• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, July 18, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ƙungiyar Mawaƙa Mata na Kannywood taron macuta ne, ba inda za ta je – Fa’iza Badawa

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
April 5, 2023
in Labarai
0
Hajiya Fa'iza Badawa: "Ƙungiya ta ce"

Hajiya Fa'iza Badawa: "Ƙungiya ta ce"

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

AN bayyana sabuwar Ƙungiyar Mawaƙa Mata na Kannywood da cewa wani gungun ne na mutanen da ba su da wata manufa sai son zuciya da son kan su, don haka babu inda za su je.

Ɗaya daga cikin sanannun mawaƙa mata, Fa’iza Badawa, ita ce ta bayyana hakan a lokacin tattaunawar ta da mujallar Fim dangane da ƙungiyar.

Idan kun tuna, a shekaranjiya Litinin mujallar Fim ta ba ku labarin kafa ƙungiyar, inda har mu ka yi hira da shahararriyar mawaƙiya Maryam A. Baba kan manufofin kafa ƙungiyar.

A raddin da ta yi, Hajiya Fa’iza ta ce: “Tun asali ma ba su su ka kafa ƙungiyar ba, ni na kafa ta. Don in za ka iya tunawa a wata hira da mujallar Fim ta yi da ni a baya, na faɗa maka na kafa sabuwar ƙungiya kuma ina jawo mawaƙa domin mu taru mu haɗa kai domin mu taimaki juna.”

Ta ƙara da cewa: “Da na kafa ƙungiyar, sai na kirawo su a waya na ce na kafa ƙungiya. To, bayan mun zo an zauna za a kafa ƙungiya, sai na ce to ya na da kyau a raba muƙamai kafin a gama shirye-shirye. Da su ka amince sai na ce to ina son a bai wa Murja Baba shugaba, don haka sai mu ka samar da shugabanci kafin a kammala tsarin da za a yi. 

“To, bayan mun yi haka sai mu ka samu aiki a Gombe wanda mu ka yi wa Gwamnan Gombe. Tun da aka je aka samo kuɗi naira miliyan tara, tun daga nan sai su ka fara canzawa. Domin da aka samo kuɗin ya kamata a zo Kano a zauna da ni da na kafa ƙungiya da sauran ‘yan cikin ta, a zo a san yadda za a raba kuɗi a fitar da kuɗin aikin da aka yi. To tun daga can sai su ka raba kuɗi. 

“Ni ban je Gombe ba, amma a can su ka fara raba kuɗi a junan su, su ba wanda su ka ga ya dace, su hana wanda su ka ga bai dace ba. 

“Sannan sai su ka rinƙa bai wa ƙananan mawaƙa kuɗi kaɗan, kuma wannan bai kamata ba tun mawaƙiya ta na ƙarama ki ba ta kuɗi kaɗan, saboda ai tare ku ka je, amma ya za a yi ki ɗauki kuɗin da ya linka nata sau uku? Wannan bai kamata ba in dai taimakon juna za a yi, sai a zo a yi waɗanda su ka yi waƙa kuɗin su daban, waɗanda ba su yi waƙa ba kuɗin su daban. 

“Amma sai su ka ɗauka hakan ba zai yiwu ba saboda su manya ne. 

“Sannan duk wanda ya bi ta hanyar su aka tafi da shi, sai sun linka masa kuɗi. Kuma ba haka ake yin rayuwa ba. In dai ka ce ka na son ka kafa mutum da ya zama mutum, to ba za ka kafa ƙungiya don ka cuce shi ba. Ya za ka kafa ƙungiya don ka tallafa wa na ƙasa sannan ka zo ka na cutar sa ka na danne masa haƙƙi? Ai ba a yin haka a rayuwa.

“Shi ya sa na faɗa maka, ƙungiyar babu inda za ta je, in dai da zalunci a cikin ta. Don ka ga ni na kafa ƙungiya, kuma kowacce mawaƙiya ni na kira ta na ce ta zo a haɗu a kafa ƙungiya. Don haka ƙungiya ta ce, kuma na fita.

“Don haka babu inda za ta je. Tunda akwai zalunci a cikin ta sai ta rushe wallahi.”

Loading

Tags: Fa'iza BadawaƙungiyaMaryam A. Baba (Sangandale)matan KannywoodmawaƙaMurja Babazabiyazabiyoyi
Previous Post

Mawaƙi a Kannywood, El-Bash Muhammad ya zama baban tagwaye

Next Post

Zaɓen 2023: Abin da ya sa MOPPAN ta ke nema wa waɗanda aka ƙona wa kaya tallafi – Gidan Dabino

Related Posts

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu
Labarai

Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu

July 7, 2025
MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 
Labarai

MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 

June 29, 2025
Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta
Labarai

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta

June 23, 2025
Next Post
Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON

Zaɓen 2023: Abin da ya sa MOPPAN ta ke nema wa waɗanda aka ƙona wa kaya tallafi - Gidan Dabino

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!