• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zama lafiya da mahaifiya ta ne jigon nasarar rayuwa ta – Daddy Hikima

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
June 28, 2021
in Labarai
0
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram


* Rarara ya ba shi kyautar mota


JARUMIN diramar nan mai dogon zango ta ‘A Duniya’, Adamu Abdullahi Adamu (Daddy Hikima), ya bayyana cewa zama lafiya da mahaifiyar sa ne jigon samun nasarar da ya ke yi a Kannywood.

Jarumin, wanda wasu ke kira Abale ko Ojo, ya faɗi haka ne a tattaunawar sa da mujallar Fim kan kyautar mota da fitaccen mawaƙi Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara) ya yi masa.

Ya ce, “Ni na san cewa ina tare da nasara ta a kowane lokaci saboda ina tare da mahaifiya ta, ina alfahari da ita. 

“Na san kuma in Allah ya yarda duk wani abu na rayuwa da ake yi zan iya yi, zan kuma shige haka in Allah ya yarda.”

Kazalika ya ce addu’o’in mahaifiyar tasa su ne abin da ke yi masa garkuwa a dukkan wani abu da ya saka a gaba na rayuwa. 

Rarara ya ba Daddy Hikima kyautar motar ne a jiya Lahadi, 27 ga Yuni, 2021 lokacin da kamfanin Zinariya ke karrama Rarara a ofishin sa saboda yadda ya ke bada gudunmawa ga ci-gaban masana’antar finafinan Hausa.

A yayin da ya ke bayyana farin cikin sa dangane da wannan kyauta, Daddy Hikima ya faɗa wa mujallar Fim cewa ko a mafarki bai kawo kyautar ba.

Ya labarta wa wakilin mu cewa sun haɗu da Rarara ne ta hanyar furodusa Bashir Maishadda, sakamakon yadda Rarara ya ke ƙaunar sa.

A kan yadda aka yi har Rarara ya yi masa wannan kyauta, jarumin ya ce, “Komai na Allah ne. Ba a daɗe ba a satin da ya gabata na yi hatsari a mashin ɗi na, sai ga irin wannan kyautar da ban taɓa tsammanin ta ba na samu.

“A jiya mun je taro na fim ɗin da na ke jarumi a ciki na ‘A Duniya’, za a karrama Rarara saboda an yi bikin cikar fim ɗin shekara ɗaya da fara shirya fim ɗin. 

A sama: Daddy Hikima na miƙa wa Rarara kyautar karramawa. A ƙasa kuma mawaƙin ne ke ba jarumin makullin kyautar motar da ya yi masa

“To ranar da aka yi bikin cikar fara nuna fim ɗin bayan Sallah da sati ɗaya ni ba na nan, ban samu damar zuwa ba, na je Abuja wasan Sallah, shi ma kuma Rararan wani uzuri ya hana shi halartar taron. To sai ya bada lokacin da za a zo a karrama shi. Da ya ke kuma an ware mutanen da za a karrama saboda wata gudunmawa da su ke bayarwa a masana’antar shirya finafinai ta Kannywood, ciki kuma har da shi Rarara, to sai ya bada lokaci ya ce a je jiya Lahadi, kuma a cikin jaruman da aka zaɓa waɗanda za su wakilci sauran har da ni.

“Bayan an zauna an gaisa haka, ana ta abubuwa kamar wasa ya ke ta dariya, sai ya ce ai shi akwai wani jarumin sa a cikin wannan fim na ‘A Duniya’ da ya ke so. Sai ya ce ni ne. 

“Sai kuwa aka ce masa, ‘Ai jarumin naka ba a fi sati ba ya na tafiya wani mai Adaidaita Sahu ya kaɗe shi a kan titi.’ Sai ya ce, ‘To in Allah ya yarda daga yau Adaidaita Sahu ba zai sake kaɗe shi ba, sai dai shi ya kaɗe shi.’

“To amma ni ban fahimci me ya ke cewa ba. Kwatsam, sai na ji ya ce, ‘Abale, na ba ka mota.’ Kamar a mafarki na ke ji maganar.”

Matashin jarumin ya ƙara da cewa, “A gaskiya na ji daɗi sosai matuƙa mara misaltuwa, kuma ina yi masa addu’ar fatan alkairi. Allah ya ci gaba da buɗa masa, sannan ni ma Allah ya kawo lokacin da zan ba wa waɗansu.”

Daddy Hikima ya kuma bayyana kyautar motar a matsayin wani abu da zai ƙara zaburar da shi wajen ganin ya dage da addu’o’i kamar yadda ya ke ganin soyayya a gun jama’a ta ko’ina, “ba ga maza ba, ba ga mata ba.”

Ya ce, “Yanzu zamani ya sauya, a duk inda ka shiga sai ka ga mutane su na nuna sun san ka, tsofaffi da yara kowa mararin gani na ya ke. To gaskiya hakan ya sa ni dole na ƙara zage dantse wajen gode wa Allah tare da yin addu’a.”

Tawagar masu shirya fim ɗin ‘A Duniya’ lokacin da su ka karrama Rarara a ofishin sa

Ya shawarci ‘yan’uwan sa jarumai da su maida hankali wajen riƙe sana’ar su ta fim da muhimmanci ta yadda za su amfanar da wasu da iyayen su da ma yara na ƙasa masu tasowa a duk lokacin da su ka samu ɗaukaka.

‘Yan’uwa da abokan arziki sun yi ta taya shi murna tare da yi masa addu’ar Allah ya tsare.

Rarara dai ya saba yin irin wannan kyautar lokaci zuwa lokaci ga ‘yan fim. Haka kuma ba a iya mota kyautar sa ta tsaya ba, har kuɗi da sauran abubuwa ya na ba su.

An ƙiyasta cewa Rarara ya raba aƙalla sama da mota 20 a Kannywood.

Wasu daga cikin ‘yan fim da su ka samu kyautar mota a wurin sa sun haɗa da Aminu Mai Dawayya, Tijjani Asase, Jamila Nagudu, Maryam Yahaya, Aminu S. Bono, Teema Yola, Aminu Dumbulun, Ummi Ibro, da Isah Bawa Doro.

Rarara da Daddy Hikima tare da motar da aka kyautar

Loading

Tags: Daddy HikimaDauda Kahutu Rararahausa actorsHausa singersKannywood
Previous Post

Halacci ne ya sa na auri Hassana – Sahabi na cikin ‘Kwana Casa’in’

Next Post

Ko a Aljanna ina so Muhibbat ta zama mata ta, inji Hassan Giggs

Related Posts

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry
Labarai

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry

June 15, 2025
Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
Next Post
Ko a Aljanna ina so Muhibbat ta zama mata ta, inji Hassan Giggs

Ko a Aljanna ina so Muhibbat ta zama mata ta, inji Hassan Giggs

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!