FITACCEN furodusa Abdul Amart (Maikwashewa) ya ƙudiri aniyar kawo sauyi ga yadda ake shirya finafinan Hausa da sabon fim ɗin sa mai suna ‘Manyan Mata’.
Ya ce yanzu zai fi maida hankali ne ga inganci maimakon neman kuɗi da fim ɗin soyayya.
Amart ya faɗi haka ne a hirar sa da mujallar Fim a wajen bikin karrama zakarun wata gasa da ya saka a kan fim ɗin nasa a Kaduna jiya.
Amart, wanda shi ne shugaban shahararren kamfanin shirya finafinai ɗin nan mai suna Abnur Entertainment, ya saki sanarwar fara gasar sabon fim ɗin nasa tun a ranar Litinin, 15 ga Yuni, 2020.
Ya shirya gasar a shafin sa na Instagram, inda ya tsara tambayoyi masu tsauri waɗanda ake tunanin in ba na kusa da shi ba babu wanda zai iya amsa su.
A ranar 5 ga Yuli, Abdul Amart ya bayyana sunayen waɗanda su ka lashe gasar daga na 1 zuwa na 20 da kuma ranar da za a raba kyaututtukan ga zakarun.
An yi bikin a jiya Lahadi, 12 ga Yuli a gidan cin abinci na Rahama Sadau, wato Sadauz Home, wanda ke lamba 27, Titin Raɓah a Kaduna.
An fara taron da misalin ƙarfe 6:30 na yamma lokacin da mawaƙi El-Mu’az Birniwa ya gabatar da addu’a.
Daga nan sai mai gabatarwa, Tahir I. Tahir, ya kira Amart ya yi wa baƙi maraba tare da bayani game da abin da ya tara mutane a wurin.
Daga nan aka raba abinci da abin sha, kowa ya ci ya hantse.
Abu na gaba shi ne raba kyaututtuka ga zakaru.
Wani matashi, Abubakar Abdulƙadir Hassan, shi ne ya zo na ɗaya, inda ya samu kyautar komfuta laptop da turare biyu da N5,000.
Ta biyu, Farida Marafa, ta samu kyautar waya ƙirar Tecno Spark 4 da yadi material biyu da turare biyu da N5,000.
Ta uku, Habiba Abdullahi, ta samu shadda Gezner da turare biyu da N5,000.
An ba Khalil Yusuf ATA, wanda ya zo na huɗu, kyautar shadda Gezner da turare biyu da N5,000, yayin da Fatima Yusuf, ta biyar, ta samu atamfa Superwax da turare biyu da N5,000.
An ce sauran zakarun, daga na 6 zuwa na 20, za a aika masu da kyautar su har inda su ke.
Bayan an gama bada kyaututtukan, sai aka kira Abu Sarki ya rufe taron da addu’a.
Wasu daga cikin matan da za su taka rawa a wannan fim na ‘Manyan Mata’ sun halarci wurin bikin, wato Hadiza Gabon, Fati Washa da A’isha Tsamiya.
Mahalarta bikin kuma akwai Adam A. Zango, Tahir I. Tahir, Sadiq Mafia, Jamilu Adamu Kochila, El-Mu’az Birniwa, Abdullahi Abbas, Falalu Ɗorayi, Abu Sarki, Yusuf Lazio, Wassh Waziri Hong, Shehu Jaha, Fati Shu’uma, Isah Bawa Doro, Aƙilu Mohammed (Baban Mulika) da Maryam Aliyu (Madam Korede).
An tashi daga taron da misalin ƙarfe 8:30 na dare.

Bayan kammala bikin ne mujallar Fim ta zanta da mai gayya, mai aiki, wato Abdul Amart, game da gasar da kuma fim ɗin. Da wakilin mu ya tambaye shi abin da ya ja hankalin sa har ya shirya wannan gasa, sai ya amsa da cewa: “Gaskiya abin da ya ja hankali na har na shirya wannan gasa shi ne, fim ɗin wani abu ne daban wanda na ke ganin a ‘career’ na idan na yi shi na bada gudunmawa ga al’umma sosai.
Shi ya sa na ga me zan fara yi in ja hankalin mutane su san fim ɗin, su san kuma me za a yi. Sai na ce bari in fara da shirya gasa.
“Da mu ka shirya kuma, Allah cikin ikon sa abin ya karɓu, kuma mu ma mu ka cika alƙawari mu ka zo mu ka ba mutane kyaututtukan su.”
Ko me fim ɗin ya ƙunsa? Amart ya ce, “Fim ɗin ya ƙunshi abubuwa da yawa. Mu na so mu jawo hankalin mutane daga barin shaye-shaye, barace-barace, fyaɗe, wanda a yanzu ya zama ruwan dare, da bauta irin wadda ake sa mata a gidajen aure, sannan za mu ƙara nuna muhimmancin karatun ‘ya mace.”
Duk wanda ya ga fostar fim ɗin, zai ga mata ne kawai a ciki. Shin babu maza a cikin fim ɗin? Sai Abdul Amart ya ce, “A’a, ba mata kaɗai ba ne a cikin fim ɗin, akwai maza. Akwai Ali Nuhu, Adam A. Zango, Sadiq Sani Sadiq, Rabi’u Rikadawa, Abdul M. Shariff, Tijjani Faraga da sauran su.”
Da mujallar Fim ta tambayi babban furodusan hanyar da ya bi ya yi alƙalancin wannan gasa, sai ya ce, “Tsakani da Allah, da mu ka ga mutane sun yi yawa a gasar, sai na ɗauko wasu ƙwararru na aje su na kwana uku. Sun ba ni tsari, su ka ce mani bai kamata a ce idan mutum bai amsa duka tambayoyin ba a ce ya faɗi. Abin da ya kamata mu yi shi ne, mu yi amfani da ‘point’, daga nan ne mu ka samu waɗanda su ka fi yawan ‘point’.
“Da su ka gama su ka kawo mani sakamako, na duba, kuma na yarda da aikin da su ka yi.”
Ko ta ina Amart zai fitar da kuɗin sa bayan fim ɗin ya fito, ganin cewa kasuwar finafinai ta mutu? Sai ya yi dariya, sannan ya bada amsa kamar haka: “A gaskiya mun yi bincike, ana sayen finafinai. Fim ba ƙaramin abu ba ne, yanzu an wuce kasuwar sidi; akwai Netflix, su na sayen fim. Akwai Amazon.
“Abu mafi sauƙi, yanzu ka fara ‘target’ ɗin yadda ake finafinan Kudu ake saya, kai ma sai ka zo ka yi ka kai. Akwai gidajen talabijin, akwai waya, ya koma ‘on demand’ yanzu, akwai intanet. To duk ta waɗannan za mu maida kuɗin mu.
“Sannan akwai tallulluka da mu ka rubuta wa kamfanoni su ba mu. Ka ga ta nan ma za mu maida kuɗaɗen mu.”
Da mu ka tambayi Amart saƙon sa ga ‘yan’uwan sa furodusoshi, sai ya ce, “Gaskiya mu juya tunanin mu, mu rinƙa ɗauko abubuwan da ke faruwa ga al’umma mu na yin fim a kai, ba wai neman kuɗi kawai ba. Ka ga ta nan za mu taimaka wa ƙasa da al’ummar mu.
“Ya zama dole sai mun rinƙa sauya labaran mu daga salon soyayya zuwa ‘social issues’, mun riƙa wayar da kan al’umma. Kuma shi zai fi kawo mana kuɗi a kan irin wanda mu ke yi na soyayya.”
Fitaccen furodusan ya kuma faɗa wa mujallar Fim cewa za su fara ɗaukar wannan fim a ranar Juma’a, 7 ga Agusta, 2020, kuma su na sa ran zuwa Nuwamba ko Disamba 2020 fim ɗin zai fito.
