WATA kotun shari’ar Musulunci da ke unguwar Hausawa a Kano ta aika wa da jarumi Haruna Yusuf (Baban Chinedu) da sammaci sakamakon ƙarar da shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Malam Isma’il Na’abba (Afakallah), ya kai shi bisa zargin ƙazafi da ɓata suna.
Afakallah ya yi ƙarar sa ne saboda maganar da ɗan wasan ya yi a Facebook inda ya zarge shi da cinye kuɗin marayun marigayi Rabilu Musa (Ibro) da ya ce gwamnatin Jihar Kano ta bayar.

Bayan da kotun ta saurari ƙorafi daga ɓangaren mai ƙara, sai ta saka ranar Laraba, 1 ga Afrilu, 2020 domin fara sauraren shari’ar.
A yau Alhamis, 19 ga Maris, 2020 kotun ta aika wa da Baban Chinedu da takardar sammaci a ofishin sa da ke Kano.
Idan ba ku manta ba, a ranar 17 ga Fabrairu, 2020 mujallar Fim ta ba ku labarin taƙaddamar da ta ɓarƙe tsakanin jarumin barkwancin kuma mawaƙi da Afakallahu, inda shi Baban Chinedu ya ce Afakallahu ya yi rub-da-ciki kan kuɗin marayun.
Ya ce gwamnatin jihar ta bada kuɗin ne ta hanyar shugaban hukumar domin a saya wa ɗiyar Ibro kayan ɗaki lokacin auren ta amma bai kai kuɗin ba.
Tun a lokacin Afakallahu ya maka shi a kotu ya na neman Baban Chinedu da ya janye kalaman sa sannan ya ba shi haƙuri, to amma Baban Chinedun ya yi biris da maganar.