DAGA MUKHTAR YAKUBU
A KWANAN baya ne aka samu bayyanar wata ƙungiyar mawaƙa mai suna Murya Ɗaya a ƙarƙashin shugabancin Ali Isah Jita tare da sauran mawaƙa waɗanda da damar su ‘yan ƙungiyar 13×13 ne wadda mawaƙi Dauda Kahutu Rarara ya ke jagoranta.
To sai dai duk da kamanceceniyar da ƙungiyar ta ke da ita da 13+13 da kuma muryar a wajen gudanar da ayyukan jinƙai, ita wannan ƙungiyar ta shigo da wani tsari na bin tsangayu na makarantun allo su na raba gidan sauro, sabulu, man shafawa da kuma yi wa almajirai aski.
Wakilin mujallar Fim ya halarci Tsangayar Malam Nafi’u da ke unguwar Gwauron Dutse a Kano lokacin da ƙungiyar ta ke raba kayan tallafin da kuma yi wa almajiran aski.
Bayan kammala rabon kayan, mun nemi jin ta bakin shugaban ƙungiyar, wato Alhaji Ali Jita, kan manufar ƙungiyar da dalilin kafa ta.
Sai ya ce, “A yanzu da ka gan mu a nan mun zo ne mu gudanar da ɗaya daga cikin aikin wannan ƙungiyar, domin ita ƙungiyar ta Murya Ɗaya manufar ta shi ne mu ga ta yaya za mu sauƙaƙa wa gwamnati ayyuka, ta yaya kuma za mu tallafa wa al’ummar mu ta kowace hanya ce.
“Kamar yadda ka gan mu a wannan tsangaya, to tsangaya ce ta biyu da mu ka zo a yau da mu ka zo don raba masu abubuwa kamar su gidan sauro, sabulu, man shafawa, abinci, bargo da kuma yi wa almajirai aski domin su samu sauƙi, su ma su san cewa akwai waɗanda su ka damu da su.
“Kuma kamar yadda na faɗa maka, wannan ƙungiyar ta sa gaba ne a kan abubuwa guda uku. Za mu kai kayan tallafi zuwa tsangayoyi guda ɗari a cikin wannan shekarar, sannan za mu kai tallafi makarantun firamare da sakandare na mata da na maza, su ma guda ɗari.
“Za mu kai ziyara zuwa gidan ajiya da gyaran hali su ma mu raba masu kayan tallafin a kowace jiha da ke Arewa. Sannan za mu je asibitoci su ma mu ga ta yaya za mu tallafa masu a iya abin da Allah ya hore mana na arziki mu ke gudanar da wannan aikin da kuma taimakon wata gidauniya mai suna ‘NHD Foundation’, su ma sun tallafa mana domin gabatar da waɗannan ayyuka.”
Dangane da yadda aka samar da wannan ƙungiyar da lokacin da ta fara aiki kuwa, Ali Jita ya ce, “To kamar yadda na faɗa maka, ni na ke shugabancin ƙungiyar, kuma akwai mawaƙan mu a ciki da yawa masu basira, kuma mun ƙirƙiro ta ne tun kafin a yi zaɓe. To amma saboda yanayin siyasa ne ya sa ba ta yi tasiri ba sai a yanzu da aka gama zaɓe mu ka zo mu ka haɗa kan mu mu zo mu ga yadda za mu taimaka wa kan mu, kuma mu taimaki al’ummar mu.
“To ita wannan ƙungiya ta daɗe, amma manufofin ta su ne taimakon al’umma waɗanda su ke cikin mu da ba su da ƙarfi ko da a cikin mu ne mawaƙan, mu ga yadda za mu taimaka wa waɗanda ba su da ƙarfi. Sannan mu duba yadda za mu rage wa gwamnati aikin jinƙai ga jama’a.
“Wannan ya sa har wata rana mu kan fita mu yi sharar titi. To duk waɗannan su ne ayyukan da su ke cikin manufar ƙungiyar mu.”

Mujallar Fim ta tambaye shi yadda kusan dukkan su ‘yan ƙungiyar 13+13, ne don haka ake ganin sun ɓalle ne daga can su ka kafa sabuwar tafiya.
Sai ya ce, “To, ita 13+13 dai ƙungiya ce ta siyasa, wannan kuma ba ta siyasa ba ce. Don ka ga a yanzu an gama siyasa babu wani da za ka je ka yi masa yaƙin neman zaɓe ko ka yi masa waƙar siyasa, don haka ƙungiya ce kawai ta mawaƙan Hausa kamar yadda ka gani. Ta mawaƙa ce da manazarta da masu basira da su ka haɗu domin su taimaki juna kuma su taimaki jama’a.
“Don haka mu na fatan mu ga mutane sun kyautata mana zato sannan su ba mu haɗin kai wajen tallafa wa ƙungiyar, domin mu ci gaba da irin waɗannan ayyuka na alheri da mu ka sa a gaba.
“Sannan ina fatan abin zai ɗore, bayan wannan ma mu ci gaba da yin ayyuka masu yawa yadda za mu daɗe mu na yi.
“Kuma ina yi wa kowa fatan alheri, kuma mu na buƙatar addu’ar kowa. Jama’a su yi mana fatan alheri, maza da mata, Allah ya haɗa kan mu ya ba mu zaman lafiya a ƙasar mu, musamman a kan yanayin rashin tsaro da mu ke ciki.”