INA kira ga ɗaukacin ‘yan ƙasar nan, a kowane sashi su ke, su yi rijista saboda ƙalubalen da ke tattare da zaɓe mai zuwa. Ga dalilai na guda uku na yin wanna kira.
1. Ambaliya
Sakamakon zaɓen fidda gwani na ‘yan takarar shugaban ƙasa ya kawo ambaliyar masu rijistar jefa ƙuri’a, musamman a ƙasar Inyamurai da ta Yarbawa. Dafifin mutanen ba ƙarami ba ne, don ya sa har hukumar zaɓe (INEC) ta ƙara na’urorin rijista a jihohi biyar a ƙasar Inyamurai, da Jihar Legas da Jihar Kano. 5-1-1. Me wannan lissafin ya nuna maka?
Kuma me ya jawo wannan dafifi? Ina ga ba zai rasa nasaba da ƙoƙarin da kowane sashi ya ke yi ba ne don ya taimaka wa nasa ɗan takarar da ƙuri’u don idan kowanne zai sa ɗaukacin masu jefa ƙuri’a a sashin sa su fito, ba shakka likkafar sa za ta ja gaba.
A nan, ‘yan Arewa su na da matsalar ko-oho ganin cewa su na da yawa. Ina ga wannan babban kusukure ne. Jefa ƙuri’a a yau ya zama wajibi ga duk wanda ya ke son ya ga an samu cigaba a kan abin da ya dame shi. Yau mu na cikin tasku na rashin zaman lafiya. Ya kamata a ce mun fi kowa damuwa da waye zai zama shugaban ƙasa saboda shi ne zai shugabanci hukumomin tsaro gaba ɗaya. Idan wani zai yi amfani da su ya taimake mu, wani zai iya amfani da su ya cutar da mu.
In mun yi shakulatin ɓangaro da zaɓe mai zuwa, ya na yiwuwa abubuwa su ƙara taɓarɓarewa har inda fitinar ba ta kai ba yau ta kai gobe, ko a ɓullo da wasu sabbin fitinun. Su ma sauran sassan ƙasar su na da abubuwan da ke damun su kuma a kan haka za su jefa ƙuri’a. To me zai sa ba za mu himmatu ba kamar yadda su ke nuna himma a kwanakin nan?
2. Tuwon Gobe
Na yarda akwai mutane da yawa da rashin kyan mulkin Buhari ya kashe wa gwiwa. Ga mai hankali, wannan shi ne ma zai sa a ƙara himma, a gwada wani, wataƙila a yi dace; ana zaton wuta a maƙera, a same ta a masaƙa. Ala ayyi halin, mu ‘yan ƙasa mu yi namu. Mu zaɓa. Idan waɗanda mu ka zaɓan su ka ci amanar mu ko su ka gaza, sai mu bar su da Allah. Rashin daɗin tuwon yau ba shi zai hana mu cin na gobe ba.
3. Ingancin Zaɓe
Bugu da ƙari, yau ƙuri’a ta na da muhimmanci ba kamar a baya ba don an ci ƙarfin maguɗi a lokacin zaɓe. Wannan cigaba ya samu ne don rijistar masu jefa ƙuri’a da aka samar tun zamanin marigayi Yar’Adua (Allah ya yi masa rahama), da amfani da fasahohin zamani na tantance masu jefa ƙuri’a, da aikawa da sakamako daga mazaɓu kai-tsaye zuwa rumbun bayanai na INEC, da kuma uwa-uba dokoki daban-daban da ke cikin dokokin zaɓe da aka kafa tun 2011.
Yau idan mutum ya jefa ƙuri’a akwai tabbaci mai rinjaye cewa za a ƙirga ta a yawan ƙuri’un ɗan takarar da ya jefa wa. Me ya fi haka daɗi? Ba a gama saita komai da komai ba, amma dai an ci ƙarfin maguɗi. Wanda aka tafka a shekarun baya ba za a sake iya yin sa ba yanzu. Don haka waɗanda da su ke cewa ƙuri’ar su ba ta da amfani ya kamata su bar wannan turbar, su fara yin zaɓe.
Sakiyar Da Ba Ruwa
Don waɗannan dalilai, ina kira ga kowa ya tsaya kan waɗanda ya ke da iko a kan su ko waɗanda su ke jin maganar sa ya tabbatar da kowannen su ya yi rijista. Kuma idan lokacin zaɓe ya zo kowa ya jefa ƙuri’ar sa ga wanda ya fi zaton zai fi alheri da kawo cigaba a ƙasa.
Wannan saƙo ne mai muhimmanci. Don Allah a kula.
* Dakta Aliyu U. Tilde shi ne Kwamishinan Ilimi na Jihar Bauchi