• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ɗaliban Hausa ‘yan ƙasar Sin sun ziyarci mawaƙi Aminu Ala

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
December 3, 2023
in Mawaƙa
0
Ɗaliban Hausa ‘yan ƙasar Sin sun ziyarci mawaƙi Aminu Ala

Aminu Ala (a tsakiya) tare da ɗalibai 'yan Chaina da malamin su

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

WASU ɗalibai masu nazarin harshen Hausa a Jami’ar Bayero, Kano, ‘yan asalin ƙasar Sin (Chaina), sun kai ziyara ga mawaƙi Aminu Ladan Abubakar (Ala) a ofishin sa da ke Titin Gidan Zu a Kano.

Sun kai ziyarar a ranar Juma’a, 1 ga Disamba, 2023 bisa jagorancin ɗaya daga cikin malaman su, Malam Kamilu Ɗahiru Gwammaja.

A jawabin sa a taron, Malam Kamilu ya faɗi dalilin su na kai ziyarar, ya ce, “Waɗannan ɗaliban mu ne a Jami’ar Bayero da su ka zo daga Jami’ar Beijing da kuma Jami’ar Tenjan daga ƙasar Sin inda su ke nazari a kan harshen Hausa, mu ka zo da su domin su ga Aminu Ala shi ma ya gan su a matsayin sa na mawaƙin Hausa da su ke da sha’awar haɗuwa da shi.”

Malam Kamilu na yin jawabi kan maƙasudin ziyarar

Ya ƙara da cewa, “Babbar manufar wannan ziyara ita ce haɗuwa tare da ji daga shi Aminu Ala na abin da ya shafi tarihin rayuwar sa da yadda ya ke waƙoƙin sa da kuma irin nau’in mutanen da ya ke yi wa waƙa.

“Don haka Aminu Ala ina gabatar maka da baƙin ka da su ka zo domin su ziyarce ka a matsayin ka na mawaƙin da su ke son haɗuwa da shi.”

Bayan ya kammala gabatarwar, kowanne daga cikin ɗaliban ya tashi ya gabatar da kan sa da kuma sunan sa, tare da jin daɗin sa na haɗuwa da shahararren mawaƙin.

Ala na yi wa baƙin marhabin

A cewar su, su na sauraron waƙar Ala a ƙasar Sin a matsayin su na masu nazarin Hausa, kuma waƙoƙin sa su na ƙayatar da su.

A lokacin da ya ke yi masu bayani, Ala ya nuna farin cikin sa da zuwan su tare da yi masu bayani a taƙaice kan tarihin sa da yadda ya ke gudanar da waƙoƙin sa, tun farkon fara waƙar sa zuwa yanzu.

Ala tare da maziyartan sa

Baƙin sun nuna gamsuwa da farin ciki kan yadda aka karrama su, su ka yi fatan zumuncin su zai ɗore tare da fatan za a sake karɓar su da hannu biyu-biyu a duk lokacin da su ka samu damar dawowa.

Aminu Ala da ɗaliban ‘yan ƙasar Sin

Loading

Previous Post

Taron marubutan Arewa ya fito da kyawawan halayen marigayi Sheikh Yusuf Ali

Next Post

Taron COP28: Su Tinubu da sauran tawagar Nijeriya ba sharholiya ce ta kai su Dubai ba, inji Idris

Related Posts

Za a yi bikin naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa a Daura ranar Asabar
Mawaƙa

Za a yi bikin naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa a Daura ranar Asabar

December 11, 2025
Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi
Mawaƙa

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi

April 19, 2025
Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala

October 28, 2024
Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala

July 16, 2024
Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara
Mawaƙa

Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara

May 13, 2024
Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 
Mawaƙa

Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 

December 7, 2023
Next Post
Taron COP28: Su Tinubu da sauran tawagar Nijeriya ba sharholiya ce ta kai su Dubai ba, inji Idris

Taron COP28: Su Tinubu da sauran tawagar Nijeriya ba sharholiya ce ta kai su Dubai ba, inji Idris

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!