HAIRAT Abdullahi ta na ɗaya daga cikin mawaƙa mata da su ke haskawa a harkar waƙa yanzu. TAa na da nasibi sosai, domin kuwa tun daga lokacin da aka fara jin muryar ta a waƙoƙi, musamman na ogan ta Umar M. Shareef, ba a daɗe ba ta samu karɓuwa. Hairat ta na ƙarƙashin kamfanin fitaccen mawaƙi Umar M. Shareef ne.
Hairat, wacce wasu su ke kiran ta da ‘yar Indiya, mawaƙiya ce mai ladabi da biyayya ga girmama na gaba da ita. Wakilin mujallar Fim ya zanta da mawaƙiyar inda ta yi masa bayani kan yadda ta fara waƙa, nasarorin ta, waƙoƙin da ta yi da sauran abubuwa a game da ita.
FIM: Ki faɗa wa masu karatu tarihin rayuwar ki a taƙaice.
HAIRAT ABDULLAHI: Suna na Hairat Abdullahi. An haife ni a garin Kaduna. Na yi firamare da sakandare duk a garin Kaduna, sannan na yi makarantar koyon aikin asibiti a Kaduna.
FIM: Ke wace yare ce?
HAIRAT: Ni yaren Eggon ce daga Jihar Nassarawa. Mama na da baba na duk ‘yan Jihar Nassarawa ne.
FIM: Kin taɓa waƙa da yaren ki?
HAIRAT: Ban taɓa yi ba, gaskiya, domin yaren ma ba na ji sosai don mu a Kaduna aka haife mu. Amma dai ina taƙama da yare na da kuma jiha ta.
FIM: Yaushe ki ka fara waƙa?
HAIRAT: Na fara waƙa a shekarar 2013.
FIM: Ya aka yi ki ka fara waƙa?
HAIRAT: Gaskiya koya na yi, kafin har na iya. Kuma ni na fara waƙa ne da yardar iyaye na. Ga shi kuma cikin yardar Allah ina ta samun nasara.
FIM: Wace waƙa ki ka fara yi?
HAIRAT: Gaskiya ba zan iya tuna wace waƙa na fara yi ba saboda a lokacin ina koyon waƙa. Amma zan iya tuna waƙa ta ta farko da oga na, Umar M. Shareef, wata waƙa ‘Ƙaddara Ko Fansa’.

FIM: Ya maganar karatun koyon aikin asibiti da ki ka yi? Ki na aikin asibitin ko kuma waƙar ki ka sa a gaba?
HAIRAT: Gaskiya waƙar na sa a gaba. Amma dai duk abin da na koya su na kai na.
FIM: Ki na ganin nan gaba za ki bar waƙa ki koma aikin asibiti?
HAIRAT: E, nan gaba ina fatan haka, nan gaba idan na yi aure. Saboda wannan aikin ya na son natsuwa ne wuri ɗaya. Mu kuma waƙa idan abu wani abu ya taso na aiki dole za mu bar garin da mu ke, mu je nan mu je can.
FIM: Mecece dangantakar ki da Umar M. Shareef da Abdul D. One?
HAIRAT: Gaskiya dangantaka ce mai ƙarfi. Umar M. Shareef dai shi ne oga, wanda kowa ya san da shi. D. One shi ma abokin aiki na ne, wanda shi ma a ƙarƙashin Umar M. Shareef ya ke. Kuma duk ina ba su girma daidai gwargwado. Sannan akwai su Muhammad Mai Leri da Umar MB.
FIM: Waɗanne matsaloli ki ka fuskanta a harkar waƙa?
HAIRAT: Ko wace irin sana’a za ka yi dole za ka ga fari, za ka ga baƙi; akwai ɓacin rai, akwai daɗi, akwai ɗaci. A haka idan mutum ya na haƙuri zai ga komai ya wuce.
FIM: Waɗanne irin wurare ne harkar waƙa ta kai ki?
HAIRAT: Na je wurare da dama. Amma ban dai riga da na tsallake ƙasa ba, gaskiya.
FIM: Ki faɗa wa masu karatu wasu daga cikin waƙoƙin ki.
HAIRAT: Akwai ‘Abin Da Ya Ke Rai Na’ na cikin fim ɗin ‘Mansoor’, akwai ‘Rariya’, ‘Dace’, ‘Ruwan Dare’, ‘Aminta Da Juna’ ‘Gwaska Return’ da sauran su. Gaskiya waƙoƙin na da yawa, ba zan iya lissafo su ba. Kuma magana ta gaskiya, ban san adadin waƙoƙin da na yi ba a duniya.
FIM: Ko kin gamsu da yadda harkar waƙa ta ke a Kaduna?
HAIRAT: Gaskiya na gamsu sosai, ta kowane ɓangare.
FIM: Ana ƙorafin cewa mawaƙa mata da ke Kaduna ba su fita waje waƙa. Mecece gaskiyar wannan maganar?
HAIRAT: Gaskiya ni dai ina shiga Kano, ina waƙoƙi da mawaƙan Kano. Ina waƙa da irin su Adamu Hassan Nagudu.
FIM: Menene bambancin mawaƙan Kano da na Kaduna?
HAIRAT: Gaskiya ba zan ce ga bambancin su ba, duk da dai mawaƙi, mawaƙi ne. Duk mawaƙan garuruwan nan ana tare, duk abin da ya tashi na mawaƙa, za ka ga kai a haɗe ana ƙoƙarin a yi komai cikin natsuwa da kwanciyar hankali.
FIM: Kin taɓa tunanin fitar da kundin waƙoƙi, wato album?
HAIRAT: Gaskiya a halin da ake ciki, yanzu haka na fara ƙoƙarin aiki yin bidiyo na waƙoƙi na da kuma na saurare. Ina yi wa masoya na albishir da nan gaba kaɗan zan yi aikin su na fitar da su, domin bidiyon ma an fara ɗauka. Ka san irin wannan aiki bai son aikin sauri. Mun fara ɗauka a hankali, a hankali.
FIM: Akwai sabon album na bidiyo da ki ke ƙoƙarin fitarwa. An ce a ƙarƙashin kamfanin Adamu Hassan Nagudu ne. Me ya sa? Wa ya ke ɗaukar nauyin fitar da album ɗin?
HAIRAT: Ba album ɗi na ba ne, album ɗin sa ne mai suna ‘Tauraro’. Ni na yi amshin waƙar, dalilin da ya sa kenan na hau waƙar. Ni dai nawa ina nan zan fitar da shi ƙarƙashin kamfanin oga na, Umar M. Shareef, wato ‘Shareef Studio’.
FIM: Wa zai ɗauki nauyin aikin naki?
HAIRAT: Umar M. Shareef ne zai ɗauki nauyi in-sha Allah.
FIM: Mecece gaskiyar maganar soyayyar ki da fitaccen makaɗin nan na zamani kuma mawaƙi, Umar MB?
HAIRAT: Umar MB an daɗe ana tare. Kuma oga na ne shi ma, gaskiya. Tun kafin in fara waƙa da Umar M. Shareef mu ke tare da Umar MB. Tun a lokacin ina koyon waƙa mu na tare da shi mu ke waƙa. Duk waƙoƙin sa na baya da na yanzu tare mu ka yi. Don haka Umar MB maigida na ne.
FIM: Kenan dai ba saurayin ki ba ne?
HAIRAT: Inaa! Maigida na ne.
FIM: Kin taɓa aure?
HAIRAT: Ban taɓa aure ba, amma dai ina da niyya. Kullum ina addu’a Allah ya zaɓa min miji nagari, wanda zai riƙe ni amana.
FIM: Akwai lokacin da ki ka ɗauka da za ki daina waƙa?
HAIRAT: Gaskiya ban ɗauki lokaci ba. Sai idan na yi aure; in wanda na aura ya ce ba ya son waƙa sai in haƙura in yi zaman aure kawai.

FIM: Ki na da burin zama furodusa mai shirya finafinai da kuma jaruma wacce za ta riƙa fitowa a fim, kamar yadda wasu mawaƙan su ke yi?
HAIRAT: Ni dai buri na in yi waƙar bidiyo nawa na kai na. Ba zan yi fim ba. Buri na na biyu, Allah ya fito min da miji in yi aure in tafi.
FIM: Waɗanne irin nasarori ki ka samu da waƙa?
HAIRAT: Gaskiya na samu nasarori sosai a rayuwa, waɗanda sai dai in gode wa Allah.
FIM: Hairat ta na samun yabo daga ‘yan’uwan ta mawaƙa da cewa ba ta da girman kai, ba ta da raina abokan sana’ar ta, ba ta da wulaƙanta waɗanda ba su kai ta ba, kuma ta kan yi wa mutane aiki kyauta. Menene sirrin?
HAIRAT: Gaskiya ni na ɗauki waƙa da muhimmanci. Kuma ba zan iya wulaƙanta abokin sana’a ta ba. Dole in girmama kowa ta yadda za mu zauna lafiya da kowa. Ko cewa ka yi in maka aiki ba ka da kuɗi, zan yi maka in dai ba ni da wani abu da ya sha gaba na, in ya so a nan gaba sai in faɗa maka za ka biya kaza.
FIM: Ya ki ka ji a lokacin da aka yi ‘The Making’ ɗin ‘Mansoor’ inda a nan ne aka fara ganin ki?
HAIRAT: Na ji daɗi sosai. Ina godiya sosai ga Sarki Baba Ali Nuhu wanda shi ya yi mana wannan abu. Ali Nuhu mai son cigaban mu ne, gaskiya. Saboda haka, a kullum ina yi masa addu’a a kan abin da zai yi maka babu tsammani. Ina godiya sosai a gare shi. Allah ya ƙara masa girma da ɗaukaka da kuma lafiya. Allah ya raya masa ‘ya’yan shi. Haka ina godiya ga Umar M. Shareef, Aminu Ala, El-Mu’az, Malam Yahaya Makaho, Umar MB, Adamu Hassan Nagudu, Hussaini Danko, Ahmad M. Sadiq, da saura su.
FIM: Mecece shawarar ki ga sauran mawaƙa?
HAIRAT: Shawara ta ga abokan sana’a ta ita ce su ƙara dagewa da jajircewa a kan sana’ar su. Kuma a duk inda su ke su riƙa ɗaukar abin da su ke yi da muhimmanci. Fatan dai Allah ya ba mu sa’a a rayuwar mu.


