NAFISA Abdullahi ta saki wasu sababbin hotuna waɗanda su ka ɗau hankula a soshiyal midiya.
Jarumar ta saki hotunan ne jiya a shafin ta na Instagram inda aka gan ta kusa da motar ta, ta sha gilashi, ta na ɗaukar hotunan da salo kala-kala.
Jarumar dai a iya cewa ta yi ɓatan dabo a Kannywood. Sai dai masoyan ta na ci gaba da dakon ganin ta a nan gaba.


Kazalika, Nafisa na ci gaba da dukan hankulan masoyan ta a cikin fim ɗin nan na Arewa24 mai dogon zango, ‘Labari Na’, inda ta ke taka rawa kamar yadda aka tsara.