga naƙasun da ta samu a shekaru takwas da ta yi a hannun tsohuwar gwamnati. To wannan shi ne dalilin da ya sa ya yi wannan muƙami.
“Kuma ita wannan masana’antar, a yanzu za ta amfani abubuwa sosai da wannan muƙami, don duk wata hanyar da ake bi a samar da ci-gaba, to wannan masana’antar za mu kai ta ga wajen. Domin mu na cikin wannan masana’antar shekara da shekaru, don haka mun san abin da ya ke damun ta kuma mu na cikin wannan tsari, don haka za mu yi ƙoƙari in Allah ya yarda mu sanar wa da gwamnati abin da ya ke damun ta. Kuma in-sha Allahu wannan gwamnati za ta share mana hawayen mu.”
Da mu ka tambaye shi abin ya bambanta ofishin sa da na Hukumar Tace Finafinai, sai ya ce, “Ai abubuwan da su ka bambanta mu su na da yawa. Shi aikin Hukumar Tace Finafinai shi ne a kai fim su duba su tace shi su tabbatar da ingancin sa tare da ba da izinin fitar da shi don kada abin da za a fitar ya zama ya saɓa da addini ko al’adar mu da sauran wasu abubuwa da doka ta ba su damar aiwatarwa.
Amma shi ofishi na duk wani abu da ya shafi masana’antar ya na ƙarƙashin ofishin mu, saman ta da tsakiyar ta da kuma ƙasa, duk abin da ya shafi harkar ita masana’antar, to mu mu na da ruwa da tsaki da shi.”
Ko wane irin shiri Oscar ya yi na kawo gyara a cikin harkar fim? Amsa: “To mu da man a shirye mu ke, domin abu ne da ya daɗe ya na damun mu tun ba yau ba. Kuma a yanzu da Allah ya ba mu wannan dama, in-sha Allah za mu amfani da wannan damar mu ga mun taimaki ita wannan masana’antar ta inda duk ya kamata. Kuma za mu yi tuntuɓa daga wajen jagororin mu ɗaya bayan ɗaya, kowanne za mu ji abubuwan da ya kamata su taimaka saboda a taimaki masana’antar.
“Za mu ɗauki abu na gaskiya mu ajiye wanda ba na gaskiya ba mu yi amfani da abin da ya dace, mu kai wa gwamnati shi domin ci-gaban masana’antar”.
To da ya ke shi ɗan fim ne, ko wanne sauyi ya ke ganin zai samar fiye da wanda ake gani a yanzu cikin harkar fim? Sai ya ce, “Za mu yi kallo duba da yadda zamani ya canza, kuma za mu yi bakin ƙoƙarin mu don ganin mun tafiyar da wannan masana’anta a zamanance kamar yadda duniya ta canza, mu ma mu na fatan wannan masana’anta ta canza domin har yanzu mu na nan a ƙaramin matakin da tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ya tafi ya bar mu.
“Mun yi zaton wannan gwamnatin ta Ganduje da ta zo za ta ɗora, sai ya zamanto sana’ar ma ta gagara, babu ita, ya zama an tarwatsa ‘yan kasuwa, aka saka masu tsoro da kama na kamawa.
“To ka ga tunda mai saya ba ya nan, idan ka ɗauko kaya ina za ka kai?
To, saboda haka su ma waɗanda su ke tsarawar su ma sai aka fara bin su, masu ba da umarni irin mu, mu ma aka bi ana kama mu ɗaya bayan ɗaya, aka sa matsorata. Wani ko ba ya son tsarin, haka ya haƙura ya bi domin ya na ganin idan bai bi tsarin ba za a kama shi, tun ba ya so haka ya haƙura ya bi. Amma mu da mu ka gane cewar wannan tsarin da aka fara ya na da ƙarshe, to duk irin wahalar da mu ka sha babu ja da baya; haka mu ka haƙura har Allah ya kawo mu ga wannan lokacin, yanzu ga shi Allah ya sa mai girma gwamna ya ba ni muƙami a wannan masana’antar.
“Kuma za mu haɗa kai da duk wanda ya ke son ci-gaba a cikin wannan masana’anta, mu haɗa kai mu kawo ci-gaba baki ɗaya.”
Da yake zamani ya canza an samu ci-gaba ta fuskar kasuwar da ma yadda ake shirya fim ɗin wane irin gyara za su samar a cikin harkar?
Sai Sunusi Oscar ya amsa da cewa, “To shi ne abin da na faɗa maka a baya, cewar za mu yi tuntuɓa ta duk inda ya kamata a wajen masana domin mu kai wannan masana’antar gaba. Ba mu za mu yi ba, mu namu wato gabatarwa ne, don haka za mu nemi masana su ba mu shawara da kuma abin da mu ka sani, mu tattara shi, mu kai wa mai girma gwamna, kuma mun san daga mun kai in-sha Allahu gwamnati za ta share mana hawayen mu.”
Fitaccen daraktan ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf da jagoran Kwankwasiyya kan wannan muhimmin aiki da ya ɗora masa, ya na cewa, “Ina godiya ga Allah da ya sanya na ke da wannan muƙami a yanzu na Babban Mataimaki ga Gwamna kan Masana’antar Kannywood. Kuma ina godiya ga mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da Madugun ɗarikar Kwankwasiyya, Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, bisa wannan muƙami da su ka ba ni. Allah ya saka musu da alheri, Allah ya sa rayuwar su ta gaba ta yi kyau, ya kawo musu babban rabon da ya fi wanda su ke kai a yanzu.”