TSOHON Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Ƙasa (MOPPAN), Malam Abdulkareem Muhammad, ya bayyana cewa zai jima ya na tunanin rasuwar babban ɗan sa namiji, Khalid, wanda ya riga mu gidan gaskiya.
Khalid ya rasu ne a ranar Litinin, 23 ga Janairu, 2023 a wani asibiti da ke ƙasar Ghana.
An kai shi Ghana ɗin ne a ranar Laraba da ta gabata domin a yi masa aikin ciwon zuciya da ya yi fama da shi. Ashe tafiyar ba ta dawowa ba ce.
Tuni aka yi jana’izar sa a can kamar yadda addinin Muslumci ya tanadar.
Ɗimbin jama’a su na tururuwa gidan Alhaji Abdulkareem da ke Lamba 19B, Government Technical College Quarters, da ke unguwar Nassarawa GRA a cikin garin Kano domin yi masa ta’aziyya.
Mujallar Fim ta ziyarci gidan domin yi wa Abdulkareem ta’aziyya tare da neman ƙarin bayani game da wannan babban rashi da ya yi.
Cikin yanayi na jimami, Malam Abdulkareem ya ce: “To, alhamdu lillahi, ita rayuwa ta Khalid ta kasance ‘yar gajeriyar rayuwa da ya tafi ya bar mu cikin alhini da kuma godiyar Allah. Don haka mu na godiya ga Allah da ya ba mu da irin sa a cikin irin wannan yanayi a cikin wannan zamani wanda ya ke harka ta tarbiyya a gaskiya ba ƙaramin aiki ba ne, saboda kuwa yanayin rayuwa ya lalace wanda kuma ya shafi tarbiyyar ‘ya’ya.
“To a cikin irin wannan yanayi har Allah ya albarkace mu da yaro kamar Khalid. To sai dai mu yi wa Allah godiya. Kuma da ya ɗauke mana shi duka dai a cikin godiyar mu ke, don ɗan gajeren lokaci da ya kasance a gare mu gaskiya mun ji daɗin wannan ɗan gajeren lokacin da Allah ya ara mana na kasancewa tare da shi.
“Saboda ‘ya’ya na takwas ne, amma Khalid shi ne na huɗu, wanda kuma mata ne a gaba da shi, sai mace ɗaya da kuma maza uku da ke kasa da shi.
“Kuma an haife shi a ranar 7 ga Satumba a 1991 kuma Allah ya albarkace shi da mata guda ɗaya da kuma ‘yar sa ɗaya.”
Da mu ka tambaye shi irin rashin lafiyar marigayin kuwa, cewa ya yi: “To, shi dai Khalid tun ya na shekaru takwas sai Allah ya jarrabe shi da ciwon hauhawar jini kuma mu ke ta faman zuwa asibitoci ta dama, ake ta gwaje-gwaje daban-daban da ba a iya samun nasarar lafiyar sa ba. Haka dai abu ya tafi har ya kai ga ya ci gaba da ruruwa da wannan cuta a jikin sa. Amma kuma daga baya sai aka gano duk wata zuciya ta jikin ɗan’adam ta na da wata ƙofa guda biyu wadda ta ke sarrafa jini, to shi kuma Allah ya halicce shi da guda ɗaya, don haka da aka gano sai aka ga akwai buƙatar a saka masa bututu guda ɗaya yadda zai kasance ya na da guda biyu kamar yadda kowane ɗan’adam ya ke da shi, kuma kafin a kai ga hakan sai Allah ya karɓi ran sa.”
A game da yadda ya samu labarin rasuwar kuwa, cewa ya yi: “To da man ya ɗan kwanta a nan Asibitin Malam Aminu Kano, ya yi wajen kwana goma a kwance. To daga nan ne aka samo mana wani asibitin a ƙasar Ghana inda kuma aka tsara tafiyar da masu jinya na musamman kuma Allah ya sa sun isa lafiya. To kuma bayan kwana biyar da kwanciyar sa a can asibitin sai Allah ya yi masa cikawa.”
Ko me Abdulkareem Muhammad zai fi tunawa da shi a game da rayuwar Khalid? Amsa: “To a gaskiya zan fi tunawa da shi, yaro ne wanda ya ke da biyayya, kuma idan ya sa abu a gaban sa ya na son ya yi, to ya kan nace don ya ga ya cimma nasara, don haka duk abin da ya sa a gaban sa, to ya na so ya ga ya yi fice.
“Kuma ya na da ɗaukar nauyi, saboda harka ta iyali za ka ga ya na ɗauka daidai gwargwado.
“Sannan kuma idan alƙawari ne, ya kan yi ƙoƙarin ya ga ya cika.
Sannan kuma harkar mu’amala da mutane, ya na da kyakkyawar dangantaka da jama’a, domin mu na ganin jama’a da su ka zo mana ta’aziyya kowa ya na faɗar hakan.
“Don haka ina kira ga matasa da su yi koyi da irin wannan kyakkyawar rayuwa irin ta Khalid da Allah ya karɓi ran sa don shi tasa ta ƙare. Mu na fatan ayyukan sa masu kyau su bi shi, mu kuma mu na fatan Allah ya kyautata namu ƙarshen, ya yi mana gafara da mu da shi duka.”