HUKUMAR Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano ta ce za ta haɗa hannu da Ma’aikatar Shari’a ta jihar domin ladaftar da ‘yan fim masu karya dokokin hukumar.
Babban Sakataren hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, shi ne ya bayyana haka a yayin wata ziyara da ya kai wa Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano don taya shi murna tare da ƙarfafa alaƙa da ma’aikatan Hukumar Shari’a da yin aiki tare.
El-Mustapha ya ƙara da cewa ya kuma je ma’aikatar ne domin ya kai kwafen sababbin dokokin da hukumar sa ta ke so ta ƙara tare da zamanantar da tsofaffin dokokin da ta ke aiki da su domin su yi daidai da zamanin da ake ciki a yanzu.

Ya ce: “Mafi yawan dokokin da hukumar ta ke aiki da su a halin yanzu su na buƙatar sauyi ko kuma a yi masu gyara.”
A nasa jawabin. Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista Haruna Isah Dederi, ya yaba wa El-Mustapha dangane da ƙoƙarin da ya ke yi na ganin hukumar ta cimma nasarorin ta.
Ya ce ƙofar su a buɗe ta ke domin bayar da dukkan shawarwarin da za su taimaki hukumar domin kawo cigaba.
