SABON zaɓaɓɓen shugaban ƙungiyar jaruman Kannywood ta Jihar Kaduna, wato ‘Kaduna Guild of Actors’, Alhaji Zaharaddin Sani Owner, ya bayyana ƙudirin sa na kawo sauyi a harkar fim a jihar.
Haka ya ce ɗaya daga cikin abubuwan da kwamitin shugabanni da ya ke jagoranta zai yi shi ne ya jawo gwamnati cikin tafiyar, ta yadda za su bar abin alheri ko da bayan sun gama wa’adin su na shugabanci.
Zaharaddin, wanda fitaccen jarumi ne, ya bayyana haka ne a cikin tattaunawar da ya yi da mujallar Fim jim kaɗan bayan an rantsar da shugabannin ƙungiyar a jiya Asabar, 12 ga Fabrairu, 2022 a Kaduna.
An dai zaɓi shugabannin ne bayan da kwamitin zaɓen da haɗaɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) da kuma jama’ar da aka yi zaman majalisi (congress) da su a ranar da aka yi zaɓen MOPPAN ɗin su ka amince da umartar dukkan shugabannin riƙo na ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin MOPPAN da su shirya wa kan su zaɓe bayan zaɓen da wata ɗaya.

Ƙungiyar jarumai ta yi hoɓɓasa tare da samun goyon bayan darakta Al-Amin Ciroma, wanda ya kafa kwamitin zaɓe na mutum biyar da su ka haɗa da Yauhuza Ilu (ciyaman), Yusuf Maina (sakatare), A’ishatu Umar Mahuta, Fati Yusuf Haske, da Alin Dman.
A ranar Alhamis, 21 ga Disamba, 2021 aka taru domin yin zaɓen a lambun ‘Side Resort’ da ke Titin Raɓah a cikin garin Kaduna, amma ba a yi zaɓen ba saboda amincewar da sauran ‘yan takara su ka yi su ka janye wa abokan hamayyar su, musamman ɓangaren ciyaman, wanda tun farko ‘yan takarar su ne Zaharaddin Sani Owner, Sabi’u M. Gidaje da kuma Nura MC.
Sun yi yarjejeniya a tsakanin su, inda dukkan su su ka amince su ka janye wa Zaharaddin, Sabi’u Gidaje kuma ya zama mataimakin sa.
A lokacin, Nura MC bai samu halartar taron ba, amma kuma dukkan abubuwan da su ka faru a wurin an sanar da shi, kuma ya amince, sannan ya yi masu fatan alheri.
Tun bayan zaɓen ne kuma sai aka ci gaba da shirye-shiryen bikin rantsar da sababbin shugabannin.
A jiyan, an fara taron rantsarwar ne da misalin ƙarfe 2:15 na rana, bayan da aka gaza farawa da ƙarfe 10:00 na safe da aka sanya da farko, kasancewar an jiran wasu muhimman mutane da aka gayyata.
Bayan an buɗe taro da addu’a, sai uban taro, Alhaji Balarabe Jaji, ya yi jawabi, inda ya ce, “Mu na yi wa Allah godiya da ya nuna mana wannan rana mai tarin albarka. Haka kuma mu na yi wa kowa barka da zuwa wannan wuri domin rantsar sababbin shugabanin mu.
“Alhamdu lillahi, kafin mu zaɓi mutum, Allah ya riga da ya zaɓe shi, abin da ya rage mana mu nemi alkhairi da kuma fatan alkhairi. Waɗannan shugabanni da ku ke gani ba yin kan su ba ne, lallai masana’antar na neman matasa masu basira, hazaƙa da jajircewa, don haka mu ba su haɗin kai da goyon baya.
“Ana yi wa masana’antar nan shaidar rashin haɗin kai. Mu daure mu haɗa kai, mu yi tafiya da masoyan mu, mu iya bakin mu, sannan mu haɗa kai.
“Idan mu ka duba, ‘yan fim ne ‘yan siyasa, masu kamfanoni da sauran su ke nema don neman ci gaba da tallata su, amma kuma daga ƙarshe sai a riƙa cewa ba mutanen arziƙi ba ne. Don haka ina ƙara faɗi: ɗn fim ba wulaƙantacce ba ne kamar yadda ake faɗi.
“Mu haɗa kai. Ina kuma mai bada haƙurin rashin fara taron kamar yadda aka tsara, wannan ya faru ne sakamakon wasu daga cikin manyan baƙin mu da ke kan hanya. Na gode.”

Shugaban kwamintin zaɓe, Yahuza Ilu, ya gabatar da sababbin shugabanni domin a rantsar da su. Ya ce, “Ina yi wa Al-Amin Ciroma godiya ta musamman domin duk abin da aka gani a wurin nan shi ne musabbabi.”
An kira dukkan shugabannin tare da faɗin muƙaman su, sannan Barista M.S. Abdullahi ya rantsar da su.
Daga nan kuma aka karrama wasu muhimman mutane. Abin da ya ƙara wa taron armashi shi ne karrama wasu daga cikin fitattun jarumai da su ka riga mu gidan gaskiya da aka yi.
Mamatan sun haɗa da Alhaji Yusuf Ladan, wanda ɗan sa Abubakar Yusuf Ladan da Haruna Ɗanjuma (Mutuwa Dole) su ka karɓar wa kambin karramawar, sai Ƙasimu Yero, Yusuf Barau, wanda ɗan sa Nuhu da kuma aminin sa Musa Muhammad Abdullahi su ka karɓar wa kambi; sai A’isha Musa Kaduna, wadda ‘ya’yan ta Yusuf da Amina su ka karɓar mawa, sai Hauwa Maina, wadda Saminu M. Mahmud, Musa Muhammad Abdullahi, da aminiyar ta Hajiya Rabi da ubangidan ta na farko, Salisu Umar Salinga, su ka karɓar mawa.
Jarumai masu rai da aka karrama su ne Musa Muhammad Abdullahi, A’ishatu Umar Mahuta, Maiwada Gwanki, Balaraba Ibrahim da Sani Idris Kauru (Moɗa).
A lokacin da aka kira Moɗa sai ɗakin taron ɗauki sowa da ihu don jinjina gare shi. Kafin ka ce kwabo jama’a sun zagaye shi, kuma da ma an saka wata waƙa da ya hau a cikin fim ɗin ‘Wasila’. A nan kowa sai ɗaukar sa ya ke yi da wayar sa ya na mamin waƙar. Bayan ya gama ne kuma sai aka kira tsohuwar jaruma Wasila Isma’il ta miƙa masa kyautar sa ta karramawa.
Moɗa ya ji daɗin miƙa masa kyautar da Wasila ta yi, domin a cikin jawabin sa na godiya ya ce da farko ya so a Abdul Amart ne ya miƙa masa kyautar, amma kuma da ya ga Wasila ce za ta miƙa masa sai ya ji hankalin sa ya ƙara kwanciya.
Moɗa ya bayyana cewa abin da ya sa ya ce ya so a ce Amart ne ya miƙa masa kyautar shi e ya na alfahari da shi, domin abin da ya yi masa na alheri ba zai taɓa mantawa da shi ba. Ya yi masa addu’ar samun gidan Aljanna.
Bayan karrama waɗannan jarumai an kira Yerima Shettima, shugaban Ƙungiyar Tuntuɓa ta Matasan Arewa (Arewa Youth Consultative Forum), domin ya miƙa wa Abdul Amart Maikwashewa kyautar sa. Sai dai kafin ya miƙa kyautar an ba mataimakin shugaban MOPPAN na Jihar Kaduna, Sulaiman Sha’ani, dama da ya yi magana kan gidauniyar neman taimakon kama ofishin ƙungiyar jarumai. Sha’ani ya yi jawabi tare da neman taimako a wurin Yerima da kuma Abdul Amart.
Waɗannan jajirtattun mutane sun amsa kukan, domin nan take Yerima Shettima ya ce zai bada N500,000, shi ma Abdul Amart ya kira yaron sa Abdullahi Abbas ya ce masa ya ba shi kwana biyu ya nemi ofis don a kama wa ƙungiyar, sannan kuma zai bada N500,000 tasa gudunmawar.
Kafin a miƙa wa Amart ɗin kyautar sa, ya yi magana game da yadda mutane su ka yi cincirindo a lokacin da aka kira Moɗa, ya ce, “Kafin wannan ranar waye ya je har gida ya duba Moɗa a gida, har da ni a cikin mu? Amma yanzu an kira shi kowa ya taso kamar da gaske ana ɗaukar sa a waya ya na mamin, anjima a gan shi a soshiyal midiya kowa na ɗorawa don a ce ya na wurin.
“Mu ji tsoron Allah. Duk inda na ke ni gaskiya na ke faɗi. Kuma kullum ina roƙon Allah duk inda zan je in dai ba zan faɗi gaskiya ba, kada Allah ya kai ni wurin.
“Yanzu in dai mutum ba ɗaukaka ya ke da shi ba, babu wanda ya damu da shi. Don haka sai mun gyara.”
Daga nan Yerima Shettima ya miƙa masa kyautar sa. Su na fita, taron ya watse. Al-Amin Ciroma shi ya rufe taro da addu’a.
An tashi daga taron da misalin ƙarfe 3:30 na rana.
Ban da mutanen da aka ambata a sama, wasu daga cikin mahalarta taron sun haɗa da Muhammad Jalige, Sadiq Sani Sadiq, Aminu Miror, Uwaisu Abubakar, Hamisu Jibril Goma, Yusuf Gidaje, Sadiqu Na-Manzon Allah, Abdullahi Abbas, Hadiza Maina, A’isha B. Umar, Fati S.U., Teema Yola da sauran su.
Bayan an taro ya watse, mujallar Fim ta tuntuɓi sabon shugaba, Zaharaddin Sani Owner, dangane da sabon nauyin da hau kan sa. Sai ya ce, “Alhamdu lillahi! Sai dai mu yi wa Allah godiya da wannan nauyi da Allah ya ba mu, kuma mun yi alƙawari kamar yadda mu ka yi rantsuwa za mu yi aiki tuƙuru domin mu ga mun kawo cigaba a wannan jiha tamu mai tarin albarka.”

Ganin cewa ƙungiya jarumai ita ce ƙungiyar da ta fi dukkan ƙungiyoyi tarin ƙalubale, ko akwai wani tsari da su ka yi don ganin sun kawo sauyi? Deeni ya ce, “Haƙiƙanin gaskiya, mu na da tsari na musamman da mu ka fitar wa wannan ƙungiya, duba da irin mutanen da ku ka ga sun zo wannan taron namu, irin su Kwamared Yerima Shettima, mu na so mu yi tsari mai kyau, kuma mu na so mu sako gwamnati a ciki, ya zamana cewa mu na da sakateriya, wanda ko bayan mu a ce mu ma za mu shirya zaɓen wasu sababbin ciyamomi.
“Don haka duk abin da za ka yi, ka yi shi a lokacin da ka ke da ƙwarin ka, domin mu na sa rai ko da Allah ya sa mun tsufa a ce ga wani abu da su wane ne su ka yi shi a Kaduna, in-sha Allahu.”
A game da yadda a kullum masana’antar fim ta ke samun kwararowar matasa ba bisa ƙa’ida ba, Fim ta tambaye shi idan akwai wani tsari da za su yi don ganin an daƙile wannan abu, ta yadda sai mutum ya shigo ta ingantacciyar hanya. Sai shugaban ya amsa da cewa, “Shi ya sa mu ka ce za mu yi ƙoƙari mu buɗe sakateriya don gwamnati ta shigo cikin harkar.
“Yanzu abin da za mu fara yi, za mu fara sanin yawan ‘ya’yan ƙungiyar mu, sannan mu ba su katin shaida na ƙungiya (ID card) in Allah ya yarda.
“Don haka ina yi wa kowa godiya da wannan goyon baya da mu ka samu, kuma ina kira ga dukkan ‘yan ƙungiyar mu da su zage damtse don ganin mun kawo cigaba.”
Babban baƙo na musamman a taron, wato Yerima Shettima, ya samu muƙamin uban ƙungiyar ne a lokacin da shugabannin ƙungiyar su ka kai masa ziyara a ofishin sa da ke dogon bene na ‘Bank of Industry’ da ke Titin Muhammadu Buhari Way (Waff Road) a kwanan baya, inda su ka roƙe shi da ya zama ɗaya daga cikin iyayen ƙungiyar, kuma ya amsa, tunda shi ma ya na auren ‘yar fim, wato Fati Ladan.
Shi ma mujallar Fim ta tuntuɓe shi game da wannan taro, inda ya amsa da cewa, “Taro ya yi kyau, kuma in ka duba za ka ga kusan kowa na nan. Kuma da ma albarkacin taro a ce kowa na wurin.
“Kuma abin bai tsaya a kan ‘yan industiri ɗin ba, har da wasu na waje irin mu ‘yan gwagwarmaya. Wannan kuma abu ne da za mu iya cewa cigaba ne.

“Kuma za mu ba su goyon baya kamar yadda ya kamata, mu tabbatar cewa abin da ya faru a baya bai sake faruwa ba, musamman kare haƙƙin su da wasu abubuwa da su ka fuskanta a kan aikin su da sana’ar su.”
Sababbin shugabannin dai su ne:
* Zaharaddin Sani Owner – Ciyaman
* Sabi’u M. Gidaje – Mataimakin Ciyaman na 1
* Zainab Adamu Zariya – Mataimakiyar Ciyaman ta 2
* Ibrahim Daddy – Sakatare
* Abdullahi A. Bello – Mataimakin Sakatare
* Sulaiman Ƙira – Ma’aji
* Ladidi Abdullahi Tubeless – Sakatariyar kuɗi
* Fati Yusuf Haske – Mai Binciken Kuɗi
* Isa Adam Man United – Kakaki na 1
* Faisal Munnir – Kakaki na 2
* Hafsat Abdullahi – Sakatariyar Tsare-tsare
* Zaharaddin Musa Mando – Jami’in Walwala
* Abdullahi Abbas – Mai Bada Shawara





