• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 8, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

INEC da hukumomin tsaro sun yi taron gaggawa don hana ci gaba da cinna wa ofisoshin hukumar wuta

by DAGA WAKILIN MU
November 13, 2022
in Nijeriya
0
Hagu zuwa dama: Mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro (NSA), Manjo-Janar Babagana Monguno (ritaya); Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu, da Sufeto-Janar na 'Yansanda, Alhaji Usman Alƙali, a taron gaggawar

Hagu zuwa dama: Mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro (NSA), Manjo-Janar Babagana Monguno (ritaya); Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu, da Sufeto-Janar na 'Yansanda, Alhaji Usman Alƙali, a taron gaggawar

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi wani taron gaggawa da hukumomin tsaro domin tattauna hanyoyin hana ci gaba da cinna wa ofisoshin ta wuta.

Kakakin Yaɗa Labarai na INEC, Festus Okoye, ya bayyana cewa taron ya gudana a ranar Juma’a, kuma an tattauna matsalar hare-haren da aka kai ne sau biyu a cikin kwana biyu jere a jihohin Ogun da Osun.

Okoye ya ce an gayyaci dukkan ɓangarorin da ke cikin Kwamitin Kula da Harkokin Tsaron Zaɓe (ICCES) domin tattauna matsalar, ganin yadda ranakun fara zaɓen sai kusantowa su ke yi.

Ya ce: “Mun samu labarin hare-haren banka wa ofisoshin INEC wuta har wurare biyu a jihohin Ogun da Osun. Wannan abu kuwa abin damuwa ne matuƙa.

“Kwamishinan Zaɓe na Jihar Ogun, Niyi Ijalaiye, ya sanar da cewa an kai wa ofishin INEC da ke Ƙaramar Hukumar Abeokuta ta Kudu harin da aka banka masa wuta.

“Maharan sun cimma mummunan burin su bayan sun fi ƙarfin jami’an tsaron da ke wurin, inda su ka banka wa ginin wuta.

“Daga cikin kayayyakin da aka yi asara akwai akwatin zaɓe 904, rumfar shiga a yi zaɓe 29, jakunkunan zuba kayan zaɓe 57, janareto takwas da kuma katin shaidar rajistar zaɓe 65,699 na waɗanda ba su kai ga karɓar na su ba.”

Okoye ya ƙara da cewa an yi irin wannan harin banka wa ofishin INEC wuta a ranar Alhamis a Karamar Hukumar Ede ta Kudu cikin Jihar Osun, kamar yadda Kwamishinan Zaɓe na Jihar,  Mutiu Agboke ya sanar.

Sai dai ya ce a nan ɓarnar ba ta yi muni ba kamar ta Jihar Ogun, kuma a wannan ba a ƙone muhimman takardu da katin shaidar rajistar zaɓe kamar yadda aka yi a Ogun ba.

Yayin da ake saura kwana 106 a fara zaɓe, Okoye ya ce tuni INEC ta fara aikawa da kayan zaɓe a ofisoshin ta na jihohi daban-daban a ƙasar nan. 

Dalilin haka ne ya bayyana cewa hare-haren da aka fara kaiwa har ana banka wa ofishin da ake ajiyar kayan zaɓe wuta abin damuwa ne kuma abin takaici.

Rahotanni da dama sun bayyana yadda aka yi amfani da sunƙin burodi aka babbake ofishin INEC a Ogun.

Kwana ɗaya kuma bayan harin Ogun, wasu taƙadarai sun banka wa ofishin INEC wuta a Jihar Osun.

Wasu cikakkun ‘yan ta-kife sun bi daren Laraba, kafin wayewar garin Alhamis, su ka banka wa ofishin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) wuta a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.

Ofishin da aka banka wa wutar ya na kusa da Iyaka ‘Mortuary’, cikin Ƙaramar Hukumar Abeokuta ta Kudu.  

Jami’an tsaro da na INEC a wurin taron

‘Yan ta-kifen da su ka banka masa wuta sun riƙa jiƙa sunƙin burodi cikin fetur, su na wurgawa a ofishin, sannan su ka ƙyasta wuta su ka tsere.

Mai gadin ofishin, mai suna Azeez Hamzat, ya shaida cewa bayan an banka wutar, ya yi gaggawar kiran ‘yan sanda.

Majiya ta tabbatar da cewa wasu kayayyaki da dama sun ƙone ƙurmus kafin jami’an kashe gobara su kai ɗauki.

Wakilin mu ya gano daga cikin ofisoshin da su ka ƙone akwai ɗakin ajiyar kayayyaki, ɗakin yin rajista, zauren shirya taruka da sauran wasu wurare.

Kwamishinan Zaɓe na Jihar Ogun, Niyi Iyalaye, ya tabbatar wa da wakilin mu da wannan lamari da ya ce abin mamaki da takaici ne matuƙa.

“Amma dai yanzu mun kai rahoto wurin ‘yan sanda, kuma su na bincike,” inji shi.

Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya ce bai san da labarin ba, saboda bai ƙarasa ofis ba tukunna, amma idan ya ƙarasa ya natsu, zai yi ƙarin bayani.

Loading

Tags: Abeokutabanka wutaFestus OkoyeINECƙone ofishiMutiu AgbokeNiyi IyalayeOgunOsunZaɓen 2023
Previous Post

Jami’a a ƙasar Togo ta ba furodusan Kannywood Abdul Amart digirin girmamawa

Next Post

Rikici tsakanin jarumin barkwanci Ali Maɗagwal da surukan sa ya janyo an hana shi shiga asibitin da matar sa ta haihu

Related Posts

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London
Nijeriya

Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London

May 16, 2025
Next Post
Ali da Hauwa'u za su Legas cikin jirgin sama jim kaɗan bayan ɗaurin auren su

Rikici tsakanin jarumin barkwanci Ali Maɗagwal da surukan sa ya janyo an hana shi shiga asibitin da matar sa ta haihu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!